Jamhuriya

Jamhuriya Kafar Labaran Gida da waje

■ Shin ƙarancin makamai ne ya sa Amurka ta dakatar da yaƙi da Iran?Lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya halarci wa...
29/07/2026

■ Shin ƙarancin makamai ne ya sa Amurka ta dakatar da yaƙi da Iran?

Lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya halarci wani taro tsaro na a Pennsylvania a farkon wannan watan tare da shugabannin manyan kamfanonin ƙera makamai na ƙasar, babban saƙonsa shi ne: a ƙera ƙarin makamai cikin sauri.

Trump ya shaida wa shugabannin kamfanonin ƙera makamai a taron da aka gudanar a Kwalejin Horas da Sojoji ta Amurka, tare da Sakataren Tsaro Pete Hegseth cewa, "Muna da makamai mafi inganci a duniya, amma muna buƙatar a riƙa ƙera su cikin sauri."

Gwamnatin Trump ta bayyana taron a matsayin wani ɓangare na shirin farfaɗo da masana'antun [ƙera makaman] Amurka da kuma ƙarfafa ƙarfin yaƙin ƙasar, abin da Hegseth ya kira "rumbun ƴanci" ko ma'ajiyar makaman 'yanci.

Sai dai abin da ba a fi mayar da hankali a kai ba shi ne yawan makamai masu tsada da kuma wahalar ƙerawa da Amurka ta lalata a kusan kwanaki 40 na hare-haren da ta kai Iran a ƙarƙashin Operation Epic Fury, da kuma hare-haren ramuwar gayya da s**a biyo baya.

Gwamnatin Amurka ta ce zuwa yanzu yaƙin ya laƙume dala biliyan 37.5, inda mafi yawan kuɗin s**a tafi wajen saye da amfani da makamai.

Kafin tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 8 ga Afrilu, Fadar White House ta ce dakarun Amurka sun kai hare-hare kan wurare sama da 13,000 a faɗin Iran. Haka kuma na'urar kariyar sararin samaniyar Amurka ta kakkaɓo sama da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami 1,700 da Iran ta harba a wannan lokaci.

A halin yanzu Amurka ta dakatar da hare-harenta domin bai wa tattaunawar diflomasiyya damar ci gaba.

Rahoton jaridar New York Times ya ce an shawarci Trump da ya dakatar da shirin ƙara tsananta yaƙin saboda hakan na iya ƙara rage yawan makaman da Amurka ke da su.

Sai dai Trump ya musanta cewa Amurka na fama da ƙarancin makamai.

A wata hira da Wall Street Journal, shugaban na Amurka ya ce ƙasarsa tana da makamai fiye da kowace ƙasa a duniya, kuma fiye da abin da take buƙata.

kafin yaƙin ya fara.

Kowane makamin Patriot yana laƙume kusan dala miliyan huɗu, duk da cewa ana amfani da shi wajen kakkaɓo jirage marasa matuƙa na Iran waɗanda farashinsu bai wuce tsakanin dala dubu 20 zuwa dubu 50 ba.

Masana sun ce maye gurbin waɗannan makamai ba abu ne mai sauƙi ba.

Mark Cancian, babban mai ba da shawara a cibiyar CSIS, ya ce ana ɗaukar shekaru da dama kafin a ƙera makami guda.

Ya ce ko da za a ware kuɗi a yau, ba za a samu sabon makami ba sai bayan shekaru uku ko huɗu, wani lokaci ma har biyar.

A cewarsa, makaman da ake karɓa a yanzu su ne waɗanda aka amince da kuɗinsu tun a shekarar 2023.

Hankali ya karkata kan Taiwan da Pacific

Yaƙin da Amurka ta yi da Iran ya zo ne a daidai lokacin da ake fara tattaunawa kan abin da wasu jami'an sojin Amurka ke kira "Davidson window", wato lokacin da ake ganin yiwuwar China ta kai hari kan Taiwan na ƙaruwa.

Wannan batu da aka daɗe ana muhawara a kai, wanda ke da muhimmanci ga sojin Amurka a yankin Pacific, ya samo asali ne daga wani zaman sauraron ƙorafi a Majalisar Dokokin Amurka a shekarar 2021.

A lokacin, Admiral Philip Davidson, wanda a wancan lokaci ke jagorantar dakarun Amurka a yankin, ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar mamayar Taiwan "cikin shekaru shida masu zuwa".

A shekarar 2023 kuma, tsohon Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Amurka CIA, William Burns, ya yi hasashen cewa China na iya zama cikin a shirin kai hari kan Taiwan zuwa shekarar 2027.

China ta daɗe tana cewa za ta "sake haɗa" Taiwan da ƙasarta, inda take kallon tsibirin da ke mulkin kansa a matsayin wani lardi da ya b***e daga cikinta. Duk da cewa ba ta ce za ta yi amfani da ƙarfi kai tsaye ba, ba ta taɓa kawar da yiwuwar hakan ba.

Har yanzu dai ana tababa kan ko Amurka za ta shiga yaƙi domin kare Taiwan idan China ta kai hari. Sai dai duk da rashin bayyana matsayinta a fili, Amurka na ci gaba da bai wa Taiwan makaman kariya.

Mark Cancian na cibiyar CSIS ya bayyana ƙarancin makaman Amurka a matsayin wani "rauni", inda yake cewa Amurka ba za ta samu yawan makaman da take so ba idan rikici ya ɓarke a yankin Pacific.

A cewarsa, hakan na iya ƙara haɗarin barin dakarun Amurka ba su shirya yadda ya kamata ba wajen fuskantar ɗimbin makamai masu linzami da jiragen yaƙin China.

Jami'an Amurka sun ce China na sa ido sosai kan yadda aka yi amfani da tsarin kariyar sama na Amurka a yaƙin Iran.

