27/08/2026
SAKON MURNAR CIKAR JIGAWA SHEKARU 35
Danmodi Concern Organization (DCO) na taya daukacin al’ummar Jihar Jigawa murnar cika shekaru 35 da kafuwarta.
Shekaru 35 ba karamin tarihi ba ne. Tafiya ce mai cike da nasarori, kalubale, darussa da kuma buri na ganin Jigawa ta zama jiha mai zaman lafiya, hadin kai, ilimi, lafiya, tattalin arziki da ci gaba mai dorewa.
A wannan rana ta tarihi, muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa ni’imar zaman lafiya da albarkar da Ya ci gaba da yi wa Jigawa. Muna kuma yabawa iyaye da magabata da s**a bayar da gudummawa wajen gina wannan jiha tun daga farko har zuwa yau.
Ya Allah! Ka kara wa Jigawa albarka. Ka zaunar da zaman lafiya a cikin garuruwa da kauyukanta. Ka hada kan al’ummarta, ka kare ta daga fitina, rikici da dukkan sharri.
Ya Allah, Ka bai wa shugabanninmu hikima, adalci da hangen nesa. Ka sanya shugabanci ya zama hanyar hidima ga al’umma, ba hanyar zalunci ba.
Ka bude wa matasan Jigawa kofofin ilimi, sana’a da aikin yi. Ka inganta harkokin lafiya da ilimi, ka bunkasa noma da tattalin arziki, sannan Ka sa Jigawa ta ci gaba daga karfi zuwa karfi.
Allah Ya albarkaci Jigawa State.
Allah Ya albarkaci al’ummarta.
Allah Ya kawo zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai dorewa.
Amin Ya Rabbal Alamin. 🤲🏽
BARKA DA CIKA SHEKARU 35, JIGAWA STATE! 💚🤍💚
Cikin girmamawa da fatan alheri,
Danmodi Concern Organization