Bakoji TV

Bakoji TV the sole aims of this page is to bring about news and current affairs, entertain, enlightens, and motivate people and the society in general

20/07/2022

That hurricane! ( thy love ) do away whole particles and blur every bliss stars
My ears yearn your dulcet words
That get rid of every affliction
You bloated my tube with your love
It is now programming my marrow and nerves

Wannan allura ce, da matasa suke wa kansu. Wani nau'i kenan na shaye-shaye da yake dada ta'azzara a tsakanin matasa. Bay...
16/07/2022

Wannan allura ce, da matasa suke wa kansu. Wani nau'i kenan na shaye-shaye da yake dada ta'azzara a tsakanin matasa. Bayan wannan akwai Akuskura.

Ahmad Yusuf

Ya siyo iPhone 12 Pro Max ba ya so mahaifansa su gane cewa ya siya waya mai yawan kuɗi.Baba: Mu ga wayar nan da ka siyo....
16/07/2022

Ya siyo iPhone 12 Pro Max ba ya so mahaifansa su gane cewa ya siya waya mai yawan kuɗi.

Baba: Mu ga wayar nan da ka siyo.

Ɗa: To Baba ga ta.

Baba: Wannan wace irin waya ce mai kyau haka?

Ɗa: Wata sabuwar yayi ce da aka yo.

Baba: Infinix ce, ko Tecno ko Itel ko Vivo?

Ɗa: Vivo ce V40.

Baba: Gaskiya ta yi kyau sosai. Nawa ka siyo ta?

Ɗa: Dubu hamsin da biyar.

Baba: Ga dubu ɗari da sha biyar nan zan tura maka a account ka siyo guda biyu kai ɗaya, mamanku ɗaya. Ni na riƙe wannan.

Ku ba yaro shawara ya rasa yadda zai yi ya maido Vivo ɗinsa V40 😊

✍️ Ibrahim Bello (Irosis)

16/07/2022

Gayu mutanenmu

TARIHIN SHIEKH SHEIKH MAHER AL-MUEAQLY . ماهر بن حمد بن محمد بن المعيقلي البلويAmsar Tambayar Ameer Bajoga .Sheikh Maher...
09/07/2022

TARIHIN SHIEKH SHEIKH MAHER AL-MUEAQLY . ماهر بن حمد بن محمد بن المعيقلي البلوي

Amsar Tambayar Ameer Bajoga .

Sheikh Maher Al-Mueaqly Shahararren Qari ne (Mahaddin Al-Qur'ani) kuma limamin Masallacin Harami na Makkah. Ya bar aikin malamin lissafi ya zama malami a garin Makkah, kuma a yanzu ya zama mashahurin mai wa'azi kuma malamin addinin musulunci.

Farkon Rayuwa da Ilimi

An haife shi a Madina a Ranar 7 Ga Watan Janairu A shekara ta 1969, Al-Mueaqly Cikakken Sunansa ( Maheer Bin Hamad Bin Muhammad Bin Al-mu'aiqly Al-Balawi ) Ya samu digirin digirgir a fannin lissafi sannan ya shiga ma'aikatan makarantar Balat Al Shuhada sannan ya zama mashawarcin dalibi a makarantar Abd Al-Majid da ke Makkah. A shekarar 2004 ya sami digiri na biyu a fannin fikihu (Fiqh) a jami'ar Umm Al-Qura da ke Makkah, sannan ya samu digiri na uku a jami'ar a shekarar 2012.

Sana'a

Sheikh Al-Mueaqly ya fara gabatar da salloli daban-daban a Makkah da Madina. Karatun nasa bai dade Ba ya daukar hankali ba, inda jama'a s**a cika masallacin domin yin addu'a a bayansa da sauraren Karatunsa.

Daga karshe ya bar aikinsa na mai ba da shawara ya fara koyarwa a jami'ar Sarki Abdullah. An nada shi jagorancin Taraweeh a Masjid Al Nabawi a shekarun 2005 da 2006 sannan kuma a shekara ta 2007 aka nada shi jagorancin Taraweeh a Masjid Al Haram na Makkah, ba da dadewa ba bayan Ramadan aka nada shi Imami na dindindin.