A cikin 'yan shekarun nan, Beijing ta zuba kuɗi masu tarin yawa wajen bunƙasa fasahar makamai masu linzami, ciki har da masu saurin gaske (hypersonic glide missiles) waɗanda s**a fi na Iran ci gaba sosai.

Haka kuma China ta ƙara mayar da hankali wajen samar da dabarun amfani da ɗimbin jirage marasa matuƙa lokaci guda.

Sai dai ba kowa ne ke kallon raguwar ma'ajiyar makaman Amurka a matsayin matsala ba.

Jacob Olidort, tsohon jami'in leƙen asiri na CIA kuma tsohon mai ba da shawara kan manufofin Gabas ta Tsakiya a Ma'aikatar Tsaron Amurka, ya ce amfani da waɗannan makamai a fagen yaƙi yana aika wani saƙo mai ƙarfi ga abokan gaba da duniya baki ɗaya.

Yaya lamarin zai shafi Turai?

Takun-saƙar da ke tsakanin ci gaba da bai wa ƙawayen Amurka makamai da kuma kare ma'ajiyarta ta riga ta bayyana a yaƙin Ukraine.

A watan Oktoban 2025, watanni kafin fara Operation Epic Fury, Shugaba Donald Trump ya ƙi bai wa Ukraine makaman Tomahawk, inda ya ce hakan zai rage yawan makaman da Amurka ke da su.

Masana na ganin wannan mataki ya nuna irin yanayin da Amurka ke fuskanta yanzu bayan yaƙin Iran, tsakanin tallafa wa ƙawayenta da kuma kare nata ma'ajiyar makamai.

Jami'an Ukraine sun ce har yanzu suna matuƙar buƙatar makaman Patriot da sauran na kariyar sama domin dakile hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da Rasha ke ci gaba da kai musu.

A wata hira da BBC a watan Maris, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce "yaƙin Iran ba wai kawai ya shafi farashin makamashi ba ne, har ma ya rage ma'ajiyar makaman Amurka da ƙarfin kamfanonin da ke ƙera makaman kariyar sama."

Ya ce hakan na nufin Ukraine ma na fuskantar ƙarancin makaman da take buƙata.

Zelensky ya bayyana cewa Amurka na ƙera makamai masu linzami tsakanin 60 zuwa 65 a kowane wata, wato kusan 700 zuwa 800 a shekara, inda aka yi amfani da makamai aƙalla 803 a ranar farko kaɗai ta yaƙinta da Amurka da Isra'ila..

Sai dai kwanan nan Trump ya ba jami'an Turai mamaki bayan ya amince a bai wa Ukraine damar ƙera makaman Patriot a cikin ƙasarta. Irin wannan tsari ya riga ya fara aiki a Jamus da Japan.

Elaine McCusker, wadda ta shafe shekara 13 tana aiki a Ma'aikatar Tsaron Amurka kuma yanzu ƙwararriya ce a cibiyar American Enterprise Institute, ta ce ƙwarewar da Ukraine ta samu wajen yaƙi da Rasha, da kuma ta Amurka a yaƙin Iran, na iya taimakawa wajen samar da sabbin makamai masu rahusa da za a iya ƙera su da yawa, domin su riƙa cike gurbin masu tsada da ƙarancin manyan makaman da ake amfani da su yanzu.

Duk da wannan batu da ake yi, masana sun ce babu wata alamar da ke nuna makaman Amurka na dab da ƙarewa da . Ba wai don ma'ajiyarta ba ta da iyaka ba ne, sai dai saboda ana ganin Iran ta fi fuskantar matsanancin ƙarancin makamai.

Mai magana da yawun Fadar White House, Anna Kelly, ta shaida wa BBC cewa sojojin Amurka na da isassun makamai da harsasai domin cimma dukkan manufofin tsaron Shugaba Donald Trump, har ma fiye da haka.

Sai dai ta ƙara da cewa duk da haka, Shugaba Trump ya ci gaba da ƙarfafa kamfanonin ƙera makaman Amurka su ƙara yawan makaman da suke samarwa.

A baya-bayan nan, hare-haren da Rundunar Tsakiyar Amurka (CENTCOM) ta sanar da cewa sun fi mayar da hankali ne kan raunana ƙarfin Iran da ke barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Masana sun ce asarar da sojojin Iran s**a yi ta fi ta Amurka nesa ba kusa ba, bayan jerin hare-haren da Amurka da Isra'ila s**a kai, kuma Iran ba ta da ƙarfin da za ta iya maye gurbin waɗannan makamai cikin gaggawa.

Jason Brodsky, daraktan a hukumar ƴaki da mallakar makamin nukiliyar Iran ya ce mutane da dama na ɗaukar Iran a matsayin ƙasar da ke da makamai marasa iyaka, amma hakan ba gaskiya ba ne.

Ya ce hare-haren da ka kai mata sun yi mummunar illa ga wajen ƙera makaman Iran, tare da rage mata ƙarfin samar da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a adadi mai yawa.

A cewarsa, makaman da s**a rage wa Iran yanzu ana tanadar su ne domin yin barazana ga mashigar Hormuz, amma ya yi imanin cewa wannan ƙarfin ma na ci gaba da raguwa.

Ya ce gwamnatin Iran na fuskantar ƙarancin lokaci da za ta iya ci gaba da amfani da wannan damar.

Brodsky ya ƙara da cewa, a halin yanzu rikicin da ake yi da Iran shi ne abin da ya fi ɗaukar hankalin gwamnatin Amurka.

BBC Hausa ✍

'Amurka da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar nukiliya'Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa gwamnatin Donald Tru...
23/07/2026

'Amurka da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar nukiliya'

Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa gwamnatin Donald Trump ta cimma wata yarjejeniya da Saudiyya game da sarrafa makamashin nukiliya, kuma za a sanar da abin da yarjejeniyar ta ƙunsa nan ba da daɗewa ba.

Yarjejeniyar za ta iya bai wa Saudiyya damar inganta makamashin yureniyom (Uranium) ta yadda za ta iya amfani da shi a rumbunan sarrafa makamashin nukiliya.

