Dan Afirka

Dan Afirka Mulkin Mallaka • Ɗauloli • Mazan Jiya • Ɓoyayyun Tarihi • Jarumta • Arziƙi • Makircin Duniya • Tattalin Arziƙi • Tsaro ⚖️

[email protected]
(7)

Wato ba fa ƙaramar ƙullaliya aka ƙullo a cikin dokar hukumar zaɓe ta INEC ta sabunta bayanan katin zaɓen ƴan Najeriya ba...
04/04/2026

Wato ba fa ƙaramar ƙullaliya aka ƙullo a cikin dokar hukumar zaɓe ta INEC ta sabunta bayanan katin zaɓen ƴan Najeriya ba.

Lallai gwamnatin APC ta karaya, kuma tana shirya ƙullaliya domin hana zaɓe na gaskiya tafiya daidai.

Wasunmu suna ganin duk wani sha’anin siyasa bai dame su ba, amma fa siyasar ce yau ta kawo mu inda muke a Najeriya. Haka za mu ci gaba da zuba idanu?

Ina addu’ar watarana Allah Ya kawo shugaban ƙasar da zai raba ƙasar nan.Wannan wanne irin haɗin gambiza aka yi mana a ƙa...
01/04/2026

Ina addu’ar watarana Allah Ya kawo shugaban ƙasar da zai raba ƙasar nan.
Wannan wanne irin haɗin gambiza aka yi mana a ƙasar nan? Sam ba mu cancanci zama tare a matsayin ƙasa ɗaya ba! Yaushe za a daina faɗan ƙabilanci ana karkashe juna a Najeriya? 😥

Wallahi Turawa sun cuce mu. Sun raba ƴan’uwa zuwa ƙasashe da daban-daban, sun haɗe abokan hamayya a wuri ɗaya a matsayin ƙasa ɗaya. Ta yaya za a taɓa samun fahimtar juna kuwa?

30/03/2026

Lallai duk talakan da ya zaɓi Tinubu a wannan yanayi da muke ciki, to yana buƙatar a duba lafiyar ƙwaƙwalwarsa wallahi.

RIKICIN JOS:Sai fa mun tashi tsaye fa!Don da alama baƙin hauren da aka shigo mana da su cikin ƙasarmu daga Amurka sun fa...
30/03/2026

RIKICIN JOS:

Sai fa mun tashi tsaye fa!
Don da alama baƙin hauren da aka shigo mana da su cikin ƙasarmu daga Amurka sun fara gudanar da abin da ya kawo su.

Allah ya karya duk wani mai hannu a ta’addancin da ake yi a wannan ƙasa ta Najeriya.

Alhamdulillahi!Na shafe kusan watanni biyu zuwa uku kenan ina ɗaukar mabambantan darasuss**a akan ilimin “AI Filmmaking”...
29/03/2026

Alhamdulillahi!

Na shafe kusan watanni biyu zuwa uku kenan ina ɗaukar mabambantan darasuss**a akan ilimin “AI Filmmaking”, wato yanda ake haɗa cikakkun fina-finai na ƙirƙirriyar fasahar zamani ta AI.

Yanzu haka dai na kammala samun ilimi na matakin farko, kuma zan dakata haka domin ɗorawa daga inda aka tsaya a wannan shafi.

Zan ci gaba da kawo muku bidiyoyi irin na baya k**ar yanda aka saba. A gefe guda kuma muna ci gaba da shirye-shiryenmu na buɗe tashar gudanar da shirye-shiryenmu waɗanda za su haɗa har da fina-finan na ƙirƙirriyar fasahar.

Allah ya ci gaba da yi mana jagoranci. ✊

Amurka na shirin yaƙar Iran ta hanyar amfani da sojojin ƙasa! Yayin da Trump ke ta yayata maganar sulhu a duniya, a daid...
27/03/2026

Amurka na shirin yaƙar Iran ta hanyar amfani da sojojin ƙasa!

Yayin da Trump ke ta yayata maganar sulhu a duniya, a daidai lokacin kuma ake raɗe-raɗin ya tashi sojojin yaƙi kusan 2,500 zuwa 4,000 zuwa yankin Gabas Ta Tsakiya a yunƙurinsu na fafatawa kai tsaye tare da karɓe ikon ƙasar Iran bakiɗaya.

