13/08/2026
ADC Ta Yi Alkawarin Takaita Kashe Kuɗin Gwamnati Idan Ta Lashe Zaɓen 2027
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta gabatar da wasu tsare-tsare masu faɗi kan yadda ya kamata a riƙa kashe kuɗaɗen gwamnati, ciki har da soke tsarin “Security Vote”, ƙara tsaurara matakan kula da tafiye-tafiyen jami’an gwamnati da kuma hana amfani da kadarorin gwamnati domin amfanin kashin kai, idan jam’iyyar ta kafa gwamnati a shekarar 2027.
Jam’iyyar ta ce waɗannan matakai wani ɓangare ne na babban shirin sake fasalin yadda ake gudanar da mulki a kasar, wanda aka tsara domin rage almubazzaranci, ƙarfafa bin diddigin yadda ake amfani da kuɗaɗen gwamnati da kuma mayar da albarkatun gwamnati wajen inganta rayuwar ’yan Najeriya da kuma ci gaban tattalin arziƙi.
An bayyana waɗannan tsare-tsare ne a cikin wani kundi me dauke da shafuka 25 na manufofin shugabanci da ƙa’idojin ɗabi’a na ADC, mai suna “The Orange Book”, wanda Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya ƙaddamar a Abuja ranar Talata.
Takardar ta mai da hankali sosai kan tsare-tsaren kashe kuɗi cikin hankali da kuma tabbatar da bin diddigin ayyukan hukumomin gwamnati, inda jam’iyyar ta ce dole ne gwamnati ta gudanar da harkokinta cikin ƙarin gaskiya da bayyananniyar hanya idan ana son Najeriya ta shawo kan matsalolin tattalin arziƙinta tare da dawo da amincewar jama’a.
Ɗaya daga cikin manyan shawarwarin jam’iyyar shi ne soke ware kuɗin “Security Vote” a matsayin kuɗi guda ɗaya da kuma sauran wasu kuɗaɗen tsaro da jam’iyyar ta ce ba sa samun cikakken bincike da sa ido daga majalisa.
A ƙarƙashin sabon tsarin da ADC ta gabatar, duk wani kuɗin da gwamnati za ta kashe wajen tsaro zai buƙaci sa ido, amincewa da kuma binciken majalisa, bisa tanade-tanaden dokokin ƙasa.
Jam’iyyar ta ce manufar wannan mataki ita ce rufe hanyoyin karkatar da kuɗaɗen gwamnati ko yin amfani da su ba bisa ka’ida ba, tare da tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen da aka ware wa tsaro ne domin manufar da aka tanada mu