Takaitattun Karatuttukan Malamai

Takaitattun Karatuttukan Malamai Online GIST

SUNNONI GUDA (5) BIYAR LOKACIN SAUKAR RUWAN SAMAAnnabi ﷺ ya koyar da al'ummarsa wasu sunnoni masu tsada guda biyar na ai...
19/07/2024

SUNNONI GUDA (5) BIYAR LOKACIN SAUKAR RUWAN SAMA

Annabi ﷺ ya koyar da al'ummarsa wasu sunnoni masu tsada guda biyar na aiki da na addua a lokacin saukar ruwan sama, amma mafi yawan mutane suna mantawa da aikata wannan sunnonin lokacin saukar ruwan sama.

*1-Sunna ta Farko*
"Lokacin fara saukar ruwan sama sai kace:
*"اللهم صيباً نافعاً"*
*ALLAHUMMA SAIYIBAN NAFI'AN*

Daga Nana A'isha R.A tana cewa,lallai Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya ga ruwan sama yafara sauka yana cewa;
*(اللهم صيباً نافعاً ALLAHUMMA SAIYIBAN NAFI'AN)*
@رواه البخاري .

*2-Sunnah Ta biyu*
"Lokacin da ruwan sama yake sauka an so ka fito ruwan ya taba jikinka, yin hakan sunna ne"

Daga Anas Dan Malik R.A yana cewa:
"Ruwan sama ya samemu tare da Manzon Allah ﷺ ,sai Manzon Allah ﷺ ya yaye tufarsa har ruwan sama ya taba jikinsa,sai akace,ya Manzon Allah miyasa ka aikata haka?? "Sai yace:
*(Domin bai jima da barin wajan Allah Madaukakin sarki ba)*
@رواه مسلم .

*3-Sunnah ta Ukku*
"Idan ruwan sama ya taru, sunna ce ka dauka daga cikinsa dan yin alwala ko wanka"

Imam Nawawy Allah yayi masa Rahama yana cewa:
"Idan ruwan sama ya taru sunnane ka dauka daga cikinsa dan yin wanka da alwala daga cikisa, saboda Hadisin da aka ruwaito daga Manzon Allah ﷺ cewa:
*"Ruwan sama ya sauko sai Manzon Allah ﷺ yace: (Ku fita dan daukar ruwan da Allah ya kiraye shi ruwa mai tsarki, dan yin alwala domin godiya ga Allah)*

*4-Sunnah ta Hudu*
"Kayi addua ga Allah madaukakin sarki, ka rokeshi alkhairin duniya da lahira, domin lokacin ruwan sama, lokacin ne na amsa addu'a"

Saboda Hadisin da Manzon Allah ﷺ yake cewa:
*(Addua alokaci guda biyu ba'a mayar da su "Ma'ana karbabbune "lokacin kiran sallah da lokacin saukar ruwan sama)*
@صحيح الجامع

*5-Sunnah ta Biyar*
"Bayan an gama ruwan sama sai kace anyi mana ruwan samane daga falalar Allah da ni'imarsa, kuma kana mai yarda da hakan azuciyarka".

Saboda Hadisin Manzon Allah ﷺ lokacin da akayi ruwan sama da dare sai Manzon Allah ﷺ yace:
*(Allah Madaukakin sarki yace: Bayina sun waye gari akwai masu imani dani da kuma masu imani da taurari, wanda yace ayi mana anyi mana ruwan samane daga falalar Allah da ni'imarsa,to wannan shine yayi imani dani kuma ya kafircewa Taurari, amma wanda yace anyi mana ruwane saboda Tauraro kaza da kaza, to wannan yayi imani da Taurari ya kafircemin)*
@صحيح الجامع

Allah ne mafi sani

Allah ya rayamu akan sunnar Manzon Allah ﷺ har zuwa karshen rayuwarmu, amesn🤲🤲🤲

Projects guda 25 da zasu fashe bayan Notcoin...Idan saboda an samu Kuɗi a Notcoin ne kake ta surutu akan Crypto toh shaw...
20/05/2024

Projects guda 25 da zasu fashe bayan Notcoin...

