13/01/2026
Rahotanni sun bayyana cewa an gano mak**ai da harsasai a gidan tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Mallam Abubakar Malami, SAN da ke Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, lamarin da ya sa Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta buɗe sabon bincike a kansa.
Rahoton jaridar The Nation ya ce Hukumar EFCC ce ta fara gano mak**an yayin binciken da ta yi a gidan Malami. Sai dai, saboda mallakar mak**ai ba ta cikin hurumin EFCC, an mika dukkan kayan shaidar ga DSS domin gudanar da cikakken bincike.
Majiyoyi sun bayyana cewa adadin mak**an da aka gano ya yi yawa, lamarin da ya sa DSS ta ɗauki matakin bincike na musamman. Har yanzu ba a tabbatar da adadin mak**an ba a hukumance.
A halin yanzu, Malami—wanda aka ba shi belin kotu a makon da ya gabata tare da ɗansa Abdulaziz da matarsa Asabe Bashir—har yanzu yana tsare a Gidan Gyaran Hali na Kuje, Abuja, saboda gazawar cika sharuɗɗan belin.
A makon da ya gabata, SaharaReporters ta ruwaito cewa Malami na jinkirta cika belin da gangan, domin kauce wa sake cafke shi da DSS za ta yi bisa zargin da ke tattare da mak**ai da kuma zargin tallafawa ta’addanci. Rahotanni sun ce jami’an DSS sama da 50 sun kewaye Gidan Gyaran Hali na Kuje, a matsayin shiri na sake k**a shi idan aka sake shi bisa beli.
Rahotanni sun bayyana cewa: “Malami ya umurci lauyoyinsa su ja-belinsa a hankali, domin jami’an DSS na jiran fitowarsa su sake cafke shi kan zarge-zargen da s**a shafi ta’addanci da mak**ai.”
Wata majiya kuma ta tabbatar da cewa kayan mak**an da aka gano an mika su ga DSS domin a binciki asalin yadda s**a samu. “Yanzu Malami ne zai yi wa DSS bayani kan yadda mak**an s**a shiga gidansa,” in ji majiyar.OK