A. Hausa Update

A. Hausa Update Domin kawo muku labaran abubuwan dake faruwa a Nigeria musamman Arewa da ma kasashen ketare batare da fifita wani bangareba! kunaimemu ta whatsapp:08136857274.

ko ta Channel whatsapp link ATK24 Hausa

27/07/2026

Cigaba hira da Muntari cha-cha
Don jin yadda takun saka ya Kare da Coach BABA GANA.
Ku biyomu dan jin yadda ta kaya...

27/07/2026

Labaran Wasanni tare da Jalilat SHAREEF Uba da Kuma Auwal T Tahir.

Cristiano Ronaldo Ka iya komawa Fagen yin finafinai na Hollywood bayan ya ajiye harkar kwallon kafa.

Haryanzu da Yana da burin cika kwallaye 1,000 adai-adai lokacin da yake DA Shekarau 41 aduniya Kuma kwantiragonsa shekara dayace ta rage da Al-Nasar ta Kasar Sau'udiyya.

25/07/2026

Yayi wannan Martaninne a wata hira da yayi da ATK24.
Muntari C**A Dan wasan Kano pillars da Barau FC.

Tsohon Kocin Pillars Ba'ayi masa rashin Adalciba hasalima godiya ya kamata yayiwa kungiyar Kano Pillars.

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi watsi da sabon zargin da tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasan...
25/07/2026

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi watsi da sabon zargin da tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya yi masa, yana mai cewa ƙoƙari ne na ɓata masa suna domin ba wa ɗan takarar da yake goyon baya dama gabanin zaɓen 2027.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Prank Shaibu ya fitar Atiku ya ce bai dace Obasanjo ya danganta marigayi tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba da zargin cin hanci ba, alhali ba ya raye don ya kare kansa.

Aminiya

Shugaba Tinubu ya amince da ƙara yawan rundunonin sojin Najeriya zuwa 12Za a kafa sabbin rundunoni a Makurdi, da Ilorin,...
24/07/2026

Shugaba Tinubu ya amince da ƙara yawan rundunonin sojin Najeriya zuwa 12
Za a kafa sabbin rundunoni a Makurdi, da Ilorin, sai Jalingo da kuma Benin.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce shugaban ya kuma amince da ɗaukar sabbin sojoji 28,000, sayen kayan yaƙi, inganta jin daɗin dakarun da kuma sabunta kayan aikin rundunar.

A cewar sanarwar, za a kafa sabbin rundunoni a Makurdi (Runduna ta 5), da Ilorin (Runduna ta 9), sai Jalingo (Runduna ta 10) da kuma Benin (Runduna ta 83).

Sabon tsarin zai sa rundunonin sojin Najeriya su kai 12, inda kowacce za ta kula da wasu jihohi da aka ware mata.

Gwamnatin ta ce za a aiwatar da shirin a matakai biyu, inda za a kammala mataki na farko nan da watan Satumba, yayin da mataki na biyu zai ƙare a watan Disamban wannan shekarar ta 2026.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when A. Hausa Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share