30/07/2021
MALAM KA JI TSORON ALLAH - Shugaban Sojojin Najeriya.
SHIN SHI MA SHUGABAN SOJOJIN BAKIN CIKI YAKE YIWA PANTAMI TINDA Dr Bashir Dorayi KUN CE BAKIN CIKI YAKE YI?
Dr. Isa Ali Pantami Kaji Tsoron Allah!!!!
Idan kayi naka aiki to tabbas ka sauke nauyin da Allah ya dorama, Saura jami’an tsaro.
Ita tunatarwa tana amfanar mumini ne.
Duk duniya najeriya kadai ake sace dalibban makaranta 300 alokaci daya har su share tsawon wata uku hannun yan bindiga kuma ba’a gano suwaye ba.
Masu Karatu ku Daure ku Karanta Har Karshe, Sannan don Allah kuyi Sharing Domin Sako Ya Isa Hannun Mai Shi.
Babban Sako Zuwaga Maigirma Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Ibrahim (Pantami) FNCS, FBCS, FIIM, MCPN.
Farkon farawa Kabi wannan link kaji wayar da wani maigarkuwa da mutane yayi da wata mata 👇
https://youtu.be/RW-wocCpCBQ
Amatsayin ka na babban malami, masani addinin muslunci zanyi amfani da wannan dama domin nafara bude wannan wasikar da wa’azi zuwa gareka.
Dr. Isa Ali Pantami Kaji Tsoron Allah!!!!
Soyayyar dake tsakanina dakai bazata hanani gayama gaskiya ba, tabbas ni masoyinka ne ba makiyinka ba.
Kasani cewa kashe-kashen da akeyi a najeriya da zubar da jini wallahi Allah zai tambayeka idan alkiyama ta tsaya, a ranar da bakada karfin iko, a ranar da bakada matsayi ko kujerar mulki, a ranar da bakada wani mai ceton ka, a ranar da ayukkan alkhairi kadai ke ceton bayi zuwaga rahamar Allah.
Dr. Isa Ali Pantami kaine babban ministan sadarwa na tarayyar najeriya, duk wata waya da akeyi a najeriya kanada kamisho aciki, idan ma takasance wayar ta alkhairi ce ko ta sharri ce.
An rantsar dakai akan wannan kujerar ranar laraba 21/08/2019 yau kwanan ka dari bakwai da bakwai (707) akan wannan kujerar.
Menene shirin dakayi domin magance matsalar ta’addanci a najeriya ta hanyar kujerar ka amatsayinka na babban ministan sadarwa???
A najeriya ake sace bayin Allah a nemi miliyoyin kudin fansa ta wayar salula 📱 wane mataki ka dauka ko kake shirin dauka domin dakatar da wannan matsalar.???
Kasani cewa wannan matsayin da Allah ya azaka akai jarrabawa ne agareka, hakazalika Allah zai tambayeka akan ya ka gudanar da shugabancin ka alokacin da kake kan wannan kujerar.
Samar da kudin shiga ga gwamnatin tarayya bashi bane mafi muhimmanci,
Allah bazai tambayeka meyasa baka tarawa najeriya kudin shiga ba alokacin da kake kan wannan kujerar.
Abinda Allah zai tambayeka shine meyasa ake sace bayin Allah, kuma ake amfani da hanyar sadarwa domin neman kudin fansa baka dauke mataki ba. Meyasa ake amfani da hanyar sadarwa ake zubar da jinin bayin Allah baka dauke mataki ba. Bayan kuma kaine babban mai jagorantar kujerar ministan sadarwa na wannan kasar tamu najeriya.
Idan bazaka manta ba a shekarar 2013 da 2014 a lokacin gwamnatin shugaba goodluck jonathan mai malfa, kaine ke kuka kana zubar da hawaye 😭😭 akan irin ta’addancin da akeyi a najeriya.
Samar da kudin shiga ga gwamnatin tarayya bashi bane aikin ka, idan ma shine aikin ka to tabbas wannan aikin bazai tsiratar dakai a gaban Allah ba idan Alkiyama ta tsaya.
Nemawa matasa aiki bashi bane mafita agareka.
Nemawa al’umma ayukka daga gwamnatin tarayya wannan bashi bane aikinka, idan ma shine aikinka to tabbas bazai tsiratar dakai ba agaban Allah idan Alkiyama ta tsaya.
Abu daya zakayi ka tsira daga fushin Allah idan alkiyama ta tsaya shine:
Kowane dan najeriya yanada layin kira acikin wayar sa (sim card), kuma kowane layin kira anyi rigistar sa da katin shaidar zama dan kasa (NIN National Identification Number). Hakazalika kowanne NIN yana dauke da rahotannin kowane dan kasa k**ar haka:
(1)
Sunan mai wannan sim card
Sunan mahaifi
Sunan mahaifiya
(2)
Sunan garin ku ko kauyen da kake (Town)
Sunan kasar ka (County)
Sunan jahar ka (State)
Sunan karamar hukumar ka (LGA)
Sunan unguwar ka da gidan ku (Address)
(3)
Ranar haifuwar ka (Date of birth)
Kasar da aka haife ka (Country of birth)
Jahar da aka haife ka (State of birth)
Karamar hukumar da aka haifeka (LGA of birth)
(4)
Ranar haifuwar mahaifiyar ka
Ranar haifuwar mahaifin ka
A ina aka haife mahaifiyar ka
A ina aka haife mahaifinka
Yaushe ne aka haife mahaifinka
Yaushe ne aka haife mahaifiyar ka
(5)
Kai wane jinsi ne mace ko namiji
Kanada zanen al’ada a fuskar ka
Gashin kanka wane kala ne (Hair colour)
Tsayin ka (height)
Nauyin ka (Weight)
Shekarunka (Age)
Kalar fatar jikinka (Skin colour)
NIN number ka
Duk wanda yayi kiran waya a najeriya hukumar sadarwa nada masaniya akan wayakira sannan wa ake kira, daga ina akayi kiran, sannan mintuna nawa akayi ana wannan kiran, miye sunan wanda yayi kiran SALIHU, BELLO, UMAR, SUNDAY, ko GODWIN ne duk hukumar sadarwa tasan da wannan.
