26/02/2026
Cin Zarafin Dan Jarida: SSR na Gwamnan Kano ya nemi afuwar yan jarida
Gwamnatin Jihar Kano tare da SSR na Gwamna Abdullahi Rogo sun bai wa ’yan jarida hakuri kan zargin cin mutuncin daya daga cikin mambobinsu, bayan wani zaman sulhu da aka gudanar domin warware rikicin.
Sulhun ya biyo bayan zaman da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kira a ranar Laraba domin daidaita al’amuran da s**a lalace tsakanin bangarorin.
Taron ya samu halartar shugabannin kungiyar Kano Online Media Chapel karkashin jagorancin shugabanta, Comrade Abubakar Abdulƙadir Dangambo, da daraktocin Ma’aikatar Yada Labarai, tare da dan jarida kuma tsohon shugaban ƙungiyar ƴan jaridu ta ƙasa, Comrade Abdullahi Datti Arzai.
Da yake jawabi yayin taron, Kwamishina Waiya ya bukaci SSR Rogo da sauran jami’an gwamnati da su rika kyautata alaka da ’yan jarida domin ci gaban jihar. Ya kuma jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da aiki kafada da kafada da kafafen yada labarai, yana mai amincewa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
A nasa bangaren, Shugaban Kano Online Media Chapel, Comrade Abdulƙadir Dangambo, ya gode wa kwamishinan bisa saurin shiga tsakani da ya yi wajen warware matsalar. Sai dai ya nuna cewa ba wannan ne karo na farko da ake zargin SSR Rogo da irin wannan hali ba, lamarin da ya bayyana a matsayin abin takaici.
Ya kuma ja hankalin jami’an gwamnati da su fahimci muhimmiyar rawar da ’yan jarida ke takawa a cikin al’umma da kuma tasirin aikinsu wajen inganta dimokuradiyya da gaskiya.
Lamarin dai ya zo ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na cikin da wajen kasar nan s**a yi Allah wadai da faruwar al’amarin, tare da bai wa gwamnatin jihar wa’adin sa’o’i 24 ta dauki mataki ko kuma su dauki matakin shari’a.
Bangarorin sun bayyana fatan cewa sulhun da aka cimma zai taimaka wajen gyara alaka da kuma kauce wa maimaita irin wannan lamari a nan gaba.