22/04/2025
SANARWA
AN KUSAN RUFE SIYAR DA FOM DIN NEMAN TALLAFIN KARATU A JIHAR KATSINA NA SHEKARAR 2024/2025
A na sanar da jama'a cewa siyar da fom din neman tallafin karatu na Jihar Katsina na shekarar karatun 2024/2025, wanda aka fara a baya, na dab da zuwa karshe.
Dukkan โyan asalin Jihar Katsina da ke karatu a cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare a sassa daban-daban na Najeriya, ana shawartar su da su gaggauta cike fom din kafin lokaci ya kure.
Za a iya samun fom din ta hanyar shafin yanar gizo na hukumar: www.ktssb.org.ng
Bayan an kammala cike fom din a yanar gizo, dole ne a buga fom din sannan a hada da wadannan takardu k**ar haka:
- Takardar karbar shiga makaranta (Admission Letter)
- Rasidin rajista ko Remita Payment
- Sak**akon jarrabawar SSCE
- Takardar kammala firamare
- Takardar shaidar asalin dan jihar (Certificate of Indigene)
- Takardar haihuwa (Birth Certificate)
Wadannan takardu su ne sharuddan da za a buฦata yayin ganawar tantance cancantar samun tallafin karatun da hukumar za ta gudanar a makarantun gaba da sakandare daban-daban a fadin Najeriya.
Salisu Lawal Kerau
Jamiโin Hulda da Jamaโa
Don: Sakataren Zartarwa