DZ ABUL

DZ ABUL teaching

happy maulid
08/11/2025

happy maulid

yanzu makiyin annabi zaice na zagi malamm
30/09/2025

yanzu makiyin annabi zaice na zagi malamm

Allah ya karbi ziyarar mu
30/09/2025

Allah ya karbi ziyarar mu

farinciki ya bayyana a duniya        da bayyannar wannan masoyinaabin kewata acikin zuciya        shine metsareni daga s...
25/07/2025

farinciki ya bayyana a duniya
da bayyannar wannan masoyina

abin kewata acikin zuciya
shine metsareni daga sharrorina

maitaimakona adukkan nahiyya
wanda nake takama dashi ako ina

jikan rusulullihi mai shiriya
dan fadima da aliyu masoyana

yardar allahu ga mai tijjaniya
to akaran sonsa masoyina

πˆπ’π‡π€π‘π€ 𝐃𝐀 ππ€π’πˆπ‡π€π‘ π’π‡π„πˆπŠπ‡ πŒπ”π‡πŒπŒπ€πƒπ”π‹ πŒπ”π’π‡π‘πˆ π€π‹πŒπ”π‘π“π€ππˆ  𝐑𝐓𝐀 Siradul MustaΖ™im (hanya madaidaiciya) wanda aka faΙ—a cikin sura...
21/06/2025

πˆπ’π‡π€π‘π€ 𝐃𝐀 ππ€π’πˆπ‡π€π‘ π’π‡π„πˆπŠπ‡ πŒπ”π‡πŒπŒπ€πƒπ”π‹ πŒπ”π’π‡π‘πˆ π€π‹πŒπ”π‘π“π€ππˆ 𝐑𝐓𝐀

Siradul MustaΖ™im (hanya madaidaiciya) wanda aka faΙ—a cikin suratu Fatiha shine: Komawa zuwa ga Zatin Allah da komawa cikin Soyayyar Manzon Allah SAW, da kuma BAQA’I tare da zatin Allah Da Narkewa cikin Zatin Allah (batare da Hululi da Ittihaadi ba domin Allah ya tsarkaka ya sauka ko ya haΙ—u da jikin Abun Halitta) da Narkewa cikin Soyayyar Manzon Allah SAW, Da Neman Sanin Allah (Ma’arifah) ta hanyar Shi da Siffofinsa da Sunayensa. Da Tabbatuwa akan Bin Sunnar Manzon Allah SAW.

Duk wanda ya dawwama akan haka a duniya toh ya tabbatar zai Samu Istiqaama, wanda kuma bai dawwama akan Haka ba toh bazai samu ba, duk lokacin da istiqaamarka ta ragu a rayuwar duniya toh zaka haΙ—u da tawaya a gobe Ζ™iyama.

Ku komar da ZuΖ™atanku zuwa ga Allah, ku rayar da lokutanku da neman kusanci ga Allah da Ι—ebe kewa dashi da soyayyar Manzon Allah SAW, Ku Sani Rayuwar nan TaΖ™aitacciya ce Kuma Gashi abun nema acikinta suna da yawa.

Ku tashi kuyi Ζ™oΖ™ari a duniyar nan idan mutum Ya mutu ba zai samu damar furta LA ILAHA ILLALLAHU kafa Ι—aya tak ba. Duniya wajen Aiki (Ibaadah) ne babu Hisabi Lahira kuma wajen Hisabi ne Babu Aiki.

Allah Ya Tabbatar da duga-duganmu akan SiraΙ—il Mustqeem.

©️Aliyu Uthman Bashir


γ‚šviralγ‚·

TAFAKKURI      tabbas rijalu sun san cewa wannan  yakin da ake a isra'il dama sun san zaizo.    domin ba arokon allah ab...
19/06/2025

TAFAKKURI

tabbas rijalu sun san cewa wannan yakin da ake a isra'il dama sun san zaizo.
domin ba arokon allah abu yaki bayarwa,mutane sunyi addu'o'i akan zaluncin isra'il ga falastinu,suna masu rokon allah da ismul azim,suna jefawa a ramzi akan allah ya ruguzasu,
tabbas yauko gashi ismul'azim (makami mai linzami) sai sauka suke suna ruguza garin.
muna godema allah dawannan ni'ima da tasauka abirnin muslunci, tabbas wannan nasarace ga musulmin duniya.

makami mai linzami, akwai wani sirri acikinsa inkai taffakkuri sosai, domin wani (alifi) ne wani (hakuri)ne.
amma nabauwa masana asrarai suyi bayani akai, muna tuba

allah ya karamana son shugaba s a w da shehu tijjani rta da shehu ibrahim inyasss rta

WASIKAR SHEHU RTA ZUWA GA SARKI SUNUSI NA FARKO HALIFA SUNUSI R T A
10/06/2025

WASIKAR SHEHU RTA ZUWA GA SARKI SUNUSI NA FARKO HALIFA SUNUSI R T A

SHEIKH IBRAHIM NIASSE RTA YA LAMINCE MANA. A wannan wasiΖ™ar ta Ζ™asa Sheikhu RTA Yace:-β€œYan uwana, da MaΖ™wabtana, da Khad...
10/06/2025

SHEIKH IBRAHIM NIASSE RTA YA LAMINCE MANA.

