Bilhaqqi Media Links

Bilhaqqi Media Links Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bilhaqqi Media Links, Katsina.

Media Channel....~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~Kuna Iya Tuntubar Mu Domin Bayyana Raayoyin Kan Abinda Ya Shafi Harkokin Yau Da Kullum Da Kuma Siyasa Daga Ko Ina Ku Ke Mungode 0.8.0.6.9.4.5.0.2.6.2.......

Ku bamu Karin magana Daya akan wannan hoton nide nace ka koshi ga kwanan yinwa😔
12/09/2026

Ku bamu Karin magana Daya akan wannan hoton nide nace ka koshi ga kwanan yinwa😔

fittacen mawakin Nan ado isah gwanja Yana fama da matsanan ciyar rashin lfy ya Allah ubangiji yabashi lfy da dukkan Musl...
10/09/2026

fittacen mawakin Nan ado isah gwanja Yana fama da matsanan ciyar rashin lfy ya Allah ubangiji yabashi lfy da dukkan Muslimi duniya bakidaya Alfarmar muhammadun rasulillahi s a w ameen

INNANILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJI'UN: Cikin Alhini Nake Sanarda Ku Cewa, Allah Ya Amshe Rayuwar  Zainab Zee DiamondTa ras...
07/09/2026

INNANILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJI'UN: Cikin Alhini Nake Sanarda Ku Cewa, Allah Ya Amshe Rayuwar Zainab Zee Diamond

Ta rasu bayan sallar assuba din yau bayan tayi fama da doguwar jinya.

Allah ya miki rahama Zainab 😭😭😭

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya tabbatar wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cewa Jihar Katsina tana ta...
05/09/2026

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya tabbatar wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cewa Jihar Katsina tana tare da shi, yana mai cewa cikin sauƙi zai samu nasara a zaɓen da ke tafe.

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a yau Asabar, yayin taron PBAT Door-to-Door Movement na Tinubu/Shettima 2027 da kuma ƙaddamar da tsarin ƙungiyar a Jihar Katsina, wanda aka gudanar a People’s Square, Katsina.

A yayin jawabin nasa, Gwamna Radda ya ce: “Tinubu, kada ka ji komai, Jihar Katsina taka ce, kuma cikin sauƙi za ka ci zaɓenka da rinjaye.”

Ya kuma bayyana cewa ’yan APC a Jihar Katsina uwarsu ɗaya ce, ubansu ɗaya, yana mai cewa duk wanda aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a jihar, ’yan jam’iyyar za su mara masa baya.

Gwamna Radda ya jaddada cewa haɗin kan ’yan APC a Jihar Katsina zai taimaka wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar da dukkan ’yan takararta a zaɓukan da ke tafe.

Alhamdulillah, Alhaji Tanimu Akawu Jiki yayi sauki Marasa lafiya na gida da asibiti Allah ka basu lafiya Alfarmar Manzon...
05/09/2026

Alhamdulillah, Alhaji Tanimu Akawu Jiki yayi sauki
Marasa lafiya na gida da asibiti Allah ka basu lafiya
Alfarmar Manzon ALLAH S.A.W 🤲🏻

Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta yi gargadi kan abin da ta bayyana a matsayin wani babban bala’i da sabbin...
05/09/2026

Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta yi gargadi kan abin da ta bayyana a matsayin wani babban bala’i da sabbin kafafen sada zumunta da fasahar AI ke iya haifarwa.

Hadiza Gabon ta bayyana hakan ne yayin da take magana kan yadda fasahar zamani, musamman Artificial Intelligence (AI), ke ƙara samun karɓuwa da tasiri a kafafen sada zumunta.

Jarumar ta nuna damuwa kan yadda ake amfani da sabbin fasahohin wajen ƙirƙira da yaɗa hotuna, bidiyoyi da wasu bayanai da ka iya rikitar da jama’a.

Ta ce idan mutane ba su yi taka-tsantsan wajen amfani da waɗannan fasahohin ba, lamarin na iya haifar da matsaloli masu yawa a cikin al’umma.

Hadiza Gabon ta ce: “Bala’in da yake tinkaro mu ta hanyar sababbin kafafen sada zumunta na AI, idan ba mu dawo hayyacinmu ba, sai dai mu roƙi Allah ya sauƙaƙe.”

Innalillahi wa inna ilayhir raju un Allah yayiwa jarumar Kannywood Jamila Gwazo rasuwa jiya juma'a, ta rasu ne sakamakon...
05/09/2026

Innalillahi wa inna ilayhir raju un

Allah yayiwa jarumar Kannywood Jamila Gwazo rasuwa jiya juma'a, ta rasu ne sakamakon ciwon ciki.

Jarumar ɗaya ce daga cikin masu fotowa a shirin Dadin Kowa na Arewa24.

Muna rokon Allah yayi mata rahma yabata ladan shahada amin

Daga Bin Bala Rabiu

Baƙar mace ta farko da ta fara aiki a kamfanin kayan ado "Ford Agency" na ƙasar America Ɓaƙar mace ta farko da aka fara ...
05/09/2026

Baƙar mace ta farko da ta fara aiki a kamfanin kayan ado "Ford Agency" na ƙasar America

Ɓaƙar mace ta farko da aka fara wallafawa a mujallar "Harper’s Bazaar"

Saboda kyan fuskar ta da kyan jikin ta, aka ware mata shafuka na musamman acikin mujallar "American Vogue"

Ta kammala karatun digirin shari’a a Jami’ar Cambridge University

Tayi "Call to Bar" a Ingila

Tayi zama ministan harkokin ƙasashen waje

Tayi zama a ofishin jakadancin America

Ta auri wani ƙwararren injiniyan jiragen sama a ƙasar London, kuma yariman gidan sarauta "Wilberforce Nyabongo"
-----------------------

Yanzu ta tsufa sosai (90 years) +

Kyan fuskarta ya gushe

Dirin jikinta ya zube

Gashin kanta yayi fari

Fatar jikinta ya tsuke

Haƙoranta sun zube

Bata riƙe da kowane irin muƙami

Ta dawo gida a ƙasar Uganda 🇺🇬 da zama
--------------------------

⚠️ Duniya ɗauka take tana ajiyewa

Yau idan kaine a sama, gobe zaka sauka wani ne zai hau

Duk wanda duniya ta hanashi bin Allah da tsoron Allah, shine cikakken asararre.

Tinubu Na Sane Da Halin Ƙuncin Rayuwar Da Kuke Ciki, Saƙon Gwamnonin APC Ga Ƴan Nijeriya
03/09/2026

Tinubu Na Sane Da Halin Ƙuncin Rayuwar Da Kuke Ciki, Saƙon Gwamnonin APC Ga Ƴan Nijeriya

03/09/2026

Matan wace jiha ce sukafi yiwa Miji biyayyar Aure ? A Arewa kowa ya fada mana ra'ayi sa

Address

Katsina
820252

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bilhaqqi Media Links posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Bilhaqqi Media Links:

Shortcuts

Share