PCM Hausa

PCM Hausa PCM Hausa tashar yada labarai ce mai zaman kanta, muna gabatar da sahihan labarai, shirye shirye da podcast cikin harshen Hausa.
(7)

Wannan official page ne na PCM Hausa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta ce ta kwato motoci biyu da kuma shanu sittin da bakwai bayan wasu samame da jami’anta...
21/05/2026

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta ce ta kwato motoci biyu da kuma shanu sittin da bakwai bayan wasu samame da jami’anta s**a gudanar a sassa daban daban na jihar.

Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa jami’an ’yan sanda sun k**a wasu mutane hudu da ake zargi da damfarar masu sayen motoci bayan sun tare wata mota a hanyar Kaduna. Ya ce yayin samamen an gano wata mota daban, da na’urar POS, tare da katin shaidar aikin ɗan sanda na bogi.

Sanarwar ta kuma ce jami’an tsaro na hadin gwiwa sun kwato shanu arba’in da uku da raguna ashirin da hudu bayan sun yi artabu da masu satar shanu a yankin Mangoro zuwa Idu da ke karamar hukumar Munya. Rundunar ta ce maharan sun tsere sun bar dabbobin, yayin da ake ci gaba da bincike domin cafke sauran wadanda ake zargi da hannu a ayyukan laifukan.

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin yi wa fursunoni rajistar inshorar lafiya kyauta tare da kai musu agajin lafiya a...
21/05/2026

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin yi wa fursunoni rajistar inshorar lafiya kyauta tare da kai musu agajin lafiya a gidajen gyaran hali da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ake sa ran sama da fursunoni dubu ɗaya da ɗari biyar za su amfana da shirin. An fara shirin ne a gidan gyaran hali na Kuje, kuma daga baya za a faɗaɗa shi zuwa gidajen gyaran hali na Gwagwalada da Suleja.

Mai kula da harkokin lafiya da muhalli na Babban Birnin Tarayya, Dakta Adedolapo Fasawe, ta ce an ƙaddamar da shirin ne bisa umarnin Ministan Abuja, Nyesom Wike, domin tabbatar da cewa kowa ya samu damar kula da lafiyarsa ba tare da la’akari da matsayinsa ba. Ta ce fursunonin da aka yi wa rajista za su riƙa samun duba lafiya, gwaje gwaje, tiyata, magunguna da sauran kulawar lafiya kyauta. Haka kuma an gudanar da rajistar lambar ɗan ƙasa ta NIN domin sauƙaƙa shigar da bayanansu cikin tsarin inshorar lafiyar.

Dakta Adedolapo Fasawe ta kuma tabbatar da cewa cibiyar lafiyar gidan gyaran halin za ta riƙa samun wadatattun magunguna da kayan aikin lafiya a kai a kai. A yayin shirin an yi wa fursunoni gwajin hawan jini da ciwon s**ari da zazzaɓin cizon sauro tare da duba lafiyar idanu, inda aka bai wa wasu tabarau da magunguna. Mataimakin Kwanturola na gidan gyaran hali na Kuje, Rasheed Ogundare, ya yabawa gwamnatin bisa wannan shiri, yana mai cewa shi ne karo na farko da aka gudanar da irin wannan cikakken shirin lafiya ga fursunoni a cibiyar.

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da janye dakatarwar da ta sanya a wasu kasuwannin shanu da ke faɗin jihar, domin bai wa ...
21/05/2026

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da janye dakatarwar da ta sanya a wasu kasuwannin shanu da ke faɗin jihar, domin bai wa jama’a damar gudanar da harkokin cinikin Babbar Sallah mai zuwa.

A baya dai gwamnatin jihar ta dakatar da harkokin kasuwanci a wasu kasuwannin shanu da ke ƙananan hukumomin Alkaleri da Bauchi da Kirfi da Tafawa Balewa a ranar 9 ga watan Afrilu saboda matsalolin tsaro. Sai dai a cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Gwamna Bala Mohammed Shawara Kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa gwamnan ya amince da buɗe kasuwannin nan take.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne saboda muhimmancin kasuwannin wajen cinikin dabbobi da kuma bai wa jama’a damar samun dabbobin layya kafin Babbar Sallah. Mukhtar Gidado ya ƙara da cewa za a bar kasuwannin a buɗe na tsawon makonni biyu, yayin da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da hukumomin yankuna za su ci gaba da sanya ido domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarabawar shiga many...
21/05/2026

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta JAMB, domin maye gurbin Farfesa Ishaq Oloyede wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 31 ga watan Yulin 2026.