Idan saboda an samu Kuɗi a Notcoin ne kake ta surutu akan Crypto toh shawara itace ka gyara zama da kyau domin baka fara komai ba, domin abubuwa da zasu zo bayan Notcoin sai ka rasa me zaka ce, idan yanzu kana cewa chacha ne ko Haram toh idan wadannan abubuwan 👇 s**a fashe bamu san me zaka ce ba.

1. OEX
2. Over.
3. Yulivers.
4. Tap Swap.
5. AZC.
6. Imota.
7. Blum.
8. Bera Chain.
9. Nurika.
10. OG.
11. Coin Savi.
12. Sidra.
13. Athene.
14. Silencio.
15. X-Plus.
16. Bondex.
17. WOW.
18. CG Candy.
19. CMC Diamond.
20. Marina Protocol.
21. DOP.
22. HOT.
23. OGC.
24. BWB.
25. Pi Network (Mai gidan gaba daya kenan).

Banda Airdrops din da mutane s**a yi, banda Testnet da aka yi participating.
In dai saboda kaga ana samun Kudi ne ka dauko s**an Crypto toh ka gyara zama akwai aiki ja a gaba.

🖊️Abdul-Hadee Isah Ibraheem

SHASHA BA SHASHASHA BANEWannan hoton da kuke gani a ƙasa shine Shasha Plotvinov, dan asalin ƙasar Rasha ne idan ban mant...
17/05/2024

SHASHA BA SHASHASHA BANE

Wannan hoton da kuke gani a ƙasa shine Shasha Plotvinov, dan asalin ƙasar Rasha ne idan ban manta ba. Shine Co-creator na kamfanin da ya ƙirƙiri Notcoin, mining ɗin da matasa da dama maza da mata s**a samu alkhairi a sanadinsa, musamman a nan arewacin Nigeria. Kunga kenan Shasha ba shashasha bane, addu'ar da muke mashi itace Allah ya bashi shiriya ya shigo addinin mu na Musulunci.

Mukan sayi Data domin shiga Facebook, WhatsApp, Tiktok, Instagram da sauransu kuma yawanci shirme yafi yawa a ciki, muna ɓata lokaci da yawa a cikinsu ba tare da sun biya mu komai ba, alhali kuwa suna samun maƙuddan kuɗaɗe sanadiyyar shigarsu da mukeyi kullu yaumin.

Mukan kunna games a wayoyinmu muna yi na tsawon lokaci, so da dama zaka ga matasa a majalisa sun zagaye wajen suna danna waya kai ka ɗauka wani darasi ne akeyi, amma da ka duba sai kaga game din Lido ce akeyi.

Amma yanzu sai akace idan ma ka danna wayar ka tara wani adadi na mining zaka iya samun kaɗaɗe masu yawa, gwargwadon aikin da kayi masu. Kuma datar da za'a ɗauka bata kai ta shiga waɗancan shafukan ba, kuma ɗan lokaci kaɗan ne ka gama sai kuma wani lokacin. Ai ina ganin da kaje waɗancan shafukan da na ambata ka ɓata lokacin ka, ƙara kaje kayi mining abinka.

Wallahi ban samu Notcoin ko ɗaya ba, amma na shiga farin ciki yanda naga mutanen mu dumu-dumu cikin alkhairi. Wasu sun samu jari, wasu sun samu abinda zasu rage wa kansu kebura. Wasu zasu tambaya ya akai ban samu ba, amsar itace; nayi mining din Notcoin mai yawa amma daga ƙarshe Telegram sunyi banning ɗin number ta.

Nayi guiding din mutane sun cire aƙalla kusan 2M anan kusa, wasu kuma munyi guiding ɗinsu ta waya sun cire, kuma ko ƙwandala basu saka ba. Yanzu naga masu ce wa masu mining mahaukata duk sun shigo ana ta haukan tare😎

Babu abinda zamu ce game da mining da crypto sai Alhamdulillah.

Shawara ga Notcoiners; Kuɗi a kashe su ta hanya mai kyau.

Shawara ga waɗanda basu fara mining ba; kaje Playstore ka ɗauko Telegram ka fara haƙa, ga links nan a comment section 👇

Duk rikicin neman Kuɗi da neman ilimin Boko da ake yi kar ka bari ya hana ka Haddar Al-Qur'ani ko neman ilimin Al-Qur'an...
02/04/2024

Duk rikicin neman Kuɗi da neman ilimin Boko da ake yi kar ka bari ya hana ka Haddar Al-Qur'ani ko neman ilimin Al-Qur'ani, kana barin Al-Qur'ani zaka fara ganin koma baya a cikin komai da kake yi. Ko baka ga koma baya a zahiri ba zaka ga cewa abubuwan da kake nema na duniya baka jin dadin su, kana nema ne kawai ba don kana da nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin zuciyar ka ba.