Yarjejeniya kan makamashin nukiliya tsakanin ƙasashen duniya abu ne da ke haifar da muhawara a tsawon shekaru.

Wasu daga cikin ƴan majalisar dokokin Amurka sun nuna damuwa kan cewa Saudiyya za ta iya yin amfani da damar wajen ƙera makaman ƙare-dangi.

Wannan yarjejeniya za ta iya sake yauƙaƙa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, wadda da alama ta fara rawa sanadiyyar yaƙin Iran - kuma hakan zai iya bai wa kamfanonin Amurka wata ƙarin dama.

BBC Hausa ✍

Ko farin jinin Buhari zai yi tasiri a siyasar ɗansa?Wasiƙar da ke waɗari a shafukan sada zumunta ta ambata cewa Yusuf Bu...
08/04/2026

Ko farin jinin Buhari zai yi tasiri a siyasar ɗansa?

Wasiƙar da ke waɗari a shafukan sada zumunta ta ambata cewa Yusuf Buhari zi yi takarar ne a jam'iyyar APC da mahaifinsa ya zama shugabanta ƙarƙashin inuwarta.

Wane tasiri farin jinin Buhari zai yi wa Yusuf?

Galibi masu kiran matashin ya yi takara, suna yi ne la'akari da irin farin jinin da mahaifinsa ya samu a fagen siyasar Najeriya.

Dr Kabiru Sa'id Sufi malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar ƙasar, ya ce Yusuf ka iya samun goyon baya da tausayawa daga al'ummar, la'akari da farin jinin mahaifinsa.

''Mahaifinsa ya yi farin jinin da wataƙila zai iya shafarsa a siyasance, kuma yadda aka yi tururuwa a lokacin jana'izar mahaifinsa na nuna tausayawa da mutane s**a nuna wa iyalan nasa'', in ji shi.

Dangane da ko Yusuf zai iya taka rawa gani a siyasance, Dr Sufi ya ce duba da yadda wasu yaƴan manyan ƴansiyasa s**a yi nasara, kuma s**a taka rawar gani, za a iya cewa shi ma Yusuf ana kyautata masa zaton yin ƙoƙarin gaske.

''Idan ka duba mutum ne mai kamun kai da kawaici, wanda bai fiya shiga yahaniya ba'', in ji Dr Sufi.

Wane ne Yusuf Buhari?

To sai dai BBC ta tuntuɓi, Bashir Ahmad tsohon mataimaki na musamman kan kafofin sadarwa na zamani ga mahaifin Yusuf, wato marigayi Muhammadu Buhari, wanda kuma ya tabbatar da gaskiya al'amarin.

Bashir Ahmad ya ce ''haka ne Yusuf zai tsaya takarar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Sandamu/Daura/Mai'Adua a zaɓen 2027 mai zuwa''.

Tsohon hadimin Buharin ya ce Yusuf ya ɗauki matakin ne bayan kwashe makonni yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki da abokan shawara.

Bayanai na ci gaba da fitowa game da batun tsayawar ɗan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari, takarar majalisar wakilan Najeriya.

Tun bayan saukar mahaifinsa daga mulki, ƴansiyasa da dama ke alaƙanta Yusuf Buhari da shiga siyasa, to sai dai ya riƙa noƙewa tare da nuna rashin muradin yin hakan.

Kiraye-kirayen da ake yi wa matashin sun ƙara tsananta tun bayan mutuwar mahaifin nasa.

Yanzu haka ana alaƙanta matashin - wanda shi kaɗai ne ɗa namiji ga marigayi Muhammadu Buhari - da takarar majalisar wakilai ta tarayya.

Mene ne gaskiyar batun?

Jaridun Najeriya sun riƙa ambato wata wasiƙa da s**a ce daga Yusuf Buhari take game da wannan aniya.

Yusuf Buhari shi ne kaɗai na namiji ga tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Shi ne ɗa na biyu a wajen mahaifiyarsa Hajiya Aisha Buhari, matar da tsohon shugaban ƙasar ta biyu.

Matashin mai shekara 34 na auren ƴar gidan tsohon sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Ya karanta fannin tattalin arziki a jami'ar Surrey da ke Birtaniya.

Ba kasafai ake ganin fuskarsa a harkokin siyasa ko mulki ba a zamanin gwamnatin mahaifinsa.

Yusuf Buhari bai taɓa riƙe wani muƙamin siyasa ba a Najeriya ba.

BBC Hausa

■____■____■Ƙarancin mai da aka shiga a 1970, ko mun doshi ganin mafi muni a yanzu?Rufe wata hanyar ruwa mai muhimmanci w...
06/04/2026

■____■____■
Ƙarancin mai da aka shiga a 1970, ko mun doshi ganin mafi muni a yanzu?

Rufe wata hanyar ruwa mai muhimmanci wadda ake amfani da ita wajen kai mai a faɗin duniya ya janyo fargabar cewa duniya na iya shiga matsalar ƙarancin mai fiye da wadda aka taɓa gani a shekarun 1970.

Lars Jensen, wani ƙwararre kan jigilar kayayyaki ta ruwa, ya faɗa wa BBC cewa tasirin yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran zai iya yin yawa fiye da na ruɗanin tattalin arziki da aka gani a 1970.

Kalamansa na zuwa ne bayan gargaɗin da shugaban hukumar makamshi ta duniya Fatih Birol ya yi a farkon wannan wata cewa duniya na "babbar barazanar ƙarancin makamashi a tarihi".

"Lamarin zai fi wanda muka taɓa gani a 1970, farashin mai ya yi mugun tashi. Kuma ya fi na ƙaruwar farashin iskar gas da muka fuskanta bayan mamayar Rasha a Ukraine," kamar yadda ya faɗa wa BBC.

Sai dai yayin da rufe mashigar Hormuz ya kawo cikas a ɓangaren samar da mai a duniya, wasu sun kalubalanci cewa duniya ta fi juriya a yanzu.