Me yake shirin faruwa da duniya?

Irin waɗannan abubuwan fa ba wai suna tsayawa kan iya waɗannan ƙasashe da suke yaƙi da juna ba ne, sak**akonsu na fantsama zuwa ko wanne yanki na duniya ne.

Amma shin Amurka za ta iya cin galaba a wannan yaƙi kuwa? Ta yaya za su iya yaƙar Iran ta ƙasa bayan sun gaza ta sama da ta ruwa? Kun san dubunnan shekarun da Iran ta ɗauka tana fafatawa da daulolin da ke son ƙwatar ta kuwa kuma har yanzu ba su samu nasara ba?

Lallai akwai sabon kallo a wannan duniya... ⚖️

21/03/2026

👏
Assalamu alaikum.
‎Ina miƙo saƙona na barka da sallah a makare, sak**akon ina ta fama da “mura”.
‎Allah Ya maimaita mana.

A jikina ina jin cewa Netanyahu ba ya duniya amma na yi duk iya bincikena domin samo tabbacin mutuwarsa sai dai haƙana y...
19/03/2026

A jikina ina jin cewa Netanyahu ba ya duniya amma na yi duk iya bincikena domin samo tabbacin mutuwarsa sai dai haƙana ya kasa cim ma ruwa.

Duk wata kafar bincike da ka tambaya sak**akon ba ya wuce abin da Turawan suke wallafawa. Akwai tarin tambayoyi bila-adadin da amsoshinsu ke alamta cewa tun 8 ga watan nan na Maris Iran ta kashe shi, amma mutanen nan sun toshe duk wata ƙofa da mutum zai samu gamsuwa da tabbaci.

Allah ya sa wannan mutumi yana barzahu a daidai wannan lokaci.

Masu salon magana suna cewa wai “siyasa sha’anin duniya ce; a duniya ake yin ta kuma a duniya ake barin ta”.Lallai duk w...
19/03/2026

Masu salon magana suna cewa wai “siyasa sha’anin duniya ce; a duniya ake yin ta kuma a duniya ake barin ta”.

Lallai duk wanda ya yi imani kuma ya yi aiki da wannan manufa to wataƙila ranar lahira wuta zai tafi. Ta yaya za ka karɓi kuɗi ko don ɗan siyasa ya biya maka wata buƙata ta ƙashin kai, kuma ka san bai cancanta ba, ka zaɓe shi ka tallata shi, ka ba shi gudunmawa ya ɗare kan kujera, kuma a ƙarƙashin jagorancinsa ayi ta zaluntar al’umma ana kashe su sannan ka ce wai a duniya za ka bar wannan tarin zunubi? Anya kana da tunani kuwa? Ai a lahira duk inda ya shiga to tare za ku tafi, saboda kai abokin cin mushensa ne.

Yanzu kenan shugaban da ya yi sata ko ya zalunci al’umma ƙarƙashin tsarin siyasa sai ace ya ci banza kenan, ba za a tambaye shi a lahira ba saboda siyasa a duniya ake yin ta? Lallai ɗaya bayan ɗaya kowa zai yi bayani gaban Mahalicci.

Yanzu talakan ƙasar nan ba ma ta batun ababen more rayuwa yake yi ba, magana fa kawai yake yi ta tsaro. Ace wai mutuwa cikin salamar ma ba za a bari talakan da ke fama da yunwa da rashin lafiya ya yi ba? Shi fa ba cewa ya yi sai ya yi rayuwa irin ta ƴaƴan masu mulki ba!

⚖️

Ƙasar nan ba za ta taɓa gyaruwa ba sai lokacin da talaka ya fara sanin kansa; ya daina son zuciya da sayar da kansa ga a...
19/03/2026

Ƙasar nan ba za ta taɓa gyaruwa ba sai lokacin da talaka ya fara sanin kansa; ya daina son zuciya da sayar da kansa ga azzalumai. Ya fara yaƙar zalunci ko da kuwa maƙiyinsa aka yiwa, sannan ya daina goyon bayan zalunci ko da kuwa nasa ne ya yi.

