21/01/2025
Wannan bayanin ya fito ne daga rahoton da aka fitar bayan tarurrukan masu ruwa da tsaki da kuma nazari da hukumar ta gudanar daga 11 ga Yuli zuwa 5 ga Agusta, 2023, don tantance yadda aka gudanar da zaben.
A tarurrukan, masu ruwa da tsaki da s**a halarta sun hada da shugabannin jam’iyyun siyasa, wakilan kungiyoyin al’umma, kwamishinonin zabe, jami’an tsaro, da wakilan kafofin watsa labarai.
Rahoton ya bayyana cewa:
“Matsalar ta faru ne yayin da jami’an zabe s**a fara loda hotunan sakamakon zaben shugaban kasa daga wuraren kada kuri’a (PU) bayan kammala kada kuri’a. Rahoton ya kara da cewa matsalar tana da alaka da wani kuskure na cikin tsarin fasaha wanda ya hana nasarar loda sakamakon zaben shugaban kasa, yayin da sauran sakamakon zaben majalisar dattijai da ta wakilai ba su fuskanci irin wannan matsalar ba.”
Rahoton ya bayyana cewa INEC ta gudanar da bincike mai zurfi, inda ta gano cewa matsalar tana da nasaba da tsarin da aka yi amfani da shi wajen tsara loda sakamakon zaben shugaban kasa wanda yake wakiltar yanki daya na kasa baki daya. Wannan ya sha bamban da tsarin loda sakamakon zaben majalisar dattijai da ta wakilai, wanda aka rarraba su bisa jihohi da yankuna.
An kuma bayyana cewa saboda mahimmancin tsarin da kuma yuwuwar harin ‘yan ta’adda ta yanar gizo, INEC ta dauki matakai masu tsauri na tsaro don kare tsarin daga kutse ko lalacewa.
Rahoton ya riga ya isa gaban kwamitocin majalisar dattijai da ta wakilai da ke kula da harkokin zabe domin ci gaba da nazari.
KBC Hausa