● Wane irin matsalar mai aka shiga a 1970?

Matsalar mai da aka fuskanta a shekarun 1970 ya sha bambab da wannan da ake gani a yau, saboda na wancan lokaci ya faru ne sakamakon wasu tsare-tsare da aka aiwatar dagan-gan," a cewar masaniya kan tattalin arzkiki Dr Carol Nakhle, ta faɗa wa BBC.

A watan Oktoban 1973, masu samar da mai daga ƙasashen Larabawa sun sanya takunkumi kan wasu ƙasashe karkashin jagorancin Amurka bisa goyon baya da s**a bai wa Isra'ila a lokacin yaƙin Yom Kippur. Tsarin ya zo haɗe da batun rage samar da mai.

"Sakamakon haka ne farashin mai ya kusa ninƙawa sau huɗu a watannin farko na yaƙin," in ji Nakhle.

Wannan ya haifar da tashin farashin man fetur a manyan kasashen da ke mu'amala da mai, kuma Nakhle ya ce hakan ya haifar da "matsalar tattalin arziki da kuma na kuɗi a duniya".

Dakta Tiarnán Heaney, wani mai bincike a jami'ar Queen da ke Belfast, ya ce ƙaruwar farashin man fetur ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a faɗin duniya, "ma'ana kasuwanni sun durkushe kuma rashin aikin yi ya karu".

"Wannan ya yi tasiri sosai da kuma lalata masana'antun musamman na ɗinki a ƙasashe da dama da s**a fuskanci yajin aiki, tashe-tashen hankula, da ƙaruwar talauci, inda magidanta da dama s**a shiga matsi na abin da za su kai bakin salati," in ji shi.

Amurka da Birtaniya sun samu tawayar tattalin arziki wanda ya daɗe daga 1973 zuwa 1975, tare da rikicin da ya janyo faduwar gwamnatin Ted Heath a 1974.

● Me ke faruwa a matsalar mai da ake ciki yanzu?

Tun bayan da Amurka da Isra'ila s**a kaddamar da yaƙi kan Iran a watan da ya gabata, an rufe mashigar Hormuz mai muhimmanci wajen kai kayayyaki a faɗin duniya.

Lamarin ya janyo cikas wajen fitar da mai, iskar gas da kuma sauran kayayyaki na buƙatu a faɗin ƙasashen yankin Gulf, wanda ya saba fitar da kashi biyar na mai da ake amfani da shi a duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da dabaru da dama don ganin an fita daga matsalar, ciki har da kira ga ƙawayen ƙasar su tura jiragen ruwa na yaƙi da za su yi rakiya, da kuma barazanar ci gaba da kai hare-hare Iran idan ba su bar jiragen ruwa s**a wuce cikin aminci ba ta mashigar.

Sai dai Jensen, wani ƙwararre kan jigilar kayayyaki ta ruwa, ya shaida wa BBC cewa yawancin mai da ya bar yankin Gulf a watan da ya gabata na ci gaba da isa matatun mai a faɗin duniya, kuma nan ba da jimawa za a dakatar da jigila.

"Matsalar ƙarancin mai da muke gani za ta ƙara yin muni, ko da gobe za a buɗe mashigar Hormuz," in ji shi.

"Za mu fuskanci gagarumin matsalar makamashi - ba wai idan wannan yaƙi ya ci gaba ba, illa har na tsawon watanni shida zuwa 12 idan yaƙin ya kare."

● Shin matsalar mai ta yanzu za ta iya fin na 1970 muni?

Nakhle, wadda ita ce sakatare-janar na ƙungiyar makamashi ta Larabawa, ta ce kasuwar mai ta yanzu ta bambanta da ta shekarun 1970, yayin da yawan kuɗi da ake zuba wa ma ya ragu.

Ta yi imanin cewa yayin da farashi ya haura, amma matsalar da ake ciki yanzu ba ta kai ta da muni ba.

"Yayin da yawan mai da ake fitarwa ya ragu - wanda an daɗe ba a ga haka ba - amma kasuwannin yanzu sun fi juriya fiye da na shekarun 1970," in ji ta.

Sai dai Joel Hancock, darektan bincike kan farashin mai a wata cibiya, ya ce wani abin bambanci shi ne matsalar ƙarancin mai ta 1970 ta ta'allaka ne kan ƙasashen da s**a cigaba, waɗanda ke da kuɗi da kuma "ƙarfin siyasa" wajen shawo kanta.

Matsalar yanzu ta fi shafar ƙasashe masu tasowa, "waɗanda ba su da kuɗi da hukumomin da za su iya fita daga matsalar," in ji shi.

Hancock ya ce matsalar da ake ciki a yanzu za ta kare "da zarar an kawo karshen yaƙi."

Daga BBC Hausa

♡♤♡♤♡♤♡♤♡♤♡♤Da gaske ne sha'awar ma'aurata na dakushewa?A shekara ta 1990 Alan Reeves yakan yi rawa tsirara a gaban dubb...
06/04/2026

♡♤♡♤♡♤♡♤♡♤♡♤
Da gaske ne sha'awar ma'aurata na dakushewa?

A shekara ta 1990 Alan Reeves yakan yi rawa tsirara a gaban dubban mutane yayin da yake mamba a ƙungiyar Dreamboys. Ya yi farin jini sosai inda ake neman sa a lokuta da dama tare da abokansa masu rawa, sun taɓa fitowa a fim ɗin Spice Girls mai suna Spice World.

A wancan lokaci ya na da shekara 24 da haihuwa.

Amma da ya kai shekara 30, sai ya tsinci kansa a mawuyaci hali- sha'awarsa ta ragu ƙwarai.

"Ba na jin daɗin jikina," in ji shi.

Reeves mai shekaru 52 a yanzu ya ce rashin sha'awa ya zamar masa ƙalubale a alaƙarsa.