~ Idan ka koma wa karatun Al-Qur'ani kai kanka sai kayi mamakin kanka anya kaine kuwa? Saboda littafi ne mai albarka duk wanda ya riƙe shi sai albarka ta shafe shi.
In dai ka riƙe Al-Qur'ani da wahala ka shiga wata sabga ka faɗ, da wahala kayi faɗuwar da zaka gagara tashi.
~ A cikin plan dinka ya zama akwai section na Al-Qur'ani ba zallan neman duniya ba, zaka ga kafi Jin dadin yin duk abinda kasa a gaba.

~ Ka daure ka iya haɗa abu biyu, ka iya haɗa Al-Qur'ani da neman duniyar ka, kada ka koma zallan Al-Qur'ani baka neman Kudi, kada ka koma neman Kuɗi baka neman Al-Qur'ani. Babu wadanda Allah yake jefa musu albarka idan s**a rike Al-Qur'ani kamar matasa, a zahiri a Fili zasu dinga ganin albarkan Al-Qur'ani a cikin rayuwa.

🖊️ Abdul-Hadee Isah Ibraheem

02/04/2024

Duk rikicin neman Kudi da neman ilimin Boko da ake yi kar ka bari ya hana ka Haddar Al-Qur'ani ko neman ilimin Al-Qur'ani, kana barin Al-Qur'ani zaka fara ganin koma baya a cikin komai da kake yi. Ko baka ga koma baya a zahiri ba zaka ga cewa abubuwan da kake nema na duniya baka jin dadin su, kana nema ne kawai ba don kana da nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin zuciyar ka ba.

~ Idan ko koma wa karatun Al-Qur'ani kai kanka sai kayi mamakin kanka anya kaine kuwa? Saboda littafi ne mai albarka duk wanda ya rike shi sai albarka ta shafe shi.
In dai ka rike Al-Qur'ani da wahala ka shiga wata sabga ka fadi, da wahala kayi faduwar da zaka gagara tashi.
~ A cikin plan dinka ya zama akwai section na Al-Qur'ani ba zallan neman duniya ba, zaka ga kafi Jin dadin yin duk abinda kasa a gaba.

~ Ka daure ka iya hada abu biyu, ka iya hada Al-Qur'ani da neman duniyar ka, kada ka koma zallan Al-Qur'ani baka neman Kudi, kada ka koma neman Kudi baka neman Al-Qur'ani. Babu wadanda Allah yake jefa musu albarka idan s**a rike Al-Qur'ani kamar matasa, a zahiri a Fili zasu dinga ganin albarkan Al-Qur'ani a cikin rayuwa.

🖊️ Abdul-Hadee Isah Ibraheem

Assalamu Alaikum. Barkan mu da shan ruwa. Allah ya karɓa mana.Wannan receipt ɗin da kuke gani shaidar biyan kudi ne da w...
18/03/2024

Assalamu Alaikum. Barkan mu da shan ruwa. Allah ya karɓa mana.

Wannan receipt ɗin da kuke gani shaidar biyan kudi ne da wani bawan Allah ya tsakuro daga cikin Pi ɗinshi ya kawo aka saida mashi, saboda zai yi hidimar Azumi da Sallah, yanzu haka kudin suna a cikin account dinshi kwance. A hakan ma farashin Pi din ya sauka a kasuwar bayan fage.

Yanzu wannan ka ce mashi Pi ƙarya ne ko Pi scam ne ya yarda? Kuma ko ƙwandala 1 bai saka ba, kawai abinda yakeyi shine duk bayan 24 hours zai danna wani waje a cikin wayarsa shikenan.

Wannan Pi kenan. Akwai minings na nan da dama waɗanda ake yinsu akan waya waya, wanda haƙurin ɗan lokaci kaɗan zaka yi zaka samu alkhairi sosai ba tare da ka saka ko sisin kobo ba.