Ina mai tabbatar muku da cewa shugabannin Najeriya ba su shirya kawo ƙarshen matsalolin nan da suke faruwa ba. Tun daga jam’iyya mai mulki har abokan hamayyarta. Ku duba ku gani mana. Su waye ma suke adawa da gwamnatin yanzu? Duka sun yi shiru ba sa iya taɓuka komai. Tun da aka k**a El-Rufa’i ragowar s**a tsuke baki. Kowa yana jin tsoro kada ya zaƙalƙale wajen s**ar gwamnati a je a k**a shi, saboda ya san shi ma bai shuka abin kirki ba.

Yanzu labarin kashe-kashe a ƙasar nan ya zama k**ar na karin kumallon da muke yi a gida; ɗai-ɗai ranar da ba za ka ji an tashi wani gari ko an karkashe mutane ko an saka bam ba. Yanzu a Arewacin Najeriya kusan ɗai-ɗai jihar da ba ta fama da irin waɗannan ayyukan miyagun.

Kanon ma da ba a yin irin na sauran yankunan ita ma ga shi harkar daba da sara s**a ne s**a dabaibaye ta, ta ko ina. Amma tsawon wannan lokaci kun ga wani yunƙuri da duka mahukuntan suke yi domin kawo zaman lafiya mai ɗorewa? Kuma wallahi duk wanda ya ce maka matsalar tsaron Najeriya ta fi ƙarfin gwamnati to kariya kawai yake ba wa azzalumai.

Ba kuma iya laifin gwamnatin ba ne. Mu ma idan an k**a wani namu ba so muke a hukunta shi ba. Ko a nan Kano da yara ke harkar dabar ba ma so a hukunta su. Haka za ka ga iyaye na ta bibiyar ofisoshin ƴan siyasa domin a sakar musu ƴaƴa su ci gaba da ɓarna a doron ƙasa. Kowa ya zama azzalumi ba ya so a taɓa nasa saboda son zuciya.

A duk lokacin kuma da ka ja hankalin mutane ko na mahukunta akan a gyara sai a k**a jifan ka da mugayen kalamai — ace adawar siyasa kake yi wa gwamnati ko wasu ne s**a ɗauki nauyinka ko ƙabilanci ko wani abu mak**ancin haka. To kada a hukunta kowa, aci gaba da tafiya a haka ku gani idan watarana ƙasar za ta zaunu mana dukkanmu.

Sai dai addu’ar da irina ba za su taɓa dainawa ba ita ce: tun daga kan ƴan B*k* Haram zuwa masu garkuwa da mutane, masu tashin ƙauyuka da ƴan sara s**an da s**a addabi mutane, da masu ɗaukar nauyinsu, ɓarayin gwamnati da duk masu hannu a sanya talaka cikin mummunan yanayi a wannan ƙasa, duk wanda ba shi da niyyar tuba izuwa ga Allah, to muna roƙon Ubangiji ya tarwatsa shi, Allah ya lalata rayuwarsa k**ar yanda yake lalata ta wasu.

⚖️

Wallahi a yanzu dai, idan ka cire burin gamawa da duniya lafiya da nake yi, na rantse da Allah, ba ni da wani buri a dun...
18/03/2026

Wallahi a yanzu dai, idan ka cire burin gamawa da duniya lafiya da nake yi, na rantse da Allah, ba ni da wani buri a duniya da ya fi in ga Afirka da ƙasata Najeriya sun gyaru. Ina matuƙar son yankin nan wallahi.

Babu abin da yake ba ni takaici irin in ga duk wani yanki a duniya yana ci gaba amma ban da namu. Babu ilimi, babu lafiya, babu ruwa, babu wuta, babu hanyoyi, babu kimiyya da fasahohi, babu tsaro, babu ƴancin ɗan’adam, babu masana’antu — babu komai! Wai shin mu ba za mu rayu k**ar sauran sassan duniya ba? Wannan wacce irin nahiya ce da za mu yi ta rayuwa k**ar waɗanda babu ƙwaƙwale a cikin kawunansu?

