Giwa TV

Giwa TV Kafar Zamani Domin Shiri Kai Tsaye, Labarai da Rahotanni, Karatun Addini da Tallace Tallace Kana mu Nishadantar da Masu Bibiyan Shafukan mu na Yanar Gizo.

Zaku iya Samun mu a 08064418179. Mungode!!!

*MESSAGE FROM THE PALACE OF HIS EMINENCE, THE SULTAN OF SOKOTO*Asalamu alaykum to the muslim ummah. We want whoever gets...
10/06/2026

*MESSAGE FROM THE PALACE OF HIS EMINENCE, THE SULTAN OF SOKOTO*

Asalamu alaykum to the muslim ummah. We want whoever gets this message should please help to share to every muslim.

We are encouraged to wake up in the night and do two Rakaat Nafila.

*In the first Rakaat, recite ‘Sura Fatiha and Suratul Masad 3x’
*second rakaat, Suratul Fatiha, and this verse ‘Wamakaru makaran wallahu khairul makirin 7x’ with the following intention:

‘whoever has a hand in this crisis caused by BOKO HARAM, kidnapping and banditry’

May ALLAH SWT destroy all of them just exactly the way HE destroyed Fir'auna and his army.

Whoever receives and read this message should kindly share to every muslim.

May ALLAH SWT reward you abundantly

*PLEASE SHARE*

10/06/2026
HOTUNA: Yadda aka wayi gari da mummunar ambaliyar ruwa a garin Bara, karamar hukumar Kirfi ta jihar Bauchi.Rahotanni sun...
10/06/2026

HOTUNA: Yadda aka wayi gari da mummunar ambaliyar ruwa a garin Bara, karamar hukumar Kirfi ta jihar Bauchi.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ibtila’i ya yi sanadiyyar rasuwar Aishatu Sagir da jikarta Rahama Sagir, tare da rugujewar gidaje, asarar dabbobi da dukiyoyin al’umma masu tarin yawa.

📷: Hon. Muhammad Bashir Bara
Dan Galadiman Bara

09/06/2026

Majalisar Wakilai a Najeriya ta bukaci Babban Mai Bai wa Shugaba Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu da dukkan hafsoshin tsaro har ma ministan tsaro da su gurfana a zauren majalisar domin amsa tambayoyi kan tsaron kasa.

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allah ya yi wa Malam Yahaya Billi rasuwa a hannun kidnap...
09/06/2026

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allah ya yi wa Malam Yahaya Billi rasuwa a hannun kidnappers a jiya, sun tabbatar da Kashe shi bisa sharadin da S**a saka aka kasa cikawa.😭

Don haka za a gabatar da salatul Ga'ib a yau kamar haka, Wuri: Garkan Sarki, Lokaci: 4:30, ALLAH ya Jaddada rahama a gare shi.

Ya ALLAH ka kawo mana karshen Matsalar tsaro a Nigeria 😭🙏

Usman Ibrahim Kobie

PRP a Kan SiraɗiA siyasa, tarihi babban Malami ne, kuma abun kiyayewa. Duk jam'iyyar da ta kasa koyon darasi daga abin d...
09/06/2026

PRP a Kan Siraɗi

A siyasa, tarihi babban Malami ne, kuma abun kiyayewa. Duk jam'iyyar da ta kasa koyon darasi daga abin da ya faru da wasu jam'iyu, sau da yawa kan tsinci kanta tana maimaita irin kura-kuran da ta daɗe tana s**a. Hausawa na cewa, "wanda bai ji bari ba, zai ji hoho." Haka kuma ana cewa, "idan kura ta yi murna da rashin wutsiyar kare, ya kamata ta tuna ita ma ba ta da tata."

Kamar yadda kowa ya sani, jam'iyyar PRP a jahar Bauchi ta samu sabon ƙarfi da karsashi bayan shigowar Sanata Shehu Buba cikin jam'iyyar. Wannan sauyin sheƙa ya jawo hankalin jama'a da dama, ya kuma sanya mutane da yawa s**a fara kallon PRP a matsayin wata sabuwar mafita ga masu neman siyasar adalci da gaskiya a jahar Bauchi.