"Mu kan shafe watanni 3 ko 4 a wasu lokutan ba tare da jima'i ba. Ba na son yi," ya ce.

"Irin wannan yanayi zai iya raba Namiji da Mace.

Yanzu ya koma mai horas da masu motsa jiki a London, Reeves wanda ya fara shan magungunan da ke dawo da sinadarin testosterone watau testosterone replacement therapy (TRT). Ya bayyana cewar sha'awarsa ta dawo inda a yanzu ya na ji kamar shekarunsa 20.Mata ma ba a bar su a baya ba, sun fara komawa testosterone.

Rachel Mason ƴar shekaru 37 mai wallafa labarai game da shekarun da mata suke manyanta watau menopause, ta bayyana cewar magungunan TRT sun ƙara mata kuzari da sha'awa.

An samu ƙaruwar masu amfani da magungunan, bayanai na baya-bayan nan da hukumar NHS ta bayar sun ce an samu ƙaruwar masu buƙatar da kashi 135 tsakanin shaekara ta 2021 da shekara ta 2024.

An samu ƙarin ne ya yin da sha'awar ta ragu tsakani sosai a Birtaniya kamar yadda wata hukumar ƙididdiga ta bayyana (Natsal), lamarin da ya haifar da tambayar sama da mutane 10,000 game da sha'awar su.

A shekara ta 1990. mutane masu shekara 16 zuwa 44 sun bayar da rahoton yin jima'i aƙalla sau 5 a wata ɗaya. Amma a shekara ta 2000 an samu raguwa da kashi 4 ya yin da a shekara ta 2010 aka kuma samun raguwa da kashi 3. A halin yanzu a ana dakon sabon sakamakon binciken cikin wannan shekara, masu bincike na sa rai za a kuma samun raguwar duk da cewar ba su faɗi wani dalili da ke haifar da raguwar sha'awa stakanin mutanen ba.

Ana tafka muhawara sakamakon wannan komabata da ake samu, Shin ko ƙarawa sinadarin testosterone ƙarfi a jikin mutane zai ƙara sha'awar jima'i ko kuwa batu ne kawai don neman suna da kuɗi?

● Dakushewar sha'awa

Matsalar dakushewar sha'awa da Alan Reeves ke fuskanta, ɗaya daga cikin misalai ne da masu bincike s**a ce yana ƙara yawaita.

"A tsawon shekaru, mun ga raguwar sha'awa tsakanin mutane," in ji Soazig Clifton.

"Akwai ma'aurata a cikin wannan lamari ba kamar a can baya ba, wanda kuma hakan ne ke nuna raguwar sha'awa matuka."

An fi samun raguwar sha'awar tsakanin tsofaffi, ma'aurata ko kuma masu soyayya.

Clifton ta ce akwai wahala a iya bayyana me ya sa ƙarfin sha'awa ke raguwa.

"Babu alkaluma da za su iya faɗa mana dalilin da ya sa ake samun raguwar yin jima'i a matsayin al'umma," in ji ta.

Akwai bincike da yawa waɗanda ke ƙoƙarin fahimtar dalilin da ya sa ake samun haka, suna nuna cewa tsarin zamani na iya zama babban dalili, saboda mutane na ƙarin abubuwa da za su yi.

Gajiyar da muke yi yanzu ta fi ta shekaru 30 da s**a wuce, wanda hakan na iya zama dalili, in ji Dakta Ben Davis, masanin ilimin jima'i.

"Mutane na fama da abubuwa da yawa," in ji shi, "Akwai fasaha, amma akwai ƙaruwa gajiya, damuwa da kuma kaɗaici... duka waɗannan za su iya zama abin da ya sa ake samun dakushewar sha'awa.

Akwai kuma hasashen cewa wata ƙarancin sinadarin halitta na namiji wanda ke ƙara ƙarfin jima'i na cikin dalilai na dakushewar jima'i.

"Sindarin halittar namiji na raguwa," in ji Farfesa Geoffrey Hackett.

"Ƙaruwar masu ƙiba, na'ui na biyu na cutar suga, ƙaruwar mutanen da ke zama ko kwanciya na tsawon lokaci - duka waɗannan na rage sinadarin halittar namiji wato testosterone. Kuma hakan zai iya zama dalili na raguwar son yin jima'i.

● Sinadarin halitta ya dawo min da jin daɗin rayuwa

Melissa Green ta kasance tana na abin da zai ƙara mata sinadarin halitta kusan shekara guda. Ta ce ba ya ga dawowar jin daɗin rayuwarta - abin ya ceci har aurenta.

Ƴar shekaru 43 da haihuwa ta ce ƙarancin sha'awa ya yi tasiri sosai a dangantakarsu.

"Rayuwata ta koma sabuwa. A wani lokaci, ina jin tamkar ƴar shekara 20," in ji ta.

"Na ƙara samun ƙarfi, ina da kuzari, kuma ƙarfin sha'awata ta dawo."

Ga maza, sinadarin halitta na raguwa ne da kashi ɗaya daga shekara 30 zuwa 40.

Hukumar lafiya ta Birtaniya ta ce wannan ba abin damuwa bane saboda yana cikin ɓangare na tsufa kuma da wuya ya shafi ƙarfin sha'awa.

Alan Reeves ya ce an yi masa allurai huɗu domin mayar da sinadarin halittarsa yadda ya kamata daga NHS. Sai dai, bayan yi masa magani, an faɗa masa cewa abin ba zai ci gaba da aiki ba, "ba tare da an yi masa bayani ba."

"Na koma gidan jiya," in ji shi. "Lokacin ne na yanke shawarar yin shiru."

Don haka, wane mataki ake son sinadarin halittar namiji ya kai? a

Hukumar lafiya ta Birtaniya ta ce idan sinadarin halittar najimi ya yi kasa da mataki shida zuwa takwas, to za a iya cewa suna da matsala.

