26/08/2026
Kano: Mutum ɗaya ya mutu bayan da wani magidanci ya buɗe wuta akan ƴan biki saboda ƙarar kiɗa ta dame shi
Wani mutum mai shekaru 34, mai suna Rabiu Mukthar, ya buɗe wuta kan mahalarta wani bikin aure a Kano, inda ya kashe mutum guda tare da jikkata wasu uku.
Lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin, wanda ke zaune a unguwar Tudun Yola, ya fusata saboda ƙarar kiɗan da ake kunnawa a wajen bikin.
Kakakin Rundunar ’yansandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa Mukthar ya fito daga gidansa ya fara harbin mutanen da ke halartar bikin.
A cewar Kiyawa, wanda ake zargin ya yi amfani da bindigar pump-action wajen harbin jama’ar da ke wajen taron.
Ya ce bayan samun rahoton harin, ’yan sanda sun gaggauta isa wurin tare da cafke Mukthar da wani mutum guda da ake zargi da hannu a lamarin.
Kakakin rundunar ya ƙara da cewa an kwato bindigar da ake zargin an yi amfani da ita wajen kai harin daga hannun Mukthar.
Kiyawa ya ce a lokacin bincike, wanda ake zargin ya shaida wa ’yan sanda cewa masu shirya bikin ba su tuntube shi ba kafin gudanar da taron.
Ya kuma ce Mukthar ya bayyana cewa hayaniyar kiɗan ta hana shi barci, lamarin da ya sa ya fusata tare da kai harin.
A halin yanzu, ana tsare da waɗanda ake zargin a sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yansandan jihar Kano, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.