Sanarwar naɗin ta fito ne ta hannun Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, inda ya bayyana cewa Farfesa Segun Aina ƙwararre ne a fannin Injiniyan Kwamfuta a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife. Sanarwar ta ce Aina na da gogewa a harkokin tsarin jarabawa na zamani da fasahar sadarwa da kuma gyaran cibiyoyin gwamnati.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa Farfesa Segun Aina, wanda zai cika shekara 40 a watan Yuli, yana daga cikin matasan farfesoshi a Najeriya a fannin Injiniyan Kwamfuta, kuma zai kasance mafi ƙarancin shekaru da ya taba zama shugaban JAMB. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa sabon shugaban zai ci gaba da inganta nasarorin da Farfesa Ishaq Oloyede ya samu a lokacin jagorancinsa.

‎Daga karamar Hukumar Kibiya yayin gabatar da taron tabbatar da Dan takarar Majalisar jiha (Affirmation) na wannan karam...
21/05/2026

‎Daga karamar Hukumar Kibiya yayin gabatar da taron tabbatar da Dan takarar Majalisar jiha (Affirmation) na wannan karamar Hukuma, inda aka zabi Hon. Garba Fammar a matsayin wanda zai tsayawa wannan takara a zaben 2027, bayan da yan takara da s**a shiga zaben s**a janye masa ciki ln su harda Hon. Mai Fada Bello Kibiya, Hon. Yusuf Shehu Kibiya, Hon. Auwal Isa Durba, Hon. Umar Sale Kibiya.

‎A yayin gabatar da taron yasamu halartar jagorori da wakilan jam’iyyar APC dana Hukumar Zabe ta Kasa INEC da jami’an Tsaro.

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da ake shirin gu...
21/05/2026

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da ake shirin gudanarwa a ranar Alhamis 21 ga watan Mayu. Fubara ya ce ya dauki matakin ne bayan dogon nazari da tuntuba da iyalansa da abokansa da kuma masu goyon bayansa.

Siminalayi Fubara ya bayyana cewa zaman lafiya da hadin kan jihar Rivers sun fi muhimmanci fiye da bukatar kashin kai ta siyasa. Ya ce ya yanke shawarar ne domin bai wa jihar damar ci gaba cikin kwanciyar hankali da hadin kai, yana mai jaddada cewa zai mara wa duk wanda ya lashe tikitin jam’iyyar APC baya a zaben gwamnoni mai zuwa.

Gwamnan ya gode wa shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC bisa goyon bayan da s**a ba shi a wannan tafiya ta siyasa. Haka kuma ya bukaci magoya bayansa da su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga jam’iyyar APC tare da tabbatar da hadin kai, yana mai cewa janyewarsa daga takarar ba alamar tsoro ko gazawa ba ce, illa sadaukarwa domin zaman lafiyar jihar Rivers.

Wata kotun majistare da ke Bwari a Abuja ta bayar da umarnin kamo ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Kum...
20/05/2026

Wata kotun majistare da ke Bwari a Abuja ta bayar da umarnin kamo ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano, Hon. Idris Dankawu, bisa zargin damfara da ya shafi sama da naira miliyan 77.

Rahotanni sun nuna cewa kotun ta bayar da sammacin kamen ne bayan wani ƙorafi da kamfanin BAMZ Multi Essential Services ya shigar ta hannun lauyansa Barrista Ahmad Umar Faroukh, inda aka ce Hon. Idris Dankawu bai bayyana a gaban kotu ba. A cikin ƙorafin da Barrista Ali Jamilu ya gabatar, ya bayyana cewa ana zargin an karɓi kuɗin ne ta hannun hadimin ɗan majalisar, Isma’il Yakubu Abubakar, domin wata kwangilar girka fitilun hasken rana da ake zargin ba a aiwatar ba.

Korafin ya ce Hon. Idris Dankawu ya shaida wa kamfanin cewa ya samu kwangilar mazaba ta sanya fitilun hasken rana kan tituna da kudinta ya kai naira miliyan 770, inda aka buƙaci a biya kaso 10 cikin 100 kafin a bayar da takardar kwangilar. Sai dai bayan watanni da dama ana zargin ba a bayar da kwangilar ko wata hujjar kashe kudin ba, yayin da ƙoƙarin jin ta bakin Hon. Dankawu da hadiminsa ya ci tura saboda wayoyinsu ba sa shiga.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta ce ta bankado tare da rusa wata ƙungiya mai haɗin gwiwa ts...
20/05/2026

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta ce ta bankado tare da rusa wata ƙungiya mai haɗin gwiwa tsakanin ‘yan Najeriya da ‘yan ƙasar Mexico da ke kera miyagun ƙwayoyi, inda ta k**a mutane 10 tare da kwace sinadarai da kayan aiki da darajarsu ta kai sama da naira biliyan 480.

