15/08/2025
Assalamu Alaikum Warahmatullah
Zan Kare Gaskiya Koda Zata Jefa Ni Cikin Kiyayya."
Na zabi tsayawa da gaskiya – ba don ana sona ba, sai don ni ba na son kaina in zama abin kunya a gaban Allah.
Ana iya tsanani. Ana iya jifani da kalmomi. Ana iya kira na da mahaukaci.
Amma ba zan bar hanyar da ta fi kyau saboda hanyar da tafi sauki ba.
Ku ce min masoyi bane, ku ce min mai wata manufa ce, ku ce min ina neman suna… amma ku kasa cewa: ban faɗi gaskiya ba.
Ina so in mutu da laifin faɗin gaskiya, fiye da in rayu da jin daɗin riƙe karya.
Domin makomata a gaban Mahalicci Na take – ba a gaban mabiyanka ba.
KaiGaskiya – ba abu ne mai sauki ba. Amma kai ne aka kira.
-duniya -amutsa .