A.E.S-Hausa Info

A.E.S-Hausa Info Domin samun ingantattun labaran Hausa na kasashen kawancen Sahel (Mali, Nijar Burkina Faso) da Afrika har ma da Duniya baki daya...

  |  🇳🇪🤝🇸🇦  An nada tsohon Minista Sheikh Ali Ben Salah Hamouda a matsayin Jakadan Jamhuriyar Nijar a Masarautar Saudiyy...
17/09/2026

| 🇳🇪🤝🇸🇦
An nada tsohon Minista Sheikh Ali Ben Salah Hamouda a matsayin Jakadan Jamhuriyar Nijar a Masarautar Saudiyya.

  |  🇳🇪An yi musayar mukami a tsakanin sabo da tsohon babban hafsan Hafsoshin Sojin Nijar.Matakin na zuwa ne bayan sauye...
16/09/2026

| 🇳🇪
An yi musayar mukami a tsakanin sabo da tsohon babban hafsan Hafsoshin Sojin Nijar.

Matakin na zuwa ne bayan sauye sauyen da akayi a manyan rundunonin soji na kasar.

🚨   | An nada sabbin ministoci hudu 🇳🇪Shugaban Kasa NijarJanar Abdourahamane Tiani, ya rattaba hannu kan wani kudiri, na...
15/09/2026

🚨 | An nada sabbin ministoci hudu 🇳🇪

Shugaban Kasa NijarJanar Abdourahamane Tiani, ya rattaba hannu kan wani kudiri, na sake fasalin Gwamnati inda aka canza ministoci guda hudu tare da nada sabbi a gurabensu.

1. Ministan noma da kiwo: • Kanal BILALY ELHADJ GAMBOBO

2. Ministan Sake Gina Kasa da Inganta Dabi'un Al'umma: Malam ABDOURAHAMANE OUMAROU

3. Ministan Makamashi: • Laftanar-Kanal SEYNI ALZOUMA

4. Ministan Sadarwa da Sabbin Fasahohi Malam HAMANI KARGNE, kamar yadda sakataren gwamnatin kasar ya sanar a wannan Talata.

  |     An nada dan kasar Aljeriya Nabil_Neghiz a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafa ta Nijar  🇳🇪, inda Ya maye g...
11/09/2026

|

An nada dan kasar Aljeriya Nabil_Neghiz a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafa ta Nijar 🇳🇪, inda Ya maye gurbin dan kasar Morocco Badou_Zaki kamar hukumar Fenifoot ta sanar.

  |  🇳🇪Gwamnatin Nijar ta sanar da dakatar da bada fasfo na CEDEAO / ECOWAS, ga 'yan kasar tare da maye gurbinsa da na A...
10/09/2026

| 🇳🇪
Gwamnatin Nijar ta sanar da dakatar da bada fasfo na CEDEAO / ECOWAS, ga 'yan kasar tare da maye gurbinsa da na AES.

Saidai gwamnatin ta ce masu rike da fasfo na ECOWAS zasu ci gaba da aiki da shi har karshen wa'adinsa.

  |  🇳🇪Bayan boren sojojin da aka murkushe a karshen makon jiya a Yamai babban birnin kasar, gidan talabijin na RTN ya f...
02/09/2026

| 🇳🇪
Bayan boren sojojin da aka murkushe a karshen makon jiya a Yamai babban birnin kasar, gidan talabijin na RTN ya fitar da rahoton tarin makamai da kayan yakin da aka kwace.

  |  🇲🇱🇲🇱 KIDAL: Tsoffin 'yan sojoji 37 sun shiga rundunar sojan Mali domin tallafa kasar wajen tabbatar da tsaro.
02/09/2026

| 🇲🇱

🇲🇱 KIDAL: Tsoffin 'yan sojoji 37 sun shiga rundunar sojan Mali domin tallafa kasar wajen tabbatar da tsaro.

  |  🇧🇫  🇪🇬Kasashen Burkina Faso da Masar sun yunkuri karfafa alaka a tsakaninsu ta fagage da dama.
02/09/2026

| 🇧🇫 🇪🇬
Kasashen Burkina Faso da Masar sun yunkuri karfafa alaka a tsakaninsu ta fagage da dama.

  |  🇳🇪 An yi gangamin jadadda goyan bayan ga mulkin sojoji a fadin kasar Jamhuriyar Nijar a Wannan Laraba.Hakan na zuwa...
02/09/2026

| 🇳🇪
An yi gangamin jadadda goyan bayan ga mulkin sojoji a fadin kasar Jamhuriyar Nijar a Wannan Laraba.

Hakan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan murkushe boren wani gungun sojoji a Yamai babban birnin kasar a karshen makon jiya.

📷 fadar gwamnan jihar Agadas.

  |  🇳🇪   Tarayyar Afrika ta yi tir da boren da sojoji sukayi a karshen makon jiya a Nijar tare da cewa a shirye ta ke t...
02/09/2026

| 🇳🇪
Tarayyar Afrika ta yi tir da boren da sojoji sukayi a karshen makon jiya a Nijar tare da cewa a shirye ta ke ta taimaka wajen dawo da tsarin mulki.

Adresse

Niamey

Site Web

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque A.E.S-Hausa Info publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Raccourcis

Partager