26/04/2026
Sanata Muntari Mohammed Dandutse, mai wakiltar Katsina ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya halarci taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC da aka gudanar a yau Lahadi a birnin Katsina.
A yayin taron, jam’iyyar ta amince da amfani da tsarin sasanci/sulhu (consensus) wajen gudanar da zaɓen fidda gwani na kakar zaɓen shekarar 2027.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar.
Da yake jawabi, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su rungumi haɗin kai, ladabi da kuma sauke amanar da al’umma ta ɗora musu, yayin da jam’iyyar ke shirin tunkarar zaɓukan da ke tafe.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin ci gaba da hulɗa da ‘ya’yan jam’iyya da al’umma domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da ginshikin APC a jihar.
Ya bayyana cewa an yi la’akari da tsarin sulhu ne bayan tattaunawa da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce tsarin zai ba da damar yin sasanci inda ya dace, tare da gudanar da zaɓe a wuraren da hakan ya zama dole.
A cewarsa, tsarin sulhu zai taimaka wajen rage rikice-rikicen cikin gida, ƙarfafa haɗin kai, da kuma inganta zaman lafiya a cikin jam’iyya.
Gwamna Radda ya kuma gargaɗi masu neman takara da su guji kashe kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa shugabanci nauyi ne da ya kamata a ɗauka da gaskiya, rikon amana da tawali’u.
Hakazalika, ya buƙaci mambobin jam’iyyar da su fifita muradun jam’iyya fiye da na kansu, tare da mara wa waɗanda s**a samu nasara baya domin ciyar da jam’iyyar gaba.
A nasa jawabin, Shugaban APC na Jihar Katsina, Alhaji Bashir Gambo Saulawa, ya yaba wa masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar, tare da jaddada shirinta na gudanar da zaɓen fidda gwani cikin nasara.
Ya sanar da cewa an fitar da jadawalin zaɓen fidda gwani domin ba da cikakken jagoranci ga dukkan matakan da s**a shafi gudanar da zaɓukan.
Saulawa ya ce jam’iyyar za ta yi amfani da tsarin sulhu inda ya dace, biyo bayan shawarwari masu zurfi da masu ruwa da tsaki, domin ƙarfafa haɗin kai da rage rikice-rikice.
Haka kuma, ya sanar da kafa muhimman kwamitoci da s**a haɗa da Kwamitin Sulhu da Sasanci wanda tsohon gwamna Aminu Bello Masari ke jagoranta, tare da tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema a matsayin mataimaki.
An kuma kafa kwamitocin sulhu na yankuna uku: Katsina (Sanata Ibrahim Ida), Funtua (Hon. Tukur Ahmed Jikamshi) da Daura (Arc. Ahmed Musa Dangiwa).
Bugu da ƙari, an kafa Kwamitin Tabbatarwa (Affirmation Committee) domin tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan matakan zaɓen.
Taron ya samu halartar mataimakin gwamna, shugaban majalisar dokokin jiha, mambobin majalisun dokoki na ƙasa da jiha, da wakilai daga ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Jam’iyyar APC ta nuna ƙwarin gwiwa cewa tsarin sulhu zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da kuma samun nasara a zaɓukan 2027.
Dandutse Media Reporter

26 ga Afrilu, 2026
26 ga Afrilu, 2026