DCL Hausa

DCL Hausa DCL Hausa na yaki da labaran bogi ta hanyar kawo muku hirarraki da labarai sahihai
(16)

Wa kuke ganin ya fi cancanta ya tsayawa ADC takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2027?
24/05/2026

Wa kuke ganin ya fi cancanta ya tsayawa ADC takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2027?

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta musanta faifan bidiyon da ke cewa ana zanga-zanga a fadarFadar Mai Alfarma Sarkin Mu...
24/05/2026

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta musanta faifan bidiyon da ke cewa ana zanga-zanga a fadar

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta karyata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna cewa al'umma sun gudanar da zanga-zanga kan yunwa a fadar.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, fadar ta ce an dauki bidiyon ne tun a shekarar 2024, a lokacin da aka samu hauhawar farashin kayan abinci a Nijeriya.

Ta kuma yi zargin cewa an dawo da shi ne don cimma wata manufa mara kyau.

Ana daf da kawo karshen rikicin Amurka da Iran - Donald TrumpShugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ana daf da cim...
24/05/2026

Ana daf da kawo karshen rikicin Amurka da Iran - Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ana daf da cimma yarjejeniyar kawo karshen rikicin da ke tsakanin kasar da kuma Iran.

Haka kuma ya ce yarjejeniyar za ta kunshi bude mashigin 'Hormuz' don al'amura su ci gaba da gudana yadda ya kamata, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Yaya za ku kwatanta tsadar cefane a yankunanku, yayin da ake shirin yin Babbar Sallah?
24/05/2026

Yaya za ku kwatanta tsadar cefane a yankunanku, yayin da ake shirin yin Babbar Sallah?

Mataimakin gwamnan na Kano ya bayyana haka ne yana mai yabawa da yadda aka gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali da...
24/05/2026

Mataimakin gwamnan na Kano ya bayyana haka ne yana mai yabawa da yadda aka gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali da lumana.

Wasu bayanai da jaridar Punch ta tattaro, sun yi nuni da cewa Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya rasa goyon bayan...
24/05/2026

Wasu bayanai da jaridar Punch ta tattaro, sun yi nuni da cewa Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya rasa goyon bayan shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da kuma shugabannin jam’iyyar APC, sakamakon rashin sa albarkar ministan Abuja Nyesom Wike.

Karin bayani: https://l1nq.com/5ssqzop

Ƴan sanda sun yi ram da wani gungun masu garkuwa da mutane, sun ƙwato Naira miliyan 7.5 kuɗin fansa a KatsinaJami’an run...
24/05/2026

Ƴan sanda sun yi ram da wani gungun masu garkuwa da mutane, sun ƙwato Naira miliyan 7.5 kuɗin fansa a Katsina

Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Katsina sun cafke mutum bakwai da ake zargi da sace wani yaro mai shekara takwas a cikin birnin Katsina.

Karin bayani: https://l1nq.com/073vzmq

Abubakar Malami SAN da ya samu tikitin takarar Gwamnan jihar Kebbi a jam'iyyar ADC tare da mutane uku da s**a samu tikit...
24/05/2026

Abubakar Malami SAN da ya samu tikitin takarar Gwamnan jihar Kebbi a jam'iyyar ADC tare da mutane uku da s**a samu tikitin takarar sanatoci a jihar Kebbi;

Janar Aminu Bande mai ritaya,
Kebbi ta tsakiya

Ibrahim Muhammad Mera
Kebbi ta Arewa

Danjuma Limi
Kebbi ta Kudu

Yaya kuke kallon fafatawar siyasar 2027 a jihar Kebbi?

24/05/2026

Shugaba Tinubu ya ce ya gamsu da yadda gwamnoni ke aiki tuƙuru don sake lashe zaɓen sa karo na biyu

An fara sauya fentin makarantar da dan gwagwarmaya Dan Bello ya gyara a Kano bayan cece-kucen da wasu s**a fara yi kan k...
24/05/2026

An fara sauya fentin makarantar da dan gwagwarmaya Dan Bello ya gyara a Kano bayan cece-kucen da wasu s**a fara yi kan kalar fentin

Ina alhazan 2026 daga Nijeriya?Hukumar NAHCON ta bude cibiyar karɓar kiran gaggawa, idan kuna bukatar wani taimako ko ku...
24/05/2026

Ina alhazan 2026 daga Nijeriya?

Hukumar NAHCON ta bude cibiyar karɓar kiran gaggawa, idan kuna bukatar wani taimako ko kuna da wani muhimmin batu a cikin awanni 24 a Makkah.

Mahukuntan NAHCON sun bayyana cewa cibiyar za ta rika karɓar korafe-korafe da bayar da tallafi kan harkokin Hajji da Umrah domin tabbatar da jin daɗi da sauƙaƙa wa maniyyata gudanar da ibadunsu. Ga lambobin

📞 +966 56 546 0059
📞 +966 56 860 8760

Address

Arewacin Najeriya
Kaduna
800264

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DCL Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DCL Hausa:

Share