Wanda yayi kiran wane gari yake BORNO, KADUNA, LAGOS, ZAMFARA, SOKOTO, OGUN ko ENUGU duk hukumar sadarwa tasani.
Wanda yayi wannan kiran wane unguwa yake sannan a unguwar wane gida yake, waye mahaifinsa sannan waye mahaifiyarsa. Duk hukumar sadarwa tasani.
Wanda yayi kiran wayar shekarunsa nawa 18, 20, 25, 30, 32, 38, ko 40 duk hukumar sadarwa tasani.
Wanda yayi kiran wayar dogo ne ko gajere, baki ne ko fari, bahaushe ne ko inyamuri, fulani ne ko bayarbe. Duk hukumar sadarwa tasani.
Domin hukumar sadarwa nada (stored data) all collected informations na kowane mai amfani da layin kira a najeriya.
Idan har hakane, to taya za’ayi ace a wannan kasar tamu najeriya yan bindiga zasu sace mutum kuma har su samu damar kiran waya na tsawon wata daya suna neman kudin fansa, da har za’a kasa k**a su. Bayan kuma kowane layin kira yanada rahoton wanda yake amfani dashi har da na iyayensa da iyalansa.
Amfani da layin kira (sim card) awurin magance matsalar tsaro shine babban abinda duk kasashen duniya keyi awurin yaki da ta’addanci k**ar America 🇺🇸, China 🇨🇳, France 🇫🇷, United Kingdom 🇬🇧, Dubai 🇰🇼, Saudi Arabia 🇸🇦, India 🇮🇳, da duk wata kasar duniya datasan daraja da kimar dan adam.
Kai ka isa kaje kasar Dubai kayi ta’addanci???
Acikin mintuna 30 jami’an tsaro zasu cafke ka
Kai ka isa kaje kasar China kayi ta’addanci???
Acikin mintuna 30 jami’an tsaro su cafke ka
Sai awannan kasar tamu najeriya dan ta’adda zai sace mutum yanemi kudin fansa miliyan 30 tsawon wata daya yana waya da iyalan ka amma ba’asan wayake kiran ba.
Domin Magance Matsalar Ta’addanci a Najeriya dole sai hukumar sadarwa ta wannan kasar ta tashi tsaye da gaskiya da adalci k**ar haka:
Duk wanda ya kira waya yana neman kudin fansa to tabbas a garzaya zuwa ofishin jami’an tsaro abada wannan lamabar waya da yayi amfani da ita awurin kiran, jami’an tsaro su nemo rahoton waye shi a kamfanin sadarwa na (MTN, GLO, 9mobile ko AIRTEL). Idan aka tabbatar da waye shi a gaggauta kamo iyalansa da iyayensa a rufesu a ofishin hukuma.
Tabbas idan kayi haka Dr. Isa Ali Pantami to babu shakka ka sauke nauyin da Allah ya azama a gefen tsaro.
Idan kuma bakayi haka ba, to bakada amsar da zaka ba Allah idan akazo a farfajiyar alkiyama, ranar da kowane dan adam zai amsa tambayoyi daga ubangiji mahalicci.
Domin kuwa rayuwar dan adam daya tafi duniya da abinda ke cikin duniya daraja awurin Allah.
Rayuwar dan adam daya tafi dakin ka’aba daraja da girma awurin Allah.
Da akashe ran mutum daya gwanda a rushe dakin ka’aba yafi sauki awurin Allah inji Annabi Muhammad S.A.W
Kenan kudin da hukumar sadarwa ke tarawa gwamnatin tarayya basu bane mafita matuqar ana kashe rayukan al’umma.
Kenan nemawa matasa aiki ko nemo aikin bunkasa kasa daga gwamnatin tarayya bashi bane mafita matuqar ana kashe rayukan al’umma.
Matukar ana zubar da jinin Al’umma, kuma ace babu wata mafita duk wata kujera ko mukami yazama aikin banza.
DAGA KARSHE:
Kamar yanda nafada tun farko cewa ni ba makiyinka bane face masoyinka shine dalilin dayasa nace kaji tsoron Allah.
Kalmar kaji tsoron Allah sai masoyinka ne zai gayama.
Kamar yanda Allah S.W.T yace da Masoyinsa Annabi Muhammad S.A.W (Surah Ahzab Ayah ta daya)
Acikin kasashen duniya (195) Duk duniya wace kasace a yau takai najeriya ta’addanci da yan ta’adda????
Najeriya ita ce cibiyar ta’addanci ta duniya baki daya Boko Haram, ISWAP, Kidnappers, Yahoo, Yan fashin hanya, yan ta’addan IPOB, yan ta’addan Yoruba, yan ta’addan fulanin daji. A gefen ta’addanci Najeriya ce lamba daya.
Najeriya ita ce cibiyar zubar da jini ta duniya
Najeriya ita ce cibiyar garkuwa da mutane ta duniya, abinda muke acikin shirin film din turawa.
Najeriya ita ce cibiyar barayin gwamnati da zalunci.
Najeriya ita ce cibiyar talauci da yunwa da fatara da tsadar rayuwa.
Allah ya taimake mu yakawo mana karshen wannan bala’i. Ameen.
Sako Daga Wani Dalibin Makaranta:
Arewa Reporters