πƒπ‰πŒ π“π„π‚π‡ππŽπ‹πŽπ†π˜

  • Home
  • Nigeria
  • Kano
  • πƒπ‰πŒ π“π„π‚π‡ππŽπ‹πŽπ†π˜

πƒπ‰πŒ π“π„π‚π‡ππŽπ‹πŽπ†π˜ Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from πƒπ‰πŒ π“π„π‚π‡ππŽπ‹πŽπ†π˜, Marketing Agency, 𝐊𝐚𝐧𝐨, Kano.

YADDA ZAKA GANO IDAN WANI YANA BIBIYARKA A WHATSAPP.Da farko zaka shiga whatsapp dinka bayan ya bude sai ka duba sama za...
05/05/2024

YADDA ZAKA GANO IDAN WANI YANA BIBIYARKA A WHATSAPP.

Da farko zaka shiga whatsapp dinka bayan ya bude sai ka duba sama zakaga wasu Ι—igo uku Ι“angaren dama sai ka dannasu, zakaga zaΙ“uka sun bayyana daga cikin zaΙ“ukan zakaga inda aka rubuta "LINKED DEVICES" sai ka danna gun, buΙ—ewarshi keda wuya idan ana bibiyar chat Ι—in ka zakaga adadin wayoyin da suke bibiyar chat Ι—in ka.

Wanda ke bibiyar chat dinka ta wannan hanyar yanada cikakken iko da whatsapp naka, story ne kawai ba zai iya yima ba da kuma canja profile info ko kuma description, amma zai iya chat da kowa a matsayin kai ne, hakan na nufin bibiyar chat naka yanada matukar hatsari idan bada saninka ba.

YADDA ZAKA SAUKE IDAN KAGA ANA BIBIYARKA

Bayan ka shiga "linked devices" din ka tabbatar ana bibiyarka sai ka danna kan wanda kaga yana bibiyarka zakaga daga ina ne ake bibiyarka da lokacin da shi wanda yake bibiyarka ya sauka idan kuma yana online ne a wayarsa lokacin zakaga (Active) ma'ana lokacin nan shima yana online a wayarsa yana ganin duk abinda kake yi, abinda zakayi shi ne ka duba daga sama Ι“angaren dama zakaga wasu Ι—igo uku sai ka dannasu, zakaga "REMOVE DEVICE" sai ka danna shi, nan take zakaga ya sauka, daga nan zaiyi LOG OUT a wayarshi ba zai kara ganin chat dinka ba.

Shawara: Idan har ka gane ana bibiyarka koda ka saukw akwai bukatar ka dinga dubawa lokaci-lokaci saboda tsaro ba don tsoro baπŸ˜ƒ

Ga bidiyon video Yadda zaka yi KA shiga link din nanπŸ‘‡
https://youtu.be/ooMWpfj2aLQ?si=mjiC4bHytFThigzC

Allah yasa mu daceπŸ™

24/02/2024

MADALLAH GA WANDA YA YI ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE

Imam An-Nawawi Allah ya masa rahama yake cewa, "HaΖ™iΖ™a duk wanda Allah ya waffaqa shi da yin Azkar din safiya da maraice, to ya samu falala da ni'ima mai girma a wurin Allah, madallah da shi. Wanda kuma ya gagara yin Azkar din gabaΙ—ayansu to kada ya gaza wurin yin koda kaΙ—an ne, kai koda guda Ι—aya ne ya yi Ζ™oΖ™ari ya yi"

Address

𝐊𝐚𝐧𝐨
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when πƒπ‰πŒ π“π„π‚π‡ππŽπ‹πŽπ†π˜ posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share