24/09/2026
Alƙalin wasa na ƙasar Brazil, Anderson Daronco, ya sauya yanayin jikin sa bayan da hukumar ƙwallon ƙafa ta Brazil, CBF, ta ba shi shawarar rage nauyin jikinsa
Daronco, mai shekaru 45, ya shahara wajen kasancewa mai wadatun kafadu, amma kwamitin alƙalan wasa na CBF ya shawarce shi da ya rage kiba tare da sauya tsarin motsa jiki domin inganta yanayin jikinsa.
Alƙalin ya bi wannan shawara, inda ya yi nasarar rage nauyinsa da kilogram 12.😀
Wannan sauyi ya jawo hankalin masu bibiyar ƙwallon ƙafa, musamman ganin yadda kamanninsa s**a sauya cikin ɗan lokaci.
Daronco ya nuna cewa bin tsarin motsa jiki da kuma jajircewa na iya kawo gagarumin sauyi a jikin mutum