Ba da daɗewa ba mutane da yawa sun samu alkhairi da $ICE, $AVIVE, $WLD ga $RENEC da dai sauransu. Ga kuma Airdrops nan ba adadi.

Yanzu haka ma wasu na nan ana tayi.

Ni ban san laifin da nayi wa Nikolas ba, har yanzu ya hanani yin KYC ɗin Pi dina balantana in saida.
Ibrahim Shehu Saifullahi Lawal Yau Ibrahim Dankama ku sa baki Pi ɗina ya daskare🙄

Ana yi wa ƴan Pi dariya su kuma suna kwashe ƴan dalolinsu😆😆😆

Masu son cike aikin Fire Service ga link nan a comment section, har da ku masu SSCE.Allah bada sa'a.
30/12/2023

Masu son cike aikin Fire Service ga link nan a comment section, har da ku masu SSCE.
Allah bada sa'a.

KARIYA DAGA MUMMUNAN MAFARKAIWaɗanda suke yawan yin munanan mafarkai a cikin baccin su a dare, kamar mafarki me ban tsor...
24/12/2023

KARIYA DAGA MUMMUNAN MAFARKAI

Waɗanda suke yawan yin munanan mafarkai a cikin baccin su a dare, kamar mafarki me ban tsoro, mafarkin da yake razana mutum, ko wanda da ƙyar bacci yake ɗaukan sa, ko kuma mutum ya ringa jin tsoro me tsanani da zaran dare yayi alamu ne na Sihiri ko bibiyar Aljanu ga mutum, wanda irin wannan ke damun sa yana cikin damuwa kwarai da gaske. Amma akwai mafita.
~ Zaka ga mutum yana da karfi yana da Basira amma da zaran ya kwanta bacci toh sai hankalin sa yayi ta tashi, ya shiga tsoro da fargaba da ganin munanan abubuwa.

~ Malamai s**a ce daga cikin hanyoyin da ake rabuwa da irin wannan matsalar shine amfani da hanyoyi uku da Manzon Allah ya koyar:

Manzon Allah ya nunawa mutane cewa duk sadda zasu kwanta bacci a dare suyi Al-wala, sai su karanta:

1.

Subhanallah - Sau 33.
Alhamdulillah - Sau 33.
Allahu Akbar - Sau 34.

2.

Wannan Al-walar Manzon Allah ya fadi amfanin ta shine "Allah zai aiko da Mala'iku dauke da Makamai (Weapons) suyi Gadin jiki da ruhin mutumin da ya kwanta da Al-wala".

3.

Karanta Ayoyi daga Suratul Bakarah da daddare, ko Aya daya ce ka karanta daga Suratul Bakarah, ko Aya 5, ko 10 ko 20, duk yadda ya sauwaka, in dai kana da irin wannan matsalar kar ka yarda dare yayi baka karanta wani abu daga Suratul Bakarah ba.

Dan haka Malamai s**a ce idan Aljanu suna bibiyar ka, idan Mayu ko Matsafa suna bibiyar ka a cikin dare 'kofar da suke bin zata kulle.
~ Wadancan Zikirorin kuma zasu saukaka maka kwanciyar, tare da tsare ka daga Shedan da yake razana ka da mafarkai, Zikirorin zasu hana Aljanu su ganka ko suga ruhin ka a lokacin da kake bacci.

Idan kaje ka duba asalin Hadisin Zikirori 33, 33 da 34 zaka ga cewa Nana Fadima (R.A) ce ta tambayi Manzon Allah tace aiyuka s**an yi mata yawa a gidan Mijin ta, Shara, Wanke wanke, aiyuka da yawa kuma takan gaji, sai tace wa Mahaifin ta Manzon Allah ya nema mata 'yar aiki (House girl) da zata dinga taya ta aiki.
~ Sai Manzon Allah yace mata idan taje za tayi bacci ita da Mijin ta su karanta Subhanallah 33, Alhamdulillah 33, Allahu 34. Idan sunyi haka zasu samu sauki. Kuma haka aka yi.