Ga mata kuwa, sinadarin halittarsu na raguwa ne tsakanin shekaru 20 zuwa 40, kafin su shiga shekarun ɗaukewar al'ada. Ba matsala bace idan sinadarin ya yi kasa a loakcin, sai dai wani tasiri hakan zai yi ga sha'awar mace baki ɗaya.

Yana da wahala a gane haka, saboda yayin da sinadarin yake da muhimmanci ga mata, wanda ake buƙata ba shi da yawa.

Alan Reeves, ya kasance yana kan magani na daidaita sinadarin halitta na tsawon shekara bakwai, don ƙarfin sha'awarsa ta dawo. Ya ce rayuwarsa ta yi matukar sauya wa.

"Ƙarfin sha'awata ya dawo, akwai lokacin da na riƙa jin son yin jima'i a kowane dare har sau goma.

"Amma hakan ya ragu yanzu kuma komai ya daidaita."

Daga BBC Hausa

■□■□■□■□■□Ina ne mashigar Hormuz, kuma me ya sa take da muhimmanci?Tun bayan da yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran ya ɓarke...
06/04/2026

■□■□■□■□■□
Ina ne mashigar Hormuz, kuma me ya sa take da muhimmanci?

Tun bayan da yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran ya ɓarke, sai maganar mashigar Hormuz ta fara faɗaɗa da jan hankali, inda mutane suke ta tambayar ina ne mashigar, kuma ma ya sa take da matuƙar muhimmanci.

Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana samun nasara sosai a yaƙin, wani abu da ake ganin tamkar ya tsaya masa a wuya shi ne batun datse mashigar ta Hormuz.

Trump ya sha nanata cewa zai tura sojojin ruwan Amurka, sannan ya nemi taimakon wasu ƙasashen domin tabbatar da cewa an buɗe mashigar domin a ci gaba da tafiyar da ɗanyen mai

Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.

Tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Birtaniya wato M16, Sir Alex Younger ya shaida wa BBC cewa daga cikin manyan matsalolin da yaƙin zai haifar akwai datse tekun. "Datse tekun zai haifar da matsalar tattalin arziki mai girma saboda yadda zai shafi farashin man fetur."

■ A ina mashigar take?

Mashigar Hormuz na tsakanin Iran da Oman ne.

Taswirar tekun ta nuna ɓangarorin da suke da kyau a tsaya, da wuraren da ba a so a tsaya da kuma tudun mun tsira a tsakanin ɓangarorin biyu.

Idan tankokin mai za su wuce, sai su wuce ta kusa da tsibirin Greater da Lesser Tunb - inda ake takun-saƙa tsakanin Iran da ƙasashen Larabawa kan mallakinsa.

Masana sun ce yaƙi na cikin abubuwan da suke jawo tsaiko a hada-hada ta mashigar kamar yadda ya faru a yakin Iran da Iran a shekarar 1980 zuwa 1988.

■ Muhimmancin mashigar

Hukumar ƙididdigar makamashi ta Amurka US Energy Information Administration (EIA) ta ƙiyasta cewa a farkon shekarar 2023 an yi dakon kusan ganga miliyan 20 na fetur a a kullum ta tekun.

Wannan ke nufin ana kasuwancin kusan dala biliyan 600 na makamashi duk shekara ta tekun.

Duk wani tsaiko a tekun zai iya jawo matsala a hada-hadar man fetur a duniya, wanda nan take za a iya gani ta hanyar tashin farashin man.

Farfesa Ahmad Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur da iskar gas da ke jami'ar Philomath da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Ya ce hanyar ruwa ce da ba ta girma sosai, amma take da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.

"Ita wannan mashiga hanyar ruwa ce wadda tsayinta bai wuce kilomita 33 ba, wadda ta a daidai ƙasar Iran. Kuma hanya ce da jiragen dakon ɗanyen man fetur ke wucewa a kullum."

Ya ce daga jiragen dakon man da ke wucewa ta hanyar, akwai na ƙasashen Saudiyya da Kuwait da Iraqi da sauransu.

"Kullum ana wucewa da gangar ɗanyen mai kusan miliyan 20. Kusan kashi 20 cikin 100 na ɗanyen mai da ake buƙata a duniya," in ji shi.

Masanin ya ƙara da cewa ƙasashen da aka hana fitar da su ne s**a fi sayar da man fetur mai sauƙi a kasuwannin duniya, wanda a cewarsa hakan ke taimakawa wajen rage farahinsa.

"Su ne s**a sayar da mai mai arha. Misali Iran, kowace ganga tana kashe mata dala 10 zuwa 15 ne, kuma haka sauran suke kashewa. Idan aka ce waɗannan ƙasashen ba sa fitar da mai, sannan kuma dama na sauran ƙasashen yana da tsada, sai farashinsa ya tashi."

Ya yi misali da ƙasar China, wadda ya ce kimanin kashi 90 na ɗanyen da take buƙata daga Iran take saye.

Farfesa Ahmad ya ƙara da cewa datse mashigar zai shafi duniya ne baki ɗaya, ba ma ƙasashen da yake yaƙin ba kaɗai.

"A duk lokacin da farashin mai ya tashi, tattalin arzikin duniya na girgiza, farashin kayayyaki na hauhawa. Wanda hakan ya nuna cewa kowa ma zai ji."

Ya ƙara da cewa ita kanta Iran da ta rufe mashigar za ta ji a jikinta, "saboda tana samar da aƙalla ganga miliyan huɗu a kullum wanda shi ne kashi biyar bisa 100 na ɗanyen man duniya," in ji shi, wanda ke nufin za ta samu ragowar kuɗin shiga.

■ Akwai wata hanya daban bayan tekun?

Saboda barazanar da ake yawan fuskanta ta datse mashigar a shekarun da s**a gabata ne ya sa ƙasashen da suke dakon man fetur a yankin s**a samar da wata hanyar daban.

