Saye Online Reporters

Saye Online Reporters Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Saye Online Reporters, Media Agency, Saye Bichi Local Government Area, Bichi.

An bude wannan gidan jaridane domin Kawo Maku labarai Akan Al'amuran Yau da Kullum har zuwa kasashen ketare, domin ji da Sanin Inda aka Kwana Da Kuma Inda Tashi ta Hanyar Kawo maku sahihan labarai

Founder/CEO
Hamza Danladi Saye

09/06/2026

Innalillahi wa'enna Illaihir raje'un.
Allah yayiwa Matar Yusuf Malam Malam Rasuwa.
Za'ayi Jana'iza Yanzu Da Safen nan a gidansa.

08/06/2026

Allah yasa Albarka, Allah ya kawo Kasuwa.
Addres: Cyber City Plaza, Jaba Sabon T**i, Behind Aminu Kano International Airport Kano, Jaba Kano State.



A wannnan shekarar ma an fara shimfiɗa sinadaren rage zafin rana a hanyiyin MinaHukumomi a Saudi Arabia sun fara aiwatar...
19/05/2026

A wannnan shekarar ma an fara shimfiɗa sinadaren rage zafin rana a hanyiyin Mina

Hukumomi a Saudi Arabia sun fara aiwatar da shimfiɗa wani sinadari na rage zafin rana a kan hanyoyin yankin Mina domin rage tsananin zafin da alhazai ke fuskanta yayin gudanar da aikin Hajji. Ana sa ran wannan sinadari zai rage zafin hanyoyi da tsakanin digiri 15°C zuwa 20°C.

Sai dai da dare, bayan mahajjata sun koma wuraren hutawarsu, hanyoyin za su fara sakin zafin da s**a tara da rana ta hanyar amfani da fasaha da tsarin kimiyya.

Bayanai daga kafofin yaɗa labaran Saudiyya sun nuna cewa, zafin rana a hanyoyin Makkah da Mina kan kai har digiri 70°C a wasu lokuta.

Wannan fasaha, wadda ƙasar ta fara amfani da ita kwanan nan, na da nufin rage wahalar zafin da alhazai ke sha a lokacin aikin Hajji, musamman a kwanakin da suke shafe kusan huɗu suna zama a Mina.

Masha Allahu

A cikin Kruger National Park a ƙasar South Africawani gogaggen mai kula da namun daji mai suna Sipho Nkosi ya sami bugaw...
19/05/2026

A cikin Kruger National Park a ƙasar South Africa

wani gogaggen mai kula da namun daji mai suna Sipho Nkosi ya sami bugawar zuciya (heart attack) yayin da yake sintiri shi kaɗai.

An gano motarsa babu kowa a ciki, lamarin da ya sa aka fara neman sa.

Abin da kyamarorin sa ido da ke cikin dajin s**a nuna ya taɓa zuciyar duk wanda ya kalli bidiyon.

Wani tsohon toron giwa wanda masu kula da dajin ke kira “Mnumzane” (kalma ce ta harshen Zulu wadda ke nufin “Yallabai”), shi ne ya gano gawar Sipho.

Na tsawon kwanaki uku da dare uku, giwar ta ƙi barin wajen, yayi tsaye tare da gadin gawar, tana shafa Sipho a hankali da hancinta (trunk), tana korar kuraye da sauran dabbobin da s**a kusanci gawar, har ma tana rufe wasu sassan gawar da rassan itatuwa da ganyaye.

Har a daren rana ta uku giwar tana wurin, tana nuna alamar baƙin ciki, tana karkada jikinta a hankali kusa da mai kula dasu da ya rasu.

Sai bayan tawagar ceto ta iso da motoci ne Mnumzane ta ja baya, tana kallo cikin nutsuwa yayin da ake ɗaukar gawar Sipho...😭

Daga baya, jami’an gandun dajin sun tabbatar da cewa Sipho ne ya ceci wannan giwa tun tana ƙaramar jaririya, bayan mafarauta sun kashe mahaifiyarta shekaru da s**a wuce, Giwar ba ta manta da wannan alheri ba... 🐘

Ɗaya daga cikin abokan aikinsa da ya kalli bidiyon ya ce;
“Ba ta zo domin yin bankwana ba, tazo ne domin tabbatar da cewa babu wanda zai wulaƙanta gawar wanda ya ceci rayuwar ta tun tana ƙarama

Har yanzu Mnumzane yana yawan dawowa wannan wuri, wanda yasa masu kula da gandun dajin suke ajiye ruwa da ‘ya’yan itatuwa a wurin domin girmama su duka biyun.

Allah Yasa mu dace

Sunanta Baba Sa'ade dake tsohuwar Kasuwa a Potiskum jihar Yobe, Taliya murjin hannu take dafawa ta sayar a gidanta. Ba i...
17/05/2026

Sunanta Baba Sa'ade dake tsohuwar Kasuwa a Potiskum jihar Yobe, Taliya murjin hannu take dafawa ta sayar a gidanta. Ba iya gwauraye ba, masu aure ma daga kusa da nesa suna zuwa gidanta su ci Taliya ko su tafi dashi.

Da kudin sayar da Taliya ta aurar da yaranta.

Da kudin Taliya gashi ta biyawa kanta zuwa aikin Hajji. Allah ubangiji ya amsa Addu'o'inta.

Sai dai ta bar Gwaurayen tsohuwar kasuwa da yunwa 🤣 suna ta korafi 😁

Allah Ubangiji Ya Amsa Addu'a Ameen Thumma Ameen

YANZU-YANZU: Wata mummunar zanga-zanga ta barke kan matsalar rashin tsaro da ƴan biπdiga a ƙaramar hukumar Gwarzo ta jih...
17/05/2026

YANZU-YANZU: Wata mummunar zanga-zanga ta barke kan matsalar rashin tsaro da ƴan biπdiga a ƙaramar hukumar Gwarzo ta jihar Kano, inda dandazon matasa s**a rufe titunan garin s**a kuma cin na wuta a sakatariyar ƙaramar hukumar tare da kiran gwamnati da ta kawo musu ƙarshen ƴan biπdiga da suke addabar su.