A wannan wasiΖ™ar ta Ζ™asa Sheikhu RTA Yace:-

β€œYan uwana, da MaΖ™wabtana, da Khadimaina, Da Samarina, Bayan Sallamah ku sani Na LAMINCE MUKU cewa zaku huce dukkannin tsarekunku (Sa’anninku) cikin Ilimi da Ma’arifah da Darajah da wadata da ArziΖ™in duniya da lahira Amma da sharuΙ—Ι—a kamar haka: Barin wasa da Wargi da Rafkana daga Ibada kwata-kwata, Bin Sahun Bayin Allah na gari, Da Aiki da Iliminku gwargwadon iko, da soyayyah cikin Ι—ariΖ™a da Ahlinta, da kuma yanke abunda yake tsakaninku da maΖ™iyanku, ku tsaya tsayuwar daka cikin duk abunda na umurceku dashi. Idan kukayi haka Tubanku Zai zama KarΙ“aΙ“Ι“e kuma Aikinku zai zama Abin Godewa agurin Allah.

β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”Ibrahim Ɗan Alhaji Abdullahi Attijaniy a Birnin Kaulakh.

Allah Ya Bamu Ikon Bin Umurnin Sheikhu Ibrahim Niasse RTA. Juma’ah Mubarakah.
an shehina wa maulana ahli inyass sayyadi

©️Aliyu Uthman Bashir

BAYANI AKAN WUSULI DA KOFAR MA'ARIFA     WUSULI shine saduwa acikin wani abu a harshen hausa kenan.     wusuli a sufanci...
10/06/2025

BAYANI AKAN WUSULI DA KOFAR MA'ARIFA
WUSULI shine saduwa acikin wani abu a harshen hausa kenan.
wusuli a sufanci shine bawa yayi fana'i (yakare) acikin halarar allah, yazama baya ganin wanin allah sai allah, shine fadin hadisinnan (kanallahu wala shai'a ma'ahu) idan bawa yai haka ya shiga cikin wannan hali to shine akecewa yashiga cikin jazba (maye na fana'i).
yadda ko bawa zai shiga wanna hali shine idan shehinsa zai mai tarbiyya zai bashi zikirai Kamar haka:
salatil fatihi 500 sau uku
al'auwalu..........al'badinu 500 sau 5
mu'auwali. kafa 3 sau biyar
sai taffakkuri. da sauransu.
domin kowane shehi da yadda yake tarbiyyar muridansa.
to bayan yazo ammai imtihani za agane yayi wusuli kokuwa dai, ya danganci kyan ruhin murudin, idan yayi zai bayanin abinda yagani kamar na farko........ na karshe, wato fana'i(wusuli) shine kamar Tashar garin ma'arifa.
wanan shine ake kira da wusuli atakaice,

na daddatse wasu abubuwan sabida aikin sirrine.

KOFAR MA'ARIFA
shine idan murudi yayi wusuli yasamu fatahin farko na fana'i, sai abashi (sirrin fatiha) da (salatul fati )da (sirrin ziyara) da (sakirtu ) ya nemo sunaye guda dai-dai acikin kowannansu,wannan sunaye guda 4, sune kofa, kowace hadara akwai sunanta da zai dinga shaida aikinta a musha'hada dashi.
wannan shine kofar ma'rifa.
muna rokon allah ya karomana faida bijahi shehu barhama abdullahi inyass rta

INA MIKA SAKON BARKADA SALLAH GA SHEHINA SAYYADI ALIYU UTHUMAN BASHIR CISSEY R T A
10/06/2025

INA MIKA SAKON BARKADA SALLAH GA SHEHINA SAYYADI ALIYU UTHUMAN BASHIR CISSEY R T A

INA MIKA SAKON BARKADA SALLAH GA AHLI INYASS RTA
10/06/2025

INA MIKA SAKON BARKADA SALLAH GA AHLI INYASS RTA

Address

Unguwar Jakada Padama
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DZ ABUL posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DZ ABUL:

Share