08/09/2026
KOTU TA ƘI BAYAR DA BELIN KHADIJA SA’IDU DA AKE ZARGI DA KASHE MIJINTA
Kotun Majistare mai lamba 9 a Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Haulatu Magaji, ta yi watsi da buƙatar belin Khadija Sa’idu, wadda ake zargi da kashe mijinta, Auwal Adam, makonni bakwai bayan aurensu.
A zaman kotun, lauyan Khadija ya nemi a ba ta beli, sai dai mai gabatar da ƙara daga gwamnatin Kano ya yi ƙararrawa, yana mai cewa tuhumar da ake yi mata ta shafi kisan kai.
Lauyan ya kuma shaida wa kotun cewa ana jiran shawarwari daga Ma’aikatar Shari’a ta jihar Kano.
Kotun ta ƙi bayar da belin Khadija, sannan ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa 30 ga Satumba, 2026.
Tun da farko dai, an zargi Khadija da daba wa mijinta, Auwal Adam, wuƙa a yayin da ake zargin ya hana ta zuwa wani gidan biki a unguwar Hayin Lawali da ke Zango, ƙaramar hukumar Ungogo, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.