13/05/2026
Allah kasa kasar mu ta chanza
A nahiyar Afirka, siyasa ta kamata ta zama hanya ta kawo ci gaba, adalci da walwalar al’umma. Amma abin takaici, wasu daga cikin ’yan siyasa sun mayar da ita hanyar son rai da anfani da mulki ba tare da gaskiya da rikon amana ba. Mafi yawan matsalolin da muke fuskanta a yau suna faruwa ne saboda rashin bin doka da oda daga manyanmu.
Idan masu mulki ne da kansu basa mutunta dokokin kasa, ta yaya za a sa ran talaka zai bi doka yadda ya kamata? Domin gaskiya ita ce, idan babba ya gyara kansa kuma ya zama abin koyi, to wadanda suke kasa ma zasu bi sahu cikin sauki. Amma idan manya suna karya doka ba tare da hukunci ba, hakan yana rage darajar adalci a idon al’umma.
Kasashe masu cigaba ba wai saboda arziki kadai s**a ci gaba ba, a’a, sun ci gaba ne saboda akwai gaskiya, adalci da kuma hukunta duk wanda ya karya doka ko da kuwa wanene shi. Idan doka ta fara aiki akan manya ba tare da nuna bambanci ba, to talakawa ma zasu kara mutunta kasa da dokokinta.
Lokaci yayi da ya kamata mu dawo cikin hankalinmu, mu fahimci cewa zaman lafiya, hadin kai da yalwar arziki ba zasu samu ba sai an gina kasa akan tubalin gaskiya, rikon amana da adalci. Allah Ya shiryar da shugabanni da al’umma baki daya, Ya kawo mana zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
SANI SAGIR