Wani rahoton EIA ya ce Saudiyya ta fara amfani da bututun gabas maso yammaci mai nisan kilomita 1,200, wanda za a iya tura ganga miliyan 5 a kullum.

A shekarar 2019, Saudiyya ta gyara wasu bututun gas domin su yi ɗaukar ɗanyen man fetur.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta haɗa gaɓar tekunta na tudu da gaɓar Fujairah da ke gaɓar Oma da bututun da zai iya ɗaukar gangan mai miliyan 1.5.

A watan Yulin 2021, Iran ta ƙaddamar da bututun Greh-Jask, wanda zai iya jigilar mai zuwa gaɓar Oman. Yanzu haka bututun zai iya ɗaukar ganga 350,000 a kullum.

Rahoton EIA ta ƙiyasta cewa waɗannan hanyoyin za su iya jigilar ganga miliyan 3.5 a kullum - kusan kashi 15 na man da ake jigila ta tekun a kullum.

Daga BBC Hausa

Me ya sa shugaban mulkin sojin Burkina Faso ke shiga zukatan al'umma?Shugaban mulkin sojin Burkina Faso mai matuƙar kwar...
16/05/2025

Me ya sa shugaban mulkin sojin Burkina Faso ke shiga zukatan al'umma?

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso mai matuƙar kwarjini, kyaftin Ibrahim Traore ya koƙarta wajen mayar da kansa tamkar wani jagora mai iza wutar kishin Afirka da kuma ƴantar da ƙasarsa daga abin da ya kira danniya na ƙasashen yamma da mulkin mallaka.

Wannan mahufa tasa ta ratsa ƙasashen Afirka har da wasu sassan duniya, inda masu sha'awar salonsa ke kallon shi a matsayin wanda ke bin sawun fitattun jagororin Afirka kamar Thomas Sankara - mai ra'ayin sauyi.

"Tasirinsa mai girma ne. Na sha jin ƴan siyasa da marubuta a ƙasashe kamar Kenya na cewa: 'Shi ne mutumin da ya dace', in ji Beverly Ochieng, babbar mai bincike a kamfanin bayar da shawarwari na Contol Risks.

"Bayanansa sun yi daidai da rayuwar wannan zamani, lokacin da ƴan Afirka ke dora ayar tambaya kan dangantakar Afirka da ƙasashen Yamma da kuma dalilin da ya sa talauci ya yi katutu a nahiyar da ke da tarin arziƙi."

Bayan karɓe mulki ta hanyar juyin mulki a shekarar 2022, gwamnatin Traore ta raba hanya da uwargijiyarta Faransa inda tare da ƙulla ƙawance da Rasha ciki har da tura dakarun ƴan sa kai na Rasha.

Mulkinsa ya aiwatar da manufofin tattalin arziƙi, ciki har da kafa kamfanin haƙar ma'adinai na gwamnati wanda ke karɓar kashi 15 na hannun jari a ayyukan kamfanonin ƙetare tare da buƙatar koyar da ƙwarewa ga 'yan ƙasa.

Wannan doka ta shafi dukkan kamfanoni, ciki har da kamfanin haƙar zinare na Rasha da Nordgold, wanda aka ba lasisin wani sabon aiki a watan Afrilu kan saka hannun jari a wani kamfanin haƙar zinare na Burkina Faso. A wani abin da Traoré ke kira "juyin juya hali," gwamnatin sojin na gina matatar zinare da kuma kafa wuirin ajiyar zinare na ƙasa — karo na farko a tarihin ƙasar.

A daya bangaren kuma, kamfanonin Yammacin duniya na fuskantar ƙalubale inda kamfanin Sarama Resources daga Ostiraliya ya ɗaukaka ƙara kan Burkina Faso bayan ta soke lasisin haƙar ma'aidnan zinare. Haka kuma, gwamnatin ta ƙwace wasu ma'adinan zinare guda biyu da kamfani daga Biritaniya ke da su, tana shirin kwace wasu ƙarin ma'adinai.

Masanin tsaro daga Afirka ta Kudu, Enoch Randy Aikins, ya shaida wa BBC cewa waɗannan sauye-sauyen Traoré sun ƙara masa farin jini a nahiyar. "Yanzu haka, ana iya cewa shi ne shugaban ƙasa mafi shahara a Afirka," in ji Aikins.

Shaharar da shugaba Ibrahim Traoré ke samu yanzu ta ta'allaka ne da amfani da shafukan sada zumunta, ciki har da bidiyoyi na karya da aka kirkira da fasahar AI waɗanda ke nuna fitattun mawakan duniya kamar R. Kelly, Rihanna, Justin Bieber da Beyoncé suna yabon shi—duk da cewa ba su taɓa yin hakan ba.

Sunansa ya karade nahiyar Afrika bayan wani jawabi mai zafi da ya gabatar a taron kolin Rasha da Afrika a shekarar 2023, inda ya buƙaci shugabannin Afrika da su daina zama kamar 'yan amshi na ƙasashen yamma. Kafofin yada labarai na Rasha sun yaɗa jawabin sosai, suna tallafa masa a matsayin gwarzon masu kishin Afirka.

Shahararsa ta karu sosai a duniya baki daya, musamman a tsakanin 'yan asalin Afrika da ke zaune a ƙasashen yamma kamar Amurka da Birtaniya. Wata 'yar jarida mai suna Ochieng ta ce kalamansa sun taɓa zuƙatan waɗanda s**a taba fuskantar wariyar launin fata da mulkin mallaka.

Har ma mawakin Amurka Meek Mill ya bayyana jin dadinsa da Traoré a shafinsa na X, kodayake ya yi kuskure wajen kiransa da "Burkina Faso" maimakon sunansa, wanda daga baya ya goge.

Amma ba kowa ke kallon Traoré a matsayin gwarzo ba. Shugaban Faransa Emmanuel Macron yana s**ar shi. Macron ya zargi Rasha da China da janyo juyin mulki a ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka a Afrika.