Kullum muna cewa shugabanni da Turawa na zaluntar mu amma mafi yawa daga cikin al’ummarmu duk mun zama azzalumai. Kowa kansa yake so bai damu da wani ba. Kowa duniya yake nema ta kowanne hali bai damu da lahira ba. Kowa tsaro da kariyar kansa yake nema amma bai damu da halin da wasu suke ciki ba. Anya mu mutane ne ma kuwa? Yanzu a haka za mu ci gaba da rayuwa? A haka ƴaƴanmu za su zo su yi kyakkyawar rayuwa gobe? Wannan ita ce goben da muke gina musu?

Me ya sa ba za mu cire son zuciya mu fara samar da gyara daga kanmu ba? Me ya sa mu ma ba za mu zama masu adalci ga kawunanmu ba? A ce babu mai gaskiya da amfani sai wanda yake da alaƙa da kai, kuma babu mara gaskiya, mai cutarwa sai wanda ba shi da alaƙa da kai?

Gwamnati ba ta hukunta masu laifi sai waɗanda ba sa tare da ita, shi ma talaka ba ya son a faɗi laifin ɗan’uwansa sai dai na wani. Shi ya sa su ma shugabannin ba sa ma batun kawo gyara saboda dama daga cikinmu suke kuma irin halayenmu ne da su, kuma sun ga har yau ba mu shirya ba.

Imu-imu talakawa rayuwa muke yi kara zube; babu adalci, babu gaskiya, babu amana da alƙawari. Kowa ya samu dama sai ya zalunci ɗan’uwansa da uzurin cewa wai ai kowa ma idan ya samu dama wai haka zai yi. Anya wannan nahiyar tamu za ta gyaru kuwa? Yanzu da wannan tunanin muke tunanin samun canji? Waye zai fara gyarawa daga cikinmu kenan?

Wallahi ba fata nake yi ba, amma ko ɗana ne da na haifa yake aikata wani mummunan aiki sai na sallama shi ga hukuma ko in barranta da shi. Shi ya sa sam ba zan iya siyasa ba. Don wataƙila azzalumai ne za su kashe ni akan al’ummar da ba ta san yaƙin da kake yi mata ba.

Shi ya sa a wurin aikina ma ni ban sami faada ba, saboda ni ba na ganin rashin daidai ban yi magana ba.

Allah ya ganar da al’ummarmu!

⚖️

Ni ma ina da jiɓi da Fulani amma tabbas an zo gaɓar da dole sai na yi wannan rubutu. ⚖️Anya kuwa za a ci gaba da zuba id...
18/03/2026

Ni ma ina da jiɓi da Fulani amma tabbas an zo gaɓar da dole sai na yi wannan rubutu. ⚖️

Anya kuwa za a ci gaba da zuba idanu ana tafiya akan wannan tsarin kuwa?

Wallahi na daɗe ina kawar da kai akan wasu abubuwa da ke faruwa a Arewacin Najeriya da kuma al’ummar Hausawa, saboda addini ya hana mu nuna ƙabilanci kuma na san babu abin da ƙabilancin zai sake haifar mana sai wata mummunar ɓarnar da dukkanmu sai ta cinye mu domin ba za mu iya magance ta ba.

Amma magana ta gaskiya tun da na kalli bidiyon wannan matar da ke jikin hoton nan da aka ce wai mai ba wa gwamnan Kano shawara ce akan sha’anin Fulani, raina yake a matuƙar ɓace — na kasa daurewa. Saboda a kullum abin da yake ƙara fitowa fili ƙarara shi ne mahukuntan namu da kansu su ne matsalar ma da kanta.

1. Kun ce Hausawa da Fulani duk ɗaya ne bayan ko a ido waɗannan ƙabilu ba ma su yi k**a da juna ba, k**ar yadda ita ma wakiliyar gwamna ta yi nuni; ta ce su ne masu kyawun halittar da s**a fi dacewa su sanya babbar riga ba Hausawa ba.

2. Kun hana Hausawa su amsa sunan ƙabilarsu; kun ce ƙabilanci ne da son tayar da zaune tsaye amma ku kuna amsa naku sunan ƙabilar da alfahari.