Shugaban hukumar, Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Abuja, k**ar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito. Ya ce an gano wata babbar cibiyar sarrafa methamphetamine a cikin daji da ke Abidagba a ƙaramar hukumar Ijebu East ta jihar Ogun, bayan bincike na watanni.

A cewar Hukumar, an k**a mutane bakwai a wurin, ciki har da ‘yan ƙasar Mexico uku da ‘yan Najeriya huɗu da s**a haɗa da Martinez Felix Nemecto, Jesus López Valles, Torrero Juan Carlos, Nwankwo Sunday Christian, Igwe Abuchi Remijus, Ifeanyichukwu Chibuike Joshua da Egwuonwu Uchenna Victor. Haka kuma an k**a shugaban ƙungiyar Anochili Innocent a Lakowe Golf Estate da ke jihar Lagos, yayin da hukumar ke ci gaba da bincike kan lamarin.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya su koma tsarin gudanar da aiki...
20/05/2026

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya su koma tsarin gudanar da aiki na zamani mara amfani da takardu domin inganta sauri da gaskiya wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, yayin buɗe taron International Civil Service Conference 2026 da aka gudanar a Abuja. Ya ce lokaci ya yi da za a daina tafiyar hawainiya ta tsarin hannu tare da rungumar tsarin zamani mai amfani da fasahar zamani da bayanai wajen gudanar da ayyuka domin biyan bukatun al’umma yadda ya k**ata.

Shugaban ƙasar ya ce ma’aikatu da hukumomi 38 sun riga sun fara amfani da tsarin aiki na zamani mara takardu gaba ɗaya. Haka kuma ya yaba wa Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Mrs Didi Esther Walson Jack, bisa jagorancin sauye sauyen da ake yi, tare da jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da amfani da fasahar zamani da inganta ƙwarewar ma’aikata domin bunƙasa ayyukan gwamnati da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi zargin cewa tsohon gwamnan Kano kuma jagoran K...
20/05/2026

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi zargin cewa tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, na aiki ne a fakaice domin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Sunusi Bature ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARISE News, inda ya ce haɗakar siyasar da ake hasashen za ta kasance tsakanin Kwankwaso da Peter Obi ba za ta daɗe ba kuma ba za ta yi tasiri sosai ba. Ya ce jam’iyyar NNPP ba ta da ƙarfin da za ta iya shiga zaɓen 2027 ita kaɗai ba tare da haɗaka da wasu jam’iyyu ba.

A cewarsa, an gudanar da shawarwari tsakanin manyan masu ruwa da tsaki ciki har da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso domin nemo mafita mai ɗorewa. Haka kuma ya ce sun tattauna da jam’iyyar APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin zaɓi na farko na yiwuwar komawa APC, yana mai cewa Kwankwaso ya nuna sha’awar ganawa da Tinubu kan batun siyasa kafin daga bisani ya soke ganawar saboda tafiyarsa zuwa ƙasar China.

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da fara hutun Babbar Sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamna...
20/05/2026

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da fara hutun Babbar Sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar Kano. Daraktan wayar da kai na ma’aikatar, Malam Misbahu Yakasai ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta ce daliban makarantun kwana za su fara hutu daga ranar Asabar 23 ga watan Mayun shekarar 2026, sannan su koma makaranta ranar Lahadi 31 ga watan Mayu. Haka kuma an bayyana cewa daliban makarantun jeka ka dawo za su tafi hutun Sallah daga ranar Juma’a 22 ga watan Mayu, tare da komawa makaranta ranar Litinin 1 ga watan Yunin shekarar 2026.

Ma’aikatar ta bukaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar sun karbi ’ya’yansu a ranakun da aka tsara tare da mayar da su makaranta a lokacin komawa karatu. A nasa bangaren, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano Dakta Ali Makoda ya taya dalibai da malamai da iyaye murnar Babbar Sallah tare da yi musu fatan gudanar da bukukuwan cikin zaman lafiya da annashuwa.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when PCM Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to PCM Hausa:

Share