Wannan sirri ne ga wanda wani abu yake damun sa, ya karanta wannan idan yazo bacci, in sha Allah matsalar zata ware koda aiyuka ne suke maka yawa. B***e mafarki ko tsoro a cikin dare.
~ Akwai wani Sirri a cikin wannan Azkar din guda 33, 33 da 34 idan ka rike su gam zaka ga yadda Allah zai wadata maka 24 hours dinka, zaka ga kayi abubuwa da yawan gaske masu amfani, wanda aka kuntata masa 24 hours dinsa ba zai iya yin abinda kayi ba, ka gwada ka gani, zaka ga an sake maka fasalin 24 hours dinka. Wannan wani Sirri ne daga sirrorin da Ubangiji yake yiwa bayin sa.

~ Misali, ka duba manyan litattafan da Malamai s**a rubuta da hannun su da Tawada a zamanin Da, a yanzu idan aka ce ka karanta rubutun su a rayuwar ka sai kaga ba zai yuwu ba, rubutun Malami daya kawai, abinda zaka tambayi kanka shine yaushe s**a samu time din da s**a yi wannan rubutun haka?
~ A cikin 24 hours da ake yi har s**a iya yin hakan? saboda sun fimu riko da Azkar din, shiyasa aka wadata 24 hours dinsu fiye da namu.

~ Iyaye mata da suke rainon Kananan Yara ko jarirai zasu ga wani lokaci Yara suna kuka me tsanani a wani lokaci na dare haka kawai, irin kuka da basa yi da rana, su dinga karanta musu wannan addu'ar a dai dai Goshin su, wato a karanta Azkar din sai a shafa akan su ko Goshin su.

Idan kana so ka rabu da wadanda matsalolin sai ka dage da yin wadannan har na tsawon Makwanni ko watanni ba wai yau da gobe kadai ba.

🖋️Abdul-Hadee Isah Ibraheem

A RANAR JUMU'A ANA SON A YAWAITA SALATI GA ANNABI (SAW)Allah maɗaukakin Sarki yace:ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘَﻪُ ﻳُﺼَﻠُّ...
22/12/2023

A RANAR JUMU'A ANA SON A YAWAITA SALATI GA ANNABI (SAW)

Allah maɗaukakin Sarki yace:

ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻣَﻠَﺎﺋِﻜَﺘَﻪُ ﻳُﺼَﻠُّﻮﻥَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ۚ ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ
ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺻَﻠُّﻮﺍ ﻋَﻠﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠِّﻤُﻮﺍ ﺗَﺴْﻠِﻴﻤًﺎ

Lalle, Allah da mala’ikunSa suna salati ga Annabi.
Ya ku waɗanda s**a yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi

🍃 *اللَّهُمَّ صَلٌِ عَلَى مُحَمَّدٍ وَّ عَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ*

*اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَّ عَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيد*

Annabi( Sallallahu alaihi Wasallama.)yana cewa: (Yana cikin mafificiyar Ranakunku Ranar Juma'a, dan haka ku yawaita yin Salati agareni acikinta, domin ana bujuromin da salatinku gareni)

Annabi (Sallallahu alaihi Wasallama) yace: (Duk wanda yayi salati a gareni, Allah zaiyi masa salati Guda Goma).

KADAN DAGA CIKIN FALALAR SALATI GA ANNABI (Sallallahu alaihi Wasallama)

~Wanda yayiwa Manzon Allah s.a.w Salati ya cika Umarnin Allah ne dayiwa dukkan masu imani.

~Kuma yayi koyi cikin Abinda Allah da Mala'ikunsa suke yi ga Annabi( Sallallahu alaihi Wasallama)

~Wanda yayi Salati guda ga Annabi( Sallallahu alaihi Wasallama)Allah zaiyi masa Huda Goma.

~Za'a Rubuta masa Lada Guda Goma kuma a kankare masa zunubai guda goma.

~Za'a Daukaka darajarsa sau goma.

~Allah yana Amsa Adduar da akayi tare da Salatin Annabi( Sallallahu alaihi Wasallama) Acikinta.

~Yana samun Ceton Annabi (Sallallahu alaihi Wasallama) ga mai Yawaita salati ga Annabi s.a.w.

~Hanyace ta samun gafarar Allah.

~Hanyace ta Samun kariya da tsaron Allah ga mai yawaita salati ga Annabi (Sallallahu alaihi Wasallama)

~Manzon Allah( Sallallahu alaihi Wasallama) yana mayar da Salati ga dukkan wanda yayi masa Salatin.