Sheikh Al-Mueaqly ya kasance yana jagorantar Taraweeh tare da Sheikh Abdul-Rahman Al-Sudais sannan daga baya a shekara ta 2008 ya fara aiki tare da Sheikh Abdullah Awad Al Juhany har zuwa 2014.

An nada shi Khateeb na Masjid Al Haram ne a cikin watan Ramadan a shekarar 2016 bayan da Sarki Salman ya ba da sanarwar. Ya gabatar da Khutbah na farko a Masallacin Harami a ranar 15 ga Yuli 2016.

KARI 👇

Ya yi karatu a Kwalejin Malamai da ke Madina, inda ya kammala karatunsa a matsayin malamin lissafi, sannan ya koma Makkah Al-Mukarrama a matsayin malami, sannan ya zama jagoran dalibai a makarantar Yarima Abdulmajeed da ke Makkah. Ya yi digirinsa na biyu a shekarar 1425 bayan hijira a fannin ilimin fikihu Imam Ahmad bin Hanbal a Kwalejin Shari’a ta Jami’ar Umm Al-Qura, sannan ya samu digirin digirgir a fannin tafsiri. Yana aiki a matsayin mataimakin farfesa a sashin nazarin shari'a a kwalejin nazarin shari'a da ka'idojin shari'a na jami'ar Umm Al-Qura. kuma yana riƙe da matsayin Mataimakin Dean don Nazarin Digiri da Binciken Kimiyya.

Ya sami digiri na biyu a Jami'ar Umm Al-Qura, Kwalejin Shari'a, Sashen Shari'a ( Fiqhu ) a shekara ta 1425 bayan hijira. Littafin ya kasance mai suna: Imam Ahmad Ibn Hanbal Mas'alolin Fikihu kamar yadda hadisin Abd al-Malik al-Maimouni (tare da nazari). Ya sami digirinsa na uku a jami'ar Umm Al-Qura a shekara ta 1432 bayan hijira, wanda shine binciken littafin (Tuhfat Al-Nabih, Sharh Al-Tanbih) (na Imam Shirazi a fikihu Shafi'iyya).

Har ila yau, ya sami takardar shaidar digirin digirgir Mai Taken ( “The Prophet’s Masterpiece in Explanation of the Warning to Al-Zanklouni Al-Shafi’i, a Study and research of the Chapter on Borders and the Judiciary.”) An tattauna wannan bita a dakin taro na Sarki Abdul Aziz. Ya samu digirin digirgir a fannin shari'a a ranar 28 ga Muharram, 1434 na Hijira daidai da 11/12/2012 Miladiyya.

Ya jagoranci wa'azi A Masallacin Al-Saadi da ke gundumar Al-Awali a cikin Makkah Al-Mukarramah. Ya karbi jagorancin Sallah a Masallacin Annabi (SallalahuAlaihiWasallama) a cikin watan Ramadan na shekara ta 1426 bayan hijira da kuma 1427 bayan hijira. Kuma ya jagoranci Sallar Tarawihi da Tahajjud a Masallacin Harami na watan Ramadan na shekara ta 1428 bayan hijira, kuma An nada shi Limamin Masallacin Harami a wannan shekarar har zuwa yau.
Saliadeen Muhammad Sicey.

MUDI DA MATARSAMudi ya ce wa matarsa, "idan mun sami ruwa gobe, zan tafi gona aiki, idan kuma ba a yi ruwa ba, zan yi gy...
08/07/2022

MUDI DA MATARSA

Mudi ya ce wa matarsa, "idan mun sami ruwa gobe, zan tafi gona aiki, idan kuma ba a yi ruwa ba, zan yi gyaran kwatamin can na ƙofar gida, da yake damun mu da ɗoyi.'"