Me za ku ce akan hakan

Muna jiran ra'ayoyinku a comment section

Menene dalilin yi mata photo na Dora kan social media???Dalili shine ita magana take munema mata tai makon daxata mallak...
16/05/2026

Menene dalilin yi mata photo na Dora kan social media???

Dalili shine ita magana take munema mata tai makon daxata mallaki tata kurar ruwan shine tane meni😢

Malama aisha ta dade tana sana'ar seda ruwa
Amma bata gaza da wannan sana'ar ba tata se a yanxu daxata aurar da diyar ta budurwa
Take neman tai makon mu😢

Wannan kurar datake debo ruwa haya take karbowa naira 500 🥹
Idan tatashi seda ruwan ta biya kudin hayar kura

Sannan tanada yara mata kanana
A ahaka xa aci dasu domin su rufama kansu asiri

Tabbas tana bukar tai makon mu😭🤲🏾

Domin samun
Tabbacin labari

+2348031820624

Allah ya sakawa iyayen mu da Alkhairi Ameen.

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Rahotanni sun ce ƙasar 1$ra’ila ta nemi a dakatar da tauraron ɗan wasan Sipaniya Lamine Yamal daga buga...
13/05/2026

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Rahotanni sun ce ƙasar 1$ra’ila ta nemi a dakatar da tauraron ɗan wasan Sipaniya Lamine Yamal daga buga wa ƙasar Sipaniya wasa bayan ya daga tutar Falasdinu yayin bikin murnar lashe kofin gasar ƙwallo. Sai dai Firaministan Sipaniya Pedro Sánchez ya yi watsi da buƙatar, yana mai cewa wannan shirme ne kuma abin dariya ne, domin abin da 1$ra’ila ke aikatawa a Gaza na k1san ƙare dangi kan mata, yara da tsoffi ya k**ata a hana ta buga kowace irin gasa ta duniya.

Pedro Sánchez ya bayyana cewa maimakon hukunta Yamal, ƙasar Sipaniya za ta karrama shi saboda abin da ya kira goyon baya ga Falasɗinawa. Haka kuma ya ce za a ci gaba da daga tutar Falasdinu a bukukuwa da taruka daban-daban a faɗin Sipaniya.

Me za ku ce?

SUNA BUKATAR A KAWO MUSU AGAJIWani Magidanci da yake aiki da hukumar gidan yari yayi yunkurin hallaka matarsa na aure ta...
13/05/2026

SUNA BUKATAR A KAWO MUSU AGAJI

Wani Magidanci da yake aiki da hukumar gidan yari yayi yunkurin hallaka matarsa na aure ta yankar yankanta da wuka

Ya yi amfani da wuka wajen datse hannayenta, ya caka mata wuka a cikinta, ya sara mata wuka a goshinta da keyarta da kafafu da cinyoyinta da bayanta

An kai matar Asibiti rai a hannun Allah, bata cikin hayyacinta sak**akon munanan yanka da ya mata da wuka

Abin ya faru a cikin garin Jere North dake karamar hukumar Kagarko jihar Kaduna

Yayan matar mai suna Ismail Abdullahi nambar wayansa 08144473946, ya shaida min cewa kanwarsa ta samu sabani da mijinta har ta dawo gida tayi sati biyu, daga bisani yazo biko ta koma, tana komawa ne ya aikata mata wannan ta'addanci

Kuma har zuwa yanzu basu san dalilin da yasa ya tashi kasheta ba, ganin cewa ba'a wani dauki matakin da ya dace a kansa ba, Ismail Abdullahi ya rokeni akan na sanar domin kungiyoyin kare hakkin bil'adama su kawo musu dauki don basu da karfin da zasu iya shari'a da mijin

Wannan hoton shine na matar bayan an fara mata dressing a Asibiti, akwai hotunan da ba zasu dauruba saboda kiyaye dokokin Facebook

Muna fata Allah Ya isar mata, ya bata lafiya

Source: Datti Assalafy

INNALILLAH WA INNA ILAIHI RAJI'UN.Masu garkuwa da mutane sun k**a kuma sun hallaka Alhaji Hon Abba Anas Adamu Laushi aka...
11/05/2026

INNALILLAH WA INNA ILAIHI RAJI'UN.

Masu garkuwa da mutane sun k**a kuma sun hallaka Alhaji Hon Abba Anas Adamu Laushi akan hanyar Kaduna zuwa Abuja zai tafi sayan tikitin tsayawa takaran kujeran Gwamna na Jihar Jigawa a jam'iyyar ADC

Su biyu ne barayin s**ayi garkuwa da su ranar juma'a, s**a bukaci a basu kudin fansa Naira Miliyan 75, dayan ya samu ya gudu, shi kuma Hon. Abba Anas sun kashe shi bayan sun karbi kudin fansar, yanzu haka za'a kawo gawarsa Kano

Hon Abba Anas Tsohon dan Majalisar Tarayya ne tun daga 2007 zuwa 2011 wanda ya wakilci kananan hukumomin Birniwa, Guri da Kirikasamma a jihar Jigawa

A yanzu haka yana neman kujeran Gwamnan jihar Jigawa a jam'iyyar ADC, a kan hanyar zuwa sayan form ya hadu da ajalinsa a hannun marassa imani

Allah ya gafarta masa Ameen

Address

Saye Bichi Local Government Area
Bichi
703101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Saye Online Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share