Sanata Shehu Buba ba baƙo ba ne a siyasar jahar Bauchi. A matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan APC, ya taka muhimmiyar rawa wajen gina jam'iyyar da faɗaɗa tasirinta a faɗin jahar. Duk da haka, kamar yadda ya bayyana a lokacin ficewarsa, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake tafiyar da wasu al'amura a cikin jam'iyyar, musamman abin da ya ɗauka a matsayin rashin adalci da zalunci a wasu matakai na siyasa.

Shigowarsa PRP ya ba wa jam'iyyar dama ta musamman a kakar wannan zaɓe. Wasu ma suna ganin kamar an yayyafa wa bishiyar da ta kusa bushewa ruwa ne, ta sake fito da sabbin ganye. Hakan ya sa PRP ta zama mafakar wasu ƴan siyasa da s**a yi gudun hijira saboda zaluncin jam'iyyu da s**a baro.

Sai dai tambayar da ke gaban kowa a yau ita ce: shin PRP za ta kasance daban da jam'iyu da take s**a? Ko kuwa za ta faɗa cikin ramin da wasu jam'iyu s**a faɗa a baya?

A siyasa, babu abin da ke gina jam'iyya kamar adalci, kuma babu abin da ke rusa ta kamar son zuciya da zalunci. Lokacin da mambobi s**a fara jin cewa ba ƙa'ida ce ke aiki ba, sai dai kusanci, fifiko, alfarma ko son zuciya, tasirin jam'iya kan fara disashewa. Kuma idan karsashin jam'iya ya fara rauni, to makomar jam'iyya kan shiga haɗari.

Darasin da APC ta bari a Bauchi ya kamata ya zama abin koyi ga duk wata jam'iyya. Duk abin da ya haddasa ficewar manyan jiga-jigai da magoya baya daga cikinta, ya kamata ya zama darasi ga PRP wajen kauce wa maimaita irin waɗannan kura-kurai. Domin babu hikima mutum ya gudu daga abin da yake zargi na zalunci, sannan ya sake ginawa a sabon gidansa.

Idan har da gaske PRP tana son zama madadin jam'iyar APC ko ADC da ƴan takara da jama'a ke nema, to wajibi ne ta tabbatar da cewa tsarin zaɓen ƴan takararta ya kasance a bayyane, cikin gaskiya, adalci da bin ƙa'ida. Domin adalci ba magana ba ne kawai a baki ba, aiki ne da ake gani a aikace. Kuma shugabanci nagari ba auna shi ake yi da jawabi ba, ana auna shi ne da yadda ake mu'amala da mutane lokacin da ake yanke hukunci. Sannan duk wadda ya bayyana, duniya ta shaida ya lashe zaɓen fitarda ƴan takara, to adalci shi ne a bar masa nasararsa. Sannan a sake duba maslaha da mafitar jam'iya, shin wannan ɗan takara da ya lashe zaɓen, yana da jama'a da zasu iya kawo nasara wa jam'iyyar a kujerarsa, idan yana da ƙarfin cin zaɓe, jam'iya tayi wa kanta gata, ta bar masa kayansa.

A yau, PRP tana tsaye ne a wani mahadar hanya mai muhimmanci. Hanyar farko ita ce ta adalci, gaskiya da mutunta haƙƙin kowa, wadda za ta iya ƙara mata karɓuwa da amincewar jama'a. Hanya ta biyu kuwa ita ce ta son rai da alfarma, wadda tarihin siyasa ya nuna cewa sau da yawa suna kai jam'iyyu ga rarrabuwar kai da koma baya ko rugujewa.

Saboda haka, wannan ba s**a ba ne, kuma ba adawa ba ce. Tunatarwa ce ga shugabannin jam'iyyar da duk masu ruwa da tsaki cewa siyasa tana ginuwa ne da adalci. Duk jam'iyyar da ta rungumi adalci, mutane za su rungume ta. Amma duk jam'iyyar da ta rungumi son rai, ko da tana da ƙarfi a yau, tana iya fuskantar ƙalubalen da zai raunana ta gobe.

Tambayar da ke gaban PRP a yau ita ce: shin za ta zama abin koyi wajen gyara kura-kuran da wasu jam'iyu s**a yi, ko kuwa za ta maimaita tarihin da ita kanta ta yi amfani da shi wajen samun karɓuwa?

Lokaci ne kaɗai zai bayar da amsa. Amma abu ɗaya a bayyane yake, adalci shi ne ginshiƙin nasarar kowace jam'iyya, haka kuma rashin adalci shi ne farkon tushen rugujewar kowace jam'iya duk ƙarfinta.

