27/05/2026
Wato wannan mutumin fa farfesa ne a siyasa. Sai ya yi kamar ya mutu a siyasa sai ka ga ya sake buga wani mugun wasan ya wargaza wa abokan hamayyarsa lissafi.
Kuma duk ƙiyayyarka da shi, ba za ka iya kore gaskiyar cewa a Arewacin Najeriya shi ne ɗan siyasar da ya fi kowa jawo ƴaƴan talakawa musamman matasa a jiki ba. Indai maganar matasa kake yi, sai dai ka ƙi mutumin nan don son zuciya.
Yanzu dai ku duba ƴan takararsa da yake fitarwa a jihar Kano, kusan kaso 70 ɗinsu duk matasa ne, wasu ma ba ƴaƴan kowa ba.
Anya za a iya kai wannan mutumin ƙasa kuwa?.
Tsini maganin Tsinannu