23/09/2019
GWAMNA GANDUJE YA AMINCE DA NAƊIN MEMBOBIN HUKUMAR TALLAFAWA HARKOKIN KIWON LAFIYAR AL'UMMAR JIHAR KANO
DAGA Bashir Abdullahi El-bash
-Kafin Mu Ba Su Waɗannan Muƙamai, Sai Da Mu Ka Yi Nazari Game Da Tarihin Ayyukansu Na Baya - Gwamna Ganduje.
-Mun Kafa Wannan Hukuma Ne Kan Manufar Yi Wa Al'umma Aiki Da Kuma Tallafa Musu Gami Da Ciyar Da Fannin Lafiya Gaba, Ina Fatan Za Ku Kiyaye Da Wannan - Gwamna Ganduje.
Yau Lahadi, 22 ga watan Satumba, 2019.
Mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a wannan rana ya amince da naɗin membobin hukumar da aka kafa domin ta jiɓinci lamarin haɗa gudunmawar tallafawa harkokin kula da tsarin kiwon lafiya a Jihar Kano, wato" Kano State Contributory Healthcare Management Agency", waɗanda kuma naɗin nasu ya fara aiki ne nan take.
Daga cikin membobin hukumar, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da naɗin Dakta Bashir Muhammad Ɗankadai, a matsayin shugaban hukumar, ya yin kuma da ya amince da naɗin Dakta Halima Muhammad Mijinyawa, a matsayin sakatariyar hukumar ta (Kano State Contributory Healthcare Management Agency).
Sauran membobin hukumar sun haɗa da:
(1). Halima Musa Yakasai, wakiliya daga ma'aikatar lafiya ta Jihar Kano, wato (State Ministry Of Health).
(2). Musa Namadi Karefa (Daraktan albashi), wakili daga ofishin shugaban ma'aikata na Jiha, (Head Of Service).
(3). Tayyib Na'abba, (Daraktan kasafin kuɗi), wakili daga ma'aikatar tsare-tsare da kasafin kuɗi ta jihar Kano, wato (State Ministry Of Budget And Planning).
(4). Hafsat Kolo, wakiliya daga ƙungiyoyi masu zaman kansu, wato "Civil Society Organisations" (CSOs).
(5). Muhammad Isyaku Yammedi, wakili daga hukumar inshorar lafiya ta ƙasa, "National Health Insurance Scheme" (NHIS).
(6). Dakta Maryam Muhammad Suleiman wakiliya daga ƙungiyar likitoci ta ƙasa, (NMA).
(7). Hadiza Salisu Rogo da kuma Yakubu Abdullahi Esq, su ne wakilai daga ƙungiyar majalissar ƙolin haɗakar ƙungiyoyin ma'aikata na tarayya.
(8). Sai kuma sauran membobin hukumar waɗanda su ka wakilci ƙungiyar ƴan ƙwadago ta ƙasa, (NLC) da waɗanda su ka wakilci haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƴan kasuwa ta ƙasa, (TUC).
Sannan kuma, akwai sauran membobin hukumar waɗanda ba a faɗa ba a yanzu, su ma nan gaba za a gabatar da sunayensu da kuma ma'aikata ko hukumomin da su ka fito.
A ya yin da ya ke taya su murna, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya buƙaci duk waɗanda ya ba wa wannan muƙamai da su kiyaye da muradin da aka gina wannan hukuma akai na kawo gyara da samar da ingantaccen cigaba a fannin lafiya.
"Ina amfani da wannan dama wajen jan hankalinku da tunasar da ku cewa wannan tsari ya na da matuƙar tasiri ga Jiharmu, an kafa wannan hukuma ne kan doka da manufar yi wa al'umma aiki da tallafa musu, sannan duk waɗanda mu ka ba wa waɗannan muƙamai mun yi duba da tarihin ayyukansu na baya, mu na sa ran za su yi aiki cikin nagarta da amince tare da la'akari da sauye-sauyen zamani kamar yadda Duniya ta ke tafe a yau". Inji Gwamna Ganduje.