24/05/2026
FIYE DA MUTUM 4,000 SUN AMFANA DA TALLAFIN SHINKAFA DA KUDIN CEFA’NE NA SALLAH DA ALHAJI DAUDA KAHUTU RARARA YA RABA A GARIN KAHUTU
A wani gagarumin shirin tallafa wa al’umma gabanin shagalin Sallah, fiye da mutum dubu huɗu ne s**a ci gajiyar tallafin shinkafa da kuma kuɗin cefane naira dubu biyu-biyu da Sarkin Waka na Kasar Hausa, Alhaji Dauda Kahutu Rarara, ya raba a garin Kahutu da ke Karamar Hukumar Danja.
Tallafin ya haɗa da buhunan shinkafa tare da kuɗin cefane, wanda aka bayyana cewa an tsara shi ne domin rage wa jama’a raɗaɗin rayuwa tare da tabbatar da cewa suna gudanar da bukukuwan Sallah cikin walwala da jin daɗi.
Wannan tallafi dai ya zo a wani lokaci da jama’a ke fuskantar ƙalubalen rayuwa, inda aka ce zai taimaka matuƙa wajen rage wahalhalu musamman ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
Al’ummar Karamar Hukumar Danja sun bayyana jin daɗi da godiya bisa wannan taimako, inda s**a ce irin wannan ɗaukar nauyi da nuna tausayi na ƙara ƙarfafa dankon zumunci tsakanin shugabanni da talakawa.
Bayan kammala rabon tallafin, Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya yi kira ga masu hali da arziki da su riƙa taimaka wa mabukata, musamman a irin wannan lokaci na bukukuwa da jama’a ke buƙatar tallafi fiye da kowane lokaci.
Daga Mubarak Dabai