09/06/2026
Wai ana ta cewa vendors sunfi customers yawa ko?🤔😅
Idan naga zancen ni nake kamar na bushe da dariya, se kuma nace aa yakamata nayi uziri yanzu a wani century muke da media tayi yawa haka kuma a tsarinta tana tafiya ne da abunda kai kake yi ko km yake burgeka da ita🤩
Yakamata dai su waɗannan masu maganar su gane sunfi kusa da masu sana'a ne irinsu shiyasa suke ganin kamar sunyi yawa😀 kuma ba haka bane😃 ni yanzu a account dinnan da nake wannan post din idan na shigi banga giftawar masu abubuwa ba banajin daɗi sbd su nakeson gani.
Ni ba magana zanmuku cewa wai kowa rabansa ze samu ba aa tabbatar muku zanyii har rabon wasu se kun ci indai kun tabbata akan niyyarku, da ni da ku bamusan iya adadin mutanen dasuke zagaye damu ba.. sun ninka ninkin baninkin wanda ba sa siyarwa yawa,😀 saboda haka ni banga abun tsoro ko taahin hankali a cikin haka ba..
Duk kasuwar da kuke har abada in sha Allahy baza'a denayi daku ba, kuma ku da kuka daɗe a ciki kune mafi sanin wahalarta babu me jurewa kubar kowa yayi sha'aninsa. akwai mutane bila adadin ba km wanda ze fasa siyan kayankuu wasu ne ma zasu kari masu siya.
Kuzo kasuwa kuga yadda ake mana kuga yadda masu sai da abu 1 dayawa a rukuni ɗayaa..
Mu me zamu ce kenan?
Kuma kowaa ganin cigaba yakee kuma kullum ba'a dena gina gida a kasuwa ba kk ba'a dena buɗe shaguna ba.
shi kuma ubangiji halittunsa ba zasu ƙare ba kuma bazasu zauna babu buƙata ba.
abunda nakeso ku gane shine...
Yarinyar da bana ba'a siyamata atamfa tirmi 1 ba to shekara me zuwa zatakai wannan matakin kamar haka rayuwa take... ana kwana buƙatun mutane suna ƙaruwa hk kuma damar makin ku a kasuwa suna km daɗuwa.
Kudena wannan zancen za'aimuku dariya.
Muinhub
09-06-2026