10/10/2023
MU NE MATSALAR KASARMU
Sheikh Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Bauchi yace:
Malam ka dubi yanda kasarmu ta lalace, idan wani abu ya faru, sai aje a nemo wani mai fashin baki a gidan radio yazo yayi fashin baki, sai kaga inda matsalar kasar tayi daban, inda fashin bakinsa yayi daban, shima wanda yake fashin bakin yana bukatar ayi masa fashin baki
Ai ka kalli kasar ka kalli makomar kasar, duk wanda zai kalli Kasarmu da hangen nesa ya kalli abinda zaije ya dawo ya san abubuwa a kasar sun lalace, matsalar Kasarmu shi ne hanyar cin abincin kasar, (matsalar kasar shi ne hanyar samun kudin kasar) ka gane???
(1) Lalacewar Ilmi shi ne hanyar samun kudin wadansu, lalacewar makarantun Gwamnati shi ne hanyar samun makurantun da ba na Gwamnati ba, idan makarantun Gwamnati s**a gyaru to makarantu private ba zasu samu mutane ba, kuma Malam wallahi wadannan masu makarantun private babu wanda zai sha kansu, ba Kwamishina ba ko Ministan Ilmi ba zai sha gaban su ba, wannan matsalar ta ilmi itace hanyar cin abincin su.
(2) Matsalar Man fetur itace hanyar samun kudin masu harkar mai, saboda wanda ya ke sana'ar mai idan aka samu wahalar mai abinda zai samu a sati biyu, in za'a je a latsa ne a gidan mai a samu sai ya shekara bai samu wannan kudin ba, don haka matsalar mai itace hanyar cin abincin sa.
(3) Matsalar wuta itace hanyar samun kudin wasu, wadannan masu harkar man fetur Wallahi ba Ministan Man fetur ba ko shugaban kasa sai yayi da gaske zai iya shan gaban su,
(4) Matsalar tsaro shi ne hanyar samun kudin wasu masu tsaron, idan aka zauna lafiya ba zasu samu kudin da suke so ba, saboda haka matsalar tsaro shine hanyar samun kudinsu wannan shi ne gaskiya, saboda haka matsalar mu itace hanyar samun kudinmu saboda haka matsalar bazata kare ba.
(5) Yanzu kasan iyakan kudin da ake samu ga matsalar Cronavirus?, wadansu sanadiyar hanyar arzikinsu shine hanyar Cronavirus, to idan ka dubi wannan itace matsalar kasarmu, yaushe ne Kasar zata gyaru?
Mu da ya kamata mu hada kudi da