09/06/2026
A karo na tara (09) Maulana Sheikh Malam Babangida lauzra zai kara jagorantar mauldin nan da da'irar La'uzra ta saba shiryawa insha Allah. A ranar ta yau (Talata) 1 ga watan muharram ne za'a gabatar da wannan babban taro a sabon titin dandago Gidan Kankara kusa da makarantar Abu Hanifa kan titin Gwarzo.
Duk wanda yaga wannan sanarwa ana gayyatar sa sannan ya sanar da wanda bai gani ba.
Bakin mu da zasu taso daga nesa Allah ya kawo mana su lafiya ya sa a fara a gama Lafiya Amin.