Ismail Misau
Litinin, 8 ga Yuni, 2026

Headline: Governor Bala Mohammed Appoints Dr. Muhammad  Mujitaba Abdulkadir  as Provost of A.D. Rufai College of Educati...
08/06/2026

Headline: Governor Bala Mohammed Appoints Dr. Muhammad Mujitaba Abdulkadir as Provost of A.D. Rufai College of Education, Legal and General Studies, Misau.
Further details will be announced soon.

PRESS RELEASE8th June 2026  APC Leadership and the Federal Government Sen. Shehu Buba Umar Explains Defection to PRP, Re...
08/06/2026

PRESS RELEASE
8th June 2026

APC Leadership and the Federal Government

Sen. Shehu Buba Umar Explains Defection to PRP, Reaffirms Respect for APC Leadership

Sen. Shehu Buba Umar, representing Bauchi South Senatorial District and PRP governorship candidate for 2027, has clarified the reasons for his defection from the All Progressives Congress (APC) to the People’s Redemption Party (PRP) In an occasion with his supporters, defectors from Alkaleri/ Kirfi federal constituency.

Sen. Buba said the decision was based on principle, internal democracy, and the need to provide quality leadership for Bauchi State. Speaking at a meeting with supporters and stakeholders, he stated that his exit from the APC was not driven by personal grievances but by concerns over the party’s governorship candidate selection process.

“The emergence of a governorship candidate imposed by a few Abuja-based actors, without adequate consultation with stakeholders, party leaders, and grassroots members, undermined democratic principles,” Sen. Buba said. “We were confronted with individuals whose influence exists largely on paper, not through genuine grassroots engagement. That left many committed members with no alternative but to seek a more democratic platform.”

Following consultations with community leaders, youth and women groups, and political associates across Bauchi State, Sen. Buba joined the PRP to pursue what he described as “purposeful leadership” in the 2027 governorship election.

Despite the defection, he said he maintains cordial relations with APC leadership at both national and state levels, and a healthy working relationship with the Federal Government as a serving senator.

“Politics should not be about hostility or personal attacks. It should be about service, ideas, and development,” he said. “We have great respect for APC leaders and executives from the national level to the state level.”

Sen. Buba added that his movement is not engaged in aggressive recruitment but welcomes citizens who share its vision for good governance, transparency, economic development, youth empowerment, and improved welfare.

“We are not forcing anyone to join us. We welcome all individuals who believe in our political philosophy and commitment to building a better future for Bauchi State,” he said.

He also urged the public to disregard rumors of hostility between APC and PRP members, noting that “politics is not war” and personal relationships should outlast elections.

Sen. Buba reminded political actors that the official campaign period for 2027 has not commenced and called for peaceful, issue-based engagement.

“I call on members of APC, PRP, and all other parties to conduct their activities with maturity, tolerance, and respect for democratic principles. Elections come and go, but life continues afterward, by the grace of Allah,” he said.

He reaffirmed his commitment to serving Bauchi South and pledged to continue statewide consultations ahead of the 2027 elections.
Signed

Comrade Sabo Mohammed
Adviser on Media and Communications
Office of Sen. Shehu Buba Umar
Bauchi South Senatorial District | PRP Governorship Aspirant, Bauchi State.

Labarin Shehu Jaha da Dansa da JakinsuWata rana Shehu Jaha da dansa s**a fito suna tafiya, suna tafe a kasa yayin da jak...
07/06/2026

Labarin Shehu Jaha da Dansa da Jakinsu

Wata rana Shehu Jaha da dansa s**a fito suna tafiya, suna tafe a kasa yayin da jakinsu yake bin su a baya babu kowa a kansa. Ganin haka, mutane s**a fara yi musu dariya suna cewa, "Duba wawayen nan, ga jaki a gefensu amma suna wahalar da kansu suna tafiya a kasa!" Jin haka, Jaha ya dakata, ya sa dansa ya hau kan jakin, shi kuma ya ci gaba da takawa a kasa.

Ba su yi nisa ba, sai s**a wuce ta gaban wasu mutane daban. Nan take wadannan mutanen s**a fara kushe su, suna cewa, "Duba wannan yaro mara tarbiyya, shi yana kan jaki yana morewa, amma ya bar tsoho mahaifinsa yana shan wahala a kasa." Jin wannan magana ta dame su, sai Jaha ya ce dansa ya sauka, shi kuma ya hau kan jakin don ya nuna cewa shi ne ya kamata ya huta.