~Yin salati ga Manzon Allah( Sallallahu alaihi Wasallama) a wajan Zama yana sanyawa Mutum Rashin Asara a Ranar Alkiyama.

Allahumma salli wa sallim ala Muhammadin wa ala alihi wa sahbihi wa sallim.

YIN SALLAR ASUBA AKAN LOKACI, MUSAMMAN YINTA A CIKIN JAM'IYin sallar Asuba akan lokaci musamman yinta a cikin jam'i tana...
20/12/2023

YIN SALLAR ASUBA AKAN LOKACI, MUSAMMAN YINTA A CIKIN JAM'I

Yin sallar Asuba akan lokaci musamman yinta a cikin jam'i tana bude kofofin nasara da farin ciki a cikin rayuwa.
~Duk yawan commitment dinka kar ka bari fita Asubah ya gagare ka, musamman yanzu da ake yin sanyi.
~ Samun Asubah akan lokaci, musamman a cikin Jam'i nasara ce da mutanen kirki suke lissafa ta cikin nasarorin su.

Alkhairin da ake samu a kwanakin da aka samu Sallar Asubah a cikin su daban suke da kwanakin ba'a samu Asubah a cikin su ba, wannan a cikin sha'anin rayuwa kenan, harkar samu da rashi na yau da gobe.
~ Mazan gaske su ake gani a Asubah, Mazan da s**a amsa sunan Maza, Rijaal, Men of God.

LA ILAHA ILLALLAH  (لا إله إلا الله)Wata rana Annabi Musa Bin Imraan (A.S) yana so yayi addu'a kuma yana cikin tsananin ...
17/12/2023

LA ILAHA ILLALLAH (لا إله إلا الله)

Wata rana Annabi Musa Bin Imraan (A.S) yana so yayi addu'a kuma yana cikin tsananin buƙatar Allah ya amsa masa, sai yayi magana da Allah yace "Ya Allah ka bani wata kalma wacce duk lokacin da nake son yin addu'a zanyi amfani da ita in roƙe ka".
~ Sai Allah yace "Ya Musa kace Laa ilaha illal Lah, ka dinga amfani da wannan kalmar duk sadda za kayi addu'a, na baka ita", sai Annabi Musa yace "Ya Rabb, dukkan bayin ka (Muminai) suna fadin Laa ilaha illal Lah". Wato ina so a bani wata kalma ta musamman (Special) ba wannan da kowa yake faɗin ta ba.

~ Sai Allah yace masa babu wata kalmar data kai wannan kalma ta "Laa ilaha illal Lah" b***e ta fi ta.
Allah yace Ya Musa bari kaji:
"Da ace za'a ɗauko sammai bakwai da abubuwan da suke cikin sammai (na Rana, Watanni, Taurari, duniyoyi, Galaxies, Super Galaxies da Milky ways) banda ni, Allah".

~ A ɗauko 'ƙassai bakwai da duk abinda ke cikin su, a hade su a 'dora akan Sikelin auna kayan nauyi a ɗora a gefe ɗaya na Sikeli, a ɗauko kalmar Laa ilaha illal Lah a ɗora ta a ɗaya gefen, wallahi sai Laa ilaha illal Lah ta rinjaye su, wajen nauyi da girman ta, dan haka Ya Musa babu kamar Laa ilaha illal Lah ga duk Wanda yake so ya roke ni".
~ Tun daga ranar Annabi Musa idan yana da buƙata a wajen Allah yakan zauna yayi ta ambaton Laa ilaha illal Lah, tare da kusanto da ma'anar ta a zuciyar sa, sai yayi addu'a.

~ To kaima kaji, kema kin ji, indai kana da addu'a, wata bukata, ka aiwatar da wata Ibada kamar sallah ko karatun Al-Qur'ani, ko sadaka, ka zauna a wajen kayi Laa ilaha illal Lah, sau adadi mai yawan gaske, sai ka fadi bukatun ka, in sha Allah idan kana yawan yin haka zaka ga canji akan bukatu da matsalolin da suke damun ka, da abubuwan da kake son cimma su a rayuwa.

Allah ya karba mana, yasa mu dace....
Abdul-Hadee Isah Ibraheem

Sallar Walaha (Salatud Dhuhaa) Manzon Allah (S.A.W) yace "Sallar mutanen kirki".   ~ Idan kana so ka gwada kanka shin ka...
16/12/2023

Sallar Walaha (Salatud Dhuhaa) Manzon Allah (S.A.W) yace "Sallar mutanen kirki".

