Mainas Livestock Production And Marketing Ltd

Mainas Livestock Production And Marketing Ltd Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mainas Livestock Production And Marketing Ltd, Unguwa Uku Yan Awaki Kafin Masallacin Daurawa Na Sallar Jumaat, Birnin-Kebbi.
(2)

Veterinary Doctor
Agribusiness Entrepreneur
Livestock Farm Consultant
Content Creator About livestock
Contact Us:09133372408
Tiktok page:https://www.tiktok.com/?_r=1&_t=ZS-94iAi1oG666

Barkanmu Da Yammaci Masoya Wannan Sahfin Mai Albarka Ina Muku Fatar Alkhairi.
04/08/2026

Barkanmu Da Yammaci Masoya Wannan Sahfin Mai Albarka Ina Muku Fatar Alkhairi.

🎉 Happy Birthday to Me! 🎂Today, I celebrate another year of God's faithfulness, grace, and mercy. I am grateful for the ...
04/08/2026

🎉 Happy Birthday to Me! 🎂

Today, I celebrate another year of God's faithfulness, grace, and mercy. I am grateful for the gift of life, good health, and every lesson along the journey.

May this new chapter bring greater opportunities, success, peace, and abundant blessings.

Cheers to new beginnings and a brighter future! 🥳🎈

Munada zabi guda 250 yan wata 1 ga mai buqata location kano.Muna turawa zuwa wasu jihohin.Contact Us 09133372408
03/08/2026

Munada zabi guda 250 yan wata 1 ga mai buqata location kano.

Muna turawa zuwa wasu jihohin.

Contact Us 09133372408

Yadda Za Ka Yi Nasara Fiye da Yadda Ka Ke Tsammani a Kiwon Kajin Gida da TalotaloIdan kana son samun nasara a harkar kiw...
01/08/2026

Yadda Za Ka Yi Nasara Fiye da Yadda Ka Ke Tsammani a Kiwon Kajin Gida da Talotalo

Idan kana son samun nasara a harkar kiwon kajin gida da talotalo, ka fara da samun ilimi. Kafin ka sayi ko da ɗan tsuntsu guda, ya kamata ka san yadda ake kula da shi tun daga ranar farko. A fannin kiwo, kulawa ita ce ginshiƙin nasara.

Na biyu, ka guji sayen kaji daga kasuwannin ƙauye ba tare da bincike ba. A mafi yawan lokuta, wasu suna kai kaji kasuwa ne saboda matsaloli ko asara da s**a samu. Maimakon haka, ka nemi amintattun masu kiwo a unguwarku. Idan ka samu mutane kusan 10 masu kiwon kajin gida, ka nemi su sayar maka da 'ya'yan kajinsu bayan sun yi ƙyanƙyashe. Ka raini su tun suna ƙanana har su girma.

Har ila yau, kada ka dogara gaba ɗaya da magungunan zamani. Ka fi mayar da hankali kan rigakafi da kyakkyawar kulawa. Haka kuma, ka koyi amfani da wasu hanyoyin gargajiya masu amfani da aka tabbatar da ingancinsu, sannan ka yi amfani da magungunan zamani idan akwai buƙata kuma bisa shawarar ƙwararre.

Kafin ka fara kiwo, ka tabbata kana da isasshen ilimi da kuma tsarin kasuwanci. Duk wata sana'a tana buƙatar tsari da shiri domin a samu riba mai ɗorewa.

A wannan lokacin na tsadar rayuwa, idan kana son rage kuɗin kiwo, yana da kyau ka koyi sarrafa wasu abincin kaji da kuma wasu kayan tallafin kiwo da kanka ta hanyar amfani da albarkatun gonarka, muddin an yi hakan bisa ingantattun hanyoyi.

Babban amfanin sayen 'ya'yan kaji tun suna ƙanana shi ne idan ka ba su kulawa mai kyau, kana da babban damar samun manyan kaji masu ƙarfi, lafiya da inganci.

A ƙarshe, kafin ka fara wannan sana'a, ka zauna ka yi tunani sosai, ka tsara yadda za ka gudanar da ita, sannan ka fara cikin shiri.

Zan ci gaba da kawo muku irin waɗannan shawarwari masu amfani. Ku yi sharing domin sauran manoma su amfana.

📚 Kada ku manta, muna sayar da littattafan kiwon dabbobi da kaji cikin harshen Hausa (PDF).

📱 WhatsApp: 09133372408






Maganin Farin Kashi Da Kara Lafiya Ga Tsuntsaye Sannan Yana Maganin Coccidiosis.
17/07/2026

Maganin Farin Kashi Da Kara Lafiya Ga Tsuntsaye Sannan Yana Maganin Coccidiosis.

ABUBUWAN DA ZA MU KOYAR A CIKIN WANNAN HORON SUNE:Gabatarwa kan kiwon kajin gida da talotalo.Zaɓen irin kaji da talotalo...
12/07/2026

ABUBUWAN DA ZA MU KOYAR A CIKIN WANNAN HORON SUNE:

Gabatarwa kan kiwon kajin gida da talotalo.

Zaɓen irin kaji da talotalo masu inganci.

Gina muhalli da dakin kiwo da ya dace.

Brooding (kula da ƙananan kaji da talotalo).

Ciyarwa da tsarin abinci daga farko har zuwa girma.

Kula da Lafiya da rigakafin cututtuka.

Tsaron gona kiwo (Biosecurity).

Gane alamomin cututtuka da hanyoyin magance su.

Tsarin allurar rigakafi (Vaccination Schedule).

Kula