Suna cikin tafiya haka, sai wasu mutanen s**a sake ganinsu s**a ce, "Wannan tsoho bai da tausayi ko kadan! Shi yana zaune daram a kan jaki, amma ya bar karamin yaro yana gudu a kasa cikin wannan zafi." Domin su gyara wannan matsalar, Jaha ya jawo dansa s**a hau kan jakin su duka biyun. Amma maimakon mutane su yaba, sai s**a fara fadin cewa, "Wadannan mutane ba su da imani, kalli yadda s**a danne wannan karamin jakin da nauyinsu, ai sai ku kashe shi za su yi ai".

Daga karshe, ganin cewa kowane mataki s**a dauka sai mutane sun soki lamirinsu, Shehu Jaha ya juyo wurin dansa ya ba shi babban darasin rayuwa. Ya ce masa, "Ka gani ko? Idan ka biye wa maganar mutane, ba za ka taba yin abin da zai faranta musu rai duka ba. Don haka, ka yi abin da ka san shi ne daidai, ka bar su su fadi abin da za su fada."
Giwa TV

ℹ YADDA AKEYIN SALLAH DAREDole ne mutum ya tsarkake niyyan sa, sannan sallah dare anfi so ayishi ne a farkon dare, ko ƙa...
07/06/2026

ℹ YADDA AKEYIN SALLAH DARE

Dole ne mutum ya tsarkake niyyan sa, sannan sallah dare anfi so ayishi ne a farkon dare, ko ƙarshen dare, ba tsakiyan dare ba, kokuma mutum ya cinye daren gaba ɗaya, ma'ana daga ɗayan dare har 4:30am na dare, shine ka cinye daren gaba ɗaya!

1) Akwai buƙatan ka tsarkake zuciyarka da kuma kaya na musamman domin wannan sallah daren, idan kuma baka da kayan sallah dare, to kayan da zaka yi sallah dare dashi ka wanke shi idan da hali har turare kayi masa kafin lokacin sallah yayi.

2) Akwai buƙatan ka watsa ruwa (wanka). Kayi wanka a bisa sunnah, ma'ana babu samulu ko soso, sannan kuma lokacin da kake wankan kayita tuna kanayin wannan wankanne saboda kusantar ubangijinka mai tsarki da son tsabta!

3) Akwai buƙatan Alwala da nitsuwa da maida hankali yadda yadace, saboda Manzon Allah (SAW) yace duk wanda yakeson nitsuwa cikin sallar sa to yayi Alwala da nitsuwa da maida hankali, tabbas sallah zata samu nitsuwa da maida hankali. Ma'ana idan kana farillah ka gane farillah kakeyi, idan kana sunnah ma kagane sunnah kakeyi, haka mustahabbi.

4) Akwai buƙatan idan kazo ka ƙabbarta ka fara tuna sheɗan zaizo ya ɓata maka sallah, saboda babu inda sheɗan yafi ziyarar zukatan bayan Allah kamar lokacin da yaga zasuyi sallah kokuma suna sallah, saboda yasan sallah itace babban ibada kuma mafi Alkhairi ga rayuwar ɗan Adam. Kaikuma kayi sallar ka cikin tuna Allah da lahira (Ƙiyama).

5) Zaka iya Addu'a cikin sujudan ka, kuma kada ka takura kanka da raka'oi masu yawa, kayi abinda zaka iya, idan kuma zaka ɗaga hanu cikin sallah kokuma bayan sallah to kafara da Addu'oi da Alqur'ani yakawo wanda s**a fara da Rabbana, Rabbana, sannan kuma ka farayiwa kanka addu'a, sai iyayenka, sai Al'ummah musulmai, kuma daga ƙarshe kada ka manta kayiwa Annabi Muhammad (SAW) salati Ibrahimiyyah, kuma kada ka shafa, saboda Manzon Allah baya shafawa kamar yadda mutane sukeyi. Kawai idan ka gama saika sauƙe hannayenka!

Giwa TV

Address

Sabon Layi Street Misau
Misau

Telephone

+2348064418179

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Giwa TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Giwa TV:

Share