21/05/2026
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta ce ta kwato motoci biyu da kuma shanu sittin da bakwai bayan wasu samame da jami’anta s**a gudanar a sassa daban daban na jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa jami’an ’yan sanda sun k**a wasu mutane hudu da ake zargi da damfarar masu sayen motoci bayan sun tare wata mota a hanyar Kaduna. Ya ce yayin samamen an gano wata mota daban, da na’urar POS, tare da katin shaidar aikin ɗan sanda na bogi.
Sanarwar ta kuma ce jami’an tsaro na hadin gwiwa sun kwato shanu arba’in da uku da raguna ashirin da hudu bayan sun yi artabu da masu satar shanu a yankin Mangoro zuwa Idu da ke karamar hukumar Munya. Rundunar ta ce maharan sun tsere sun bar dabbobin, yayin da ake ci gaba da bincike domin cafke sauran wadanda ake zargi da hannu a ayyukan laifukan.