Moctar Omar

Moctar Omar je suis béninois d'origine Nigéria ma langue et haoussa je vis actuellement au Bénin

11/09/2026
11/09/2026

SABON BAYANI KAN BICHIYA MAISANGO — KWANA 100 A TSARE

An je kotu ranar Laraba kamar yadda aka tsara. Jibril Ismail da Ilyasu Aliyu Ibrahim ma sun halarta.

Abin da zan iya bayyanawa da kaina a yanzu shi ne cewa DSS ba ta halarci zaman kotun ba. Yanzu da hutun kotuna ya ƙare, akwai kuma yiwuwar a mayar da shari’ar ga wani sabon alkalin kotu.

Lauyan Bichi, Inibehe Effiong, zai fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba domin bayyana ainihin abin da ya faru a kotun, da kuma abin da za a yi a mataki na gaba.

Saboda haka, a yanzu zan bar cikakken bayani kan batun shari’ar ga waɗanda s**a fi cancanta su yi bayani a kai.

Amma yau kwanaki 100 ke nan tun da aka tsare Bichi. Duk da haka, Bichi na nan cikin ƙoshin lafiya da ƙarfin hali, yana da ƙwarin gwiwa kuma yana yana cikin walwala.

Kamar yadda muka saba, muna ci gaba da kasancewa da ƙwarin gwiwa kan tsarin shari’ar Najeriya, kuma za mu ci gaba da sa ido tare da fatan cewa adalci zai tabbata ga Bichia Maisango.

Ta hannun: Hauwa Mundi






Adresse

Cotonou

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Moctar Omar publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Raccourcis

Partager