21/08/2026
Gwamnatin jiha, fadar Sarkin Musulmai, jami’an tsaro, duka sun zuba idanu akan abin da ke faruwa da su Malam Murtala Asada.
Malam Murtala ma ya ce kwamishinan ƴan sandar jihar ya ƙi saurarar su, ya ce sai gwamnati ta fara saurarar su tukunna.
Tsawon kwanaki wani tsagera yana ta yin bidiyo yana alwashin sai ya k*she su amma har yanzu yana yawo a kan titin garin Sokoto ba tare da an ko da gayyace shi ba.
Babban laifin su Malam Murtala shi ne kawai saboda suna yaƙi da ƴan t*addan da s**a addabi al’ummarsu, s**a hana su zaman lafiya.
Masu ruwa da tsaki sun zuba idanu suna so sai bayan mai faruwa ta faru sannan sai su fito su jajanta wa mutane.
Game da hujjar yin ɓatanci da shi wannan ɗan t*adda ya dogara da ita, shin mene ne laifin Malam Murtala da ya shigo cikin jerin waɗanda yake so ya k*she bayan ba shi ne ya faɗi maganar ba?
Sannan ina hukuma da ba za ta iya k**a shi Malam Musa Lukuwa ɗin da ya yi maganar ba, a gurfanar da shi a kotu bisa wannan zargi, sai a tabbatar da laifinsa ko akasin hakan?
Me ya sa mutanen gari masu hankali ba su nemi ɗaukar mataki ba sai wani ɗan t*adda wanda kotu ta ɗaure shi bisa laifin kis*n kai amma ake zargin gwamnati ta fito da shi?
Lallai mu daina batun ganin sauyi matuƙar muna zaɓen wanda ya k**ata a yi wa adalci da wanda za tauyewa.
Wato saboda su Malam Murtala suna yaƙi da masu garkuwa da mutane ko? Ku kuma ba kwa so a taɓa su!