~ Idan kana so ka gwada kanka shin ka bin Sahun mutanen kirki musamman wajen neman Lada ta hanyar Nafilfili toh ka gwada kanka wajen yin Sallar Walaha ko rashin yin ta. Bari kaji wani abu, ita Sallar Walaha takan budewa mutum 'kofar Rahama, Arziki (Kudi) da warkewar rashin lafiya ne.

Idan kana so ka gane ta a harshen zamani toh sai ince ko ka san Morning 🌅 Exercise? (Morning jogging)? da safe zaka ga wasu mutane musamman masu Kudi ko masu Kiba s**an fita da sassafe suje suyi gudu, su jijjige jikin su, su dawo suyi wanka.
~ Dadin da suke ji tun daga safe har dare daban ne da ranar da ba suyi wannan jogging din ba. Kwakwalwar takan bude, Basira da fikira a wannan ranar daban ce.

Toh Sallar Walaha ta zarce wannan morning jogging din, (spiritually), amma fa duk da haka ba ina s**an Morning jogging bane, domin yana da amfani ga lafiyar mutum, kada a fahimci bayanin a juye.
~ Sallar Walaha kamar muce itace (spiritual morning jogging) alkhairin da zata jawo maka a wannan ranar ba kadan bane, wadanda s**a saba yi zaka basa dainawa, saboda sun san me suke samu sun san me suke ji a jikin su duk rana. Zaka ga ko ana sanyi sai sunyi, ko ana zafi ko Damina sai sun fita morning jogging, toh haka Sallar Walaha a wajen mutanen kirki.

Lamarin zai fi burgewa zai fi bayar da kala ace kana Morning jogging kuma kana yin Sallar Walaha, haske bisa haske kenan.
~ A Arewacin Nigeria anyi kuskuren bayanin Sallar Walaha ada, cewa wai Sallar Tsofi ne, kuma idan an fara ba'a dainawa, wannan ba daga karatun Annabi Muhammadu bane, gaskiya.

~ Hukuncin ta, Sunnah ce me karfi:

Idan ka samu dama kayi, idan baka samu ba babu laifi, maganar da ake cewa wai idan ka fara yin Sallar Walaha ba'a dainawa wannan ba gaskiya bane, ba Hadisin Annabi bane.
~ Saboda muhimmancin ta har a ranar Fatahu Makkah sai da Manzon Allah ya shiga wani Gida da sauri da gaggawa yaje yayi Sallar ya fito, wata Baiwar Allah ta shinfida masa Sallaya yayi Walaha.

Nana Aisha (R.A) tace:
Manzon Allah yakan yi Sallar Walaha Raka'a hudu, kuma yakan 'kara fiye da haka ma.
Karanta Sahihu Muslim, Hadisi na 1,176.

Ya halatta kayi ta raka'oi 2, ko 4, ko 6, amma ba'a wuce Raka'oi 8.

A yanzu (December 2023) musamman a nan yankin North Eastern Nigeria, muna fara yin ta daga karfe 7:30 na safe (a yadda nake fahimta) har zuwa karfe 11:30 na safe ko ma sama da haka kafin 12:00 Noon.

Yanayin lokutan s**an sha banban daga waje zuwa waje, sai ka lura da yankin da kake, ko wajen da k**e, Allah yasa mu dace....
Babu wadanda s**a fi ganin tasirin wannan Sallar kamar matasa, yam mata, da masu karancin shekaru idan suna yi, daga 'yan shekaru 55 zuwa kasa.

~ Kada ka gafala 'dan uwa, sabgogin rayuwar nan suna da yawa, kuma ana cikin su tsamo tsamo ake wuce zuwa cikin Qabari.

Karanta Sahihul Bukhariy, Hadisi na 1,178.

Karanta Sahihu Muslim, Hadisi na 748.

Sunanut Tirmiziy, Hadisi na 437, Sheikh Muhammad Nasir Al-baniy yace Hadisin Sahihi ne.
Allah ya karba mana yasa mu dace....
✍️:
Abdul-Hadee Isah Ibraheem

Address

Katsina
Dankama
820103

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Takaitattun Karatuttukan Malamai posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share