09/11/2025
GWAGWARMAYAR SHEKARU 20s
A cikin shekarunka na Ashirin (20s), duniya ta rataya maka nauyin buri mai yawa: Neman aiki, tara dukiya, ɗaukar nauyin iyali, har ma da daukar nauyin iyaye completely. Wannan matsi ne mai girma.
Amma gaskiyar rayuwa ita ce, mafi yawan samari suna shan azaba a ɓoye. Babu mai damuwa da gumi da hawaye da kake zubawa; abin da suke jira kawai shine nasara a fili. Don haka, ka daina neman yabo.
Ka mai da hankali kan aikinka. Ka ci gaba da ƙoƙari koda babu mai tafa maka. Ka koyi dabarar faɗa da rayuwa har sai ka karɓi abin da kake buƙata.
Hanyar zuwa nasara ba a shimfiɗa ta da furanni ba. Ka bar tsananin ta ya gina ƙashin bayan ka (forge you), kar ya ruguza ka. Ka zama irin mutumin da ke bunƙasa a ƙarƙashin matsi, ya mai da ciwo zuwa gadon tarihi, kuma ya haifar da girma a cikin hargitsi.
Ka yi aiki tukuru. Ka kasance mai imani. Nasararka tana jiranka in sha Allah.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️