3. Kun hana su kafa ƙungiya ta ƙabilarsu amma ku kuna da su daban-daban. Kun ce nasu za su kawo ta’addanci ne, amma ga shi naku ƙungiyoyin kullum kare maɓarnatan cikinku suke yi.

4. Kullum ba ku da aiki sai zagi da aibata ƙabila da asalin Hausawa, da kiransu marasa addini, bayan a tarihi ma da addininsu kuka zo kuka tarar da su — kai a matsayin al’umma ma sai da s**a karɓi addini da shekaru masu yawa sannan ku ma kuka karɓa. Wannan tarihin wanda bai sani ba ne yake ruɗuwa.

5. Hausawa sun ce kuna ware su a sha’anin gudanar da mulki a Arewa, kun ce a’a, amma ko ƙaramin yaro ba zai kasa fahimtar hakan ba muddin zai kalli ƙunshin shugabancin da muke da shi a yau a Arewa.

Ga shi yau har ta kai ma kuna samar da muƙamai musamman domin sha’anin Fulani amma babu na Hausawa. Babbar matsalar kuma a nan ba wai samar da muƙaman ba ne ba, sai dai irin manufar da masu muƙaman na Fulani zalla suke yaɗawa a tsakanin al’ummar Fulani da sunan wakilcin gwamnati. Ashe wannan manufar daga shugabannin take kenan? Domin har yau dai wannan mata na zaune akan kujerarta daram.

6. Ana ta kashe mu kuma kowa ya san daga inda matsalar nan take; su waye suke aikatawa, amma har yau babu wani babba a Arewacin Najeriya da ya yarda ya ma bayar da haɗinkai domin a yaƙi waɗannan ƴan ta’adda. Kai da ƙyar ma kuka bari aka ayyana sunansu a matsayin “ƴan ta‘adda” a gwamnatance, saboda kun ce ƴan’uwanku ne (Kamar yadda Mai Bayar da Shawara Kan Sha’anin Tsaro ya faɗa).

7. Yanzu wannan matar ace wai gwamnati ce ta samar da muƙaminta na mai bayar da shawara akan sha’anin Fulani, amma babu abin da take yaɗawa illa ƙabilanci da ɓarna a matsayin wakiliyar gwamnati. Ta yaya ba za ku kai mutane bango ba? Ga shi ta ce sai ta zagaye duka ƙananan hukumomin Kano 44 tana yaɗa wannan shashanci da sakarci.

Tana iƙirarin ana ware Fulani a sha’anin gwamnati kuma ta ce ta yi digiri har biyu, amma na rasa gane anya ta ci jarabawar lissafi kuwa? Domin sam ba ta iya ƙididdiga ba. Su waye suke tafiyar da gwamnatin, tun daga Kano har sauran jihohin Arewacin Najeriya? Su waye kenan s**a ware Fulanin?

Me ya sa ba za ku bar mutane su zauna lafiya ba? Wallahi kada ku kai mutane bango, domin tsaf za mu fara wayar da kan mutane akan wannan illar da wasunku suke yi wa Arewa.

Manzon Allah sallallahu alaiHi wasallam Ya hana mu nuna ƙabilanci. Saboda babu wata ƙabila a duniya da babu mutanen kirki da na banza a cikinta. Ko a ahalin su Donald Trump akwai yayansa da bai gaji irin halin mutanen gidan ba. Don idan aka aka ce za a yi wa kafatanin wata ƙabila kuɗin goro a matsayin ƴar ta’adda to tabbas wannan mummunan zalunci ne. Kuma ni kaina ina da jiɓi da Fulani. Har abokaina kusan kaso 7 cikin 10 duka Fulani ne.

Shi ya sa muke ta kawar da kai kada ace muna haifar da rikici tsakanin al’umma, amma ina mai rantsuwa da Allahn da nake yi wa azumi, wallahi irinku su ne babbar matsalar Arewa da dalilin da ya sa har yanzu aka kasa samun bakin zaren magance matsalar tsaron da ke cinye mu.

Kada fa ku haifar mana da yaƙi a cikin al’umma domin wannan rashin adalcin yana wuce makaɗi da rawa.

⚖️

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan Afirka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dan Afirka:

Share