13/11/2025
DAƊUMI-ƊUMI: Sanatoci A Najeriya Sun Amince Wa Sugaban Ƙasa Tinubu Ya Ciwo Bashin Naira Tiriliyan 1.15
Majalissar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ciwo bashin Naira tiriliyan 1.15 a cikin gida domin ciki giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025.
Amincewar ta biyo bayan karɓar rahoton kwamitin majalisar kan basussukan cikin gida da na ƙasashen waje a zaman majalisar da aka gudanar ranar Laraba, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Kwamitin ya bayyana cewa Dokar Kasafin Kuɗi ta 2025 ta tanadi jimillar kashe kuɗi har Naira tiriliyan 59.99, wanda ya ƙaru da Naira tiriliyan 5.25 daga Naira tiriliyan 54.74 da Fadar Shugaban Ƙasa ta gabatar tun farko.
Me zaku ce?
KanemTrade find it and take it