Matar ta ce, "Maigida, ba ka ce insha Allahu ba."

Sai kuwa ya hau ta da faɗa, "To Sayyada! Ko na ce insha Allahu ko ban ce ba, dole cikin biyun nan gobe a yi ɗaya. Ko dai na tafi gona ko na yi aiki a ƙofar gida."

Allah da ikonsa, sai gari ya tashi tangaram. Mudi ya saɓi magirbi ya nufi ƙofar gida wajen gyaran kwata. Yana kunno kai waje, sai kwalawa s**a yi ram da shi. Ashe su kuma sun biyo wani mai laifi ne, da ya zo daidai zauren gidan Mudi, sai ya yi kamar ciki ya afka, ashe arcewa ya yi ba su lura ba. Tun a cikin mota s**a fara ƙera shi.

Mudi ya sha gwale-gwale sosai a caji ofis, har sai da ya fita hayyacinsa. Daga ƙarshe 'yansanda s**a gane ba mutumin da suke nema ba ne. S**a ba shi haƙuri, s**a sallame shi. Da ya dawo gida, sai ya ƙwanƙwasa ƙofa. Matar ta ce, "waye?"

Ya ce, "Mudi ne, insha Allah!"

Bukar Mada
08/07/2022

06/07/2022
06/07/2022

HasbunaAllahu wa neemal wakeel!

~ A jiya kaɗai ƴan ta'adda sun kashe babban jami'in ɗan sanda a Dutsinma katsina.

~ Ƴan ta'adda sun kaima ayarin motocin shugaban kasa hari a katsina.

~ Ƴan ta'adda sun kai hari a gidan gyaran hali dake kuje Abuja, Sun ɓalle kofofin gidan manyan masu laifi sun tsere, amma su Abba kyari, faruku lawan, jolly inyami da waɗansu basu tsere ba.

~ Sannan fa har yanzu wasu ƙauyukan basu isa su zauna lafiya ba ko suyi noma ba tare da biyan haraji ga ƴan ta'adda ba.

Anya ƙasar nan ba juyin mulki za'a yi ba saboda notin kan sitiyarin zaman lafiya ya kwance.

Allah ka tabbatar mana al'amari mafi Alkhairi ka kuma bamu shugabanni na gari.

Duk promo da scholarship din da Dangote cement suke yi a lagos suke launching kuma a can beneficiaries din s**a fi yawa,...
06/07/2022

Duk promo da scholarship din da Dangote cement suke yi a lagos suke launching kuma a can beneficiaries din s**a fi yawa, , amma duk wanda ya san lagos ya san basa Amfani da simintin Dangote da LAFARGE suke Amfani na Sagamu ko Abeokuta. haka sauran kamfanoni suke Arewa ce bolar su, anan kasuwar su take a nan s**a fi cin riba. amma ba ta amfana da tsare tsaren tallafin ta
Arewa su kaskantar da kanta an Raina ta

NB
muna sane da Gine ginen da yayi cikin Jami'o a can ma yayi irinsu
Aminu soja

Nace wai kishi ne yasa naga mata da yawa suna tsaki da ganin wannan hoton? Naga wasu har cewa suke Hmmm yarinya kenan, w...
06/07/2022

Nace wai kishi ne yasa naga mata da yawa suna tsaki da ganin wannan hoton? Naga wasu har cewa suke Hmmm yarinya kenan, wasu wuce yarinya bikisan maza bane. Har yanzu banga wadda tace masha allahu Allah ya sanya Alkhairi ba, wasu kuma cewa suke yarinya ki gama rawar kanki, wasu kuma sun buge da wa'azi,

ko Meyasa hakan?

Musa rafin kuka

06/07/2022

Za a ba wa kamfanonin layukan sadarwa a Najeriya wa'adin kwana 30 don shawo kan matsalolin kwastomoninsu.
BBC Hausa

Address

Kasuwar Murtala Brigade Gama, Nassarawa Local Government
Kano
700282

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bakoji TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Bakoji TV:

Share