Duk da shahararsa, har yanzu Traoré bai cika alkawarinsa na kawo ƙarshen rikicin masu tayar ƙayar da baya a Burkina Faso ba, wanda yanzu ya shiga kasashe makwabta kamar Benin.

Gwamnatinsa ta kuma danne masu adawa da ita da kafafen yaɗa labarai da kungiyoyin farar hula, ta hanyar tura masu s**ar gwamnati zuwa filin daga don yaƙi da masu tayar da kayar baya.

A cewar Rinaldo Depagne, mataimakin daraktan cibiyar nazari ta International Crisis Group, Think-tank a Afrika, shaharar Ibrahim Traoré na da nasaba da kasancewarsa matashi a ƙasa mai yawan matasa, inda shekarun mutane ke tsakani da talatin kuma shekara goma sha bakwai a matsayin matsakaicin shekaru.

"Yana da ƙwarewar amfani da kafafen watsa labarai kuma yana amfani da tarihin Thomas Sankara wajen ƙarfafa kansa," in ji shi.

Sankara, wanda ya hau mulki ta hanyar juyin mulki a 1983 yana da shekaru 33, inda ya zama gwarzo kafin a kashe shi a wani juyin mulki a 1987 wanda ya dawo da Burkina Faso karkashin mulkin mallakar Faransa—har zuwa lokacin da Ibrahim Traoré ya karbi mulki.

Farfesa Kwesi Aning daga Ghana, ƙwararre kan tsaro ya ce shaharar Traoré na nuna sauyin siyasa da ke faruwa a yammacin Afrika. Wani bincike na Afrobarometer a 2024 da aka gudanar a ƙasashe 39 ya nuna raguwar sha'awar amfani dimokuraɗiyya ƙasashen Yamma, kodayake har yanzu ita ce mafi shahara.

Ya ƙara da cewa Traoré yana bayar da wata hanya ta daban, yana kuma dawo da zamanin 'yan gwagwarmaya na bayan samun 'yanci kamar Kwame Nkrumah na Ghana da Kenneth Kaunda na Zambia, da kuma daga baya Thomas Sankara da Jerry Rawlings na Ghana.

Ibrahim Traoré ya dauki hankula a bikin rantsar da Shugaban Ghana John Mahama a watan Janairu, lokacin da ya isa sanye da kayan soji da bindiga a kugunsa, lamarin da ya fi jan hankali fiye da sauran shugabannin Afrika guda 21 da s**a halarta.

Masanin tsaro Prof. Kwesi Aning ya ce, samartaka da ƙwarin gwiwa da halayyar janyo jama'a da Traoré ke da su sun bambanta da shugabannin Afrika da s**a tsufa.

Salon mulkinsa da tallafawa talakawa da jawaban jan hankali da goyon bayan Rasha da gwamnatin sojin da Traoré ke jagoranta ya samu yabo daga ƙungiyoyin ƙasashen duniya.

Hukumar IMF ta ce duk da ƙalubalen tsaro da ƙasar ƙarƙashin jagorancin shugaban sojin ke fuskanta, an samu ci gaba wajen haɓakar kuɗaden shiga da daƙile yawan albashi, da ƙarin kashe kudi a fannin ilimi da lafiya, tana hasashen tattalin arziki zai kasance mai karfi a shekarar 2025.

Bankin Duniya ma ya bayyana cewa kason talauci mai tsanani a Burkina Faso ya ragu zuwa kashi 24.9%, saboda ci gaba a ɓangaren noma da ayyukan hidima, ko da yake hauhawar farashi ta tashi daga kashi 0.7% a 2023 zuwa 4.2% a 2024.

Sai dai dangantaka da Amurka da Faransa na ci gaba da kasancewa cikin tsami, shugaban rundunar Amurka ta Afrika, Janar Michael Langley, kwanan nan ya zargi Traoré da amfani da zinaren Burkina Faso don kare gwamnatin sojarsa maimakon amfani da shi don amfanin kasa.

Waɗannan kalamai da aka yi a gaban kwamitin majalisar dattawan Amurka sun fusata masoyan Traoré. Daga bisani kuma, gwamnatin sojan Burkina Faso ta ce ta dakile yunkurin juyin mulki da aka shirya daga Ivory Coast – ƙasar da Janar Langley ya kai ziyara nan gaba kadan.

Ivory Coast ta musanta hannu a yunkurin juyin mulki da aka ce an shirya daga kasarta, yayin da rundunar Amurka ta Afrika (AFRICOM) ta bayyana cewa ziyarar Janar Langley ta mayar da hankali ne kan matsalolin tsaro da s**a haɗa da "tsattsauran ra'ayi da tashin hankali".

Sai dai gwamnatin sojan Burkina Faso ta shirya babban zanga-zanga a babban birnin ƙasar, tana zargin "mulkin mallaka da wakilansu" da kokarin kifar da Captain Traoré.

Wani mawaƙi mai suna Ocibi Johann ya ce: "Saboda Colin Powell ya yi ƙarya, Iraq ta lalace. Obama ya yi karya, an kashe Gaddafi, toh mu a wannan karon, karya ba za ta yi tasiri a kanmu ba." Zanga-zangar goyon baya ga Traoré ta gudana a wasu biranen duniya, ciki har da London.

Traoré ya gode wa magoya bayansa ta shafukan sada zumunta inda ya ce: "Tare da hadin kai, za mu fatattaki mulkin mallaka da sabbin hanyoyin danniya don samun Afrika mai 'yanci da ƙima."

Ko da yake ba a san makomar Traoré ba, shi da shugabannin soja na Mali da Nijar sun girgiza yankin Yammacin Afrika ta hanyar koran sojojin Faransa da ficewa daga kungiyar ECOWAS da kafa sabuwar kawance da sanya harajin kashi 0.5% kan kayayyakin shigowa ƙasar.

BBC Hausa ✍🏾

Adresse

Niamey

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Jamhuriya publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Raccourcis

Partager