Isah Miqdad Project Promoters

Isah Miqdad Project Promoters Official page for Isah Miqdad Project Promoters

12/05/2026

Yanda Shugaban Karamar Hukumar Katsina Hon. Isah Miqdad AD Saude, yayi bankwana da bada guzuri ga shuwagabannin maniyata aikin hajjin karamar hukumar Katsina, a karkashin Jagorancin Amiril Hajjin karamar hukumar Katsina, Vice Chairman Hon Usman Yusuf Saulawa

11/05/2026

Yanda Shugaban Karamar hukumar Katsina Hon. Isah Miqdad AD Saude ya hannanta sabbin motocin aikin ofis ga Kansila Mazabar Wakilin Kudu II Hon Nura Adamu da Kuma Kansila Mazabar Shinkafi “A” Hon Imrana Sa’idu Shinkafi k**ar yadda Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda PhD, CON ta bada umurni.

25/04/2026

Yanda Shugaban Karamar Hukumar Katsina Hon. Isah Miqdad AD Saude ya halarci taron gagarumar liyafar cin abincin dare (Dinner) tare da Professor Isa Ali Pantami a daren jiya juma’a, a babban dakin taro da ke “Hillside Royal Suites Katsina.”

Taron da hukumar makarantar Katsina State Institute of Technology and Management (KSITM) ta shirya a matsayin wani bangare na murnar baban bikin yaye dalibanta da s**a kammala karatu tun daga shakarar 2016 zuwa 2025, wanda zai gudana a yau asabar 25/04/2026.

17/04/2026

ZIYARAR BAZATA GA AL’UMMAR MAZABAR SHINKAFI “A”

A daren jiya alhamis 16-04-2026, Shugaban Karamar Hukumar Katsina Hon. Isah Miqdad AD Saude ya kai ziyarar sa da zumunci da jin korafe korafen al’ummar girin SHINKAFI da DAN NABASO

14/04/2026

Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude a loakcin da Mai Girma Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda PhD CON ya rattaba hannu akan dokar ta ɓaci kan kauraye, dilolin kwaya, da masu kwacen waya a cikin garin birnin Katsina, tare da samar da kotun tafi da gidan ka domin yin hukunci nan take ga duk wanda aka k**a da laifin.

13/04/2026

Daga fadar gidan gwamnatin jihar Katsina, inda Shugaban Karamar Hukumar Katsina Hon Isah Miqdad AD Saude ya jagoranci jami’an tsaro, wakilin magajin gari, masu unguwanni, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, a wani zama na musamman da Mai girma gwamnan jahar Katsina Mallam Dikko Umar Radda PhD, CON ya jagoranta domin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi cikin birnin Katsina musamman harkar kauraye, yan daba da masu kwacen waya.

Tsaro!!!Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya samar da fitilu masu amfani da hasken rana sama ...
12/04/2026

Tsaro!!!

Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya samar da fitilu masu amfani da hasken rana sama da guda ashirin ga al’ummar unguwannin Shararar Pipes da Farin Masallaci, dake cikin Mazabar Wakilin Kudu III, a wani mataki na inganta tsaro da walwalar al’umma, musamman a lokutan dare.

An gudanar da bikin kaddamar da fitilun ne karkashin jagorancin Kansilan Mazabar, Hon. Abdullahi Yusuf, tare da hadin gwiwar Kansila mai kula da sashen lafiya, Hon. Kabir Jimaita, wanda shima dan asalin yankin ne.

A yayin taron, Hon. Abdullahi Yusuf ya bayyana cewa wannan tallafi na daga cikin kokarin da Shugaban Karamar Hukumar ke yi wajen dakile matsalolin tsaro, musamman duba da yadda yankin ya fuskanci kalubale irin su fashin wayoyi, rikice-rikicen dare, da sauran ayyukan bata-gari.

Ya kara da cewa za a girke fitilun a wurare daban-daban masu muhimmanci domin tabbatar da ingantaccen tsaro da walwala ga al’ummar yankin.

A nasa jawabin, Hon. Kabir Jimaita ya yabawa Shugaban Karamar Hukumar bisa saurin daukar mataki wajen sauraron koken al’umma da kuma samar da wannan muhimmin tallafi cikin kankanin lokaci.

Taron ya samu halartar Kansila mai kula da sashen ayyuka na Karamar Hukumar Katsina, Hon. Engr. Abubakar Jafaru, tare da sauran manyan baki da al’umma da dama.

Zaharaddeen Muazu Rafindadi
Sakataren yada Labarai na Shugaban Karamar Hukumar Katsina.

11.04.26

SANARWA!!!SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA TALLAFAWA AL’UMMAR TUDUN YAN LIHIDDA DA  NAIRA MILIYAN DAYA DON GYARAN TAR...
12/04/2026

SANARWA!!!

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA TALLAFAWA AL’UMMAR TUDUN YAN LIHIDDA DA NAIRA MILIYAN DAYA DON GYARAN TARANSFOMAR DAKE SAMAR DA WUTAR LANTARKI.

Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya amince da kashe miliyan ɗaya (₦1,000,000) don gyara wata transformer na wutar lantarki da ya lalace a Tudun Yan Lihidda, Zone C, kusa da unguwar Kofar Soro.

Wannan transformer ya kasance ba ya aiki kusan shekara guda, wanda ya bar mazauna yankin cikin duhu ba tare da wutar lantarki ba, hakan ya shafi ayyukan yau da kullum na al’ummar wannan yanki.

Bayan korafin da al’ummar wurin s**a yi a hukumance, Gwamnatin Karamar Hukumar ta yi saurin shiga don magance matsalar.

Kansila da ke wakiltar mazabar Wakilin Arewa B, Hon. Ibrahim Bello Giwa, ya gabatar da kuɗin a madadin Shugaban ga Injiniya Murtala, wanda ke kula da aikin gyaran taransfomar. Ya ba da tabbacin cewa za a aiwatar da aikin cikin gaggawa da kuma inganci don samar da Maganin matsalar.

Wannan mataki na nuna sadaukarwar shugaban Karamar Hukumar wajen gudanar da mulki mai kyau da kuma himmatuwa wajen magance bukatun al’umma kai tsaye. Duk da ƙarancin kuɗin da karamar hukumar ke fuskanta a halin yanzu, shugaban na ci gaba da ba da fifiko ga ayyukan da ke amfanar da al’umma kai tsaye.

Mazauna Tudun Yan Lifidda sun nuna godiyar su ta gaske game da ansa bukatar su cikin saurin, tare da yaba wa shugaban akan sauran ayyukan alkairi da ya zuba masu a wannan mazaba da kuma sadaukarwarsa ga jin dadin al’ummar karamar hukuma Katsina baki daya

ISAH MIQDAD PROJECT PROMOTERS ✍🏻
12 April, 2026

Address

Katsina Local Government Council
Katsina
820101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Isah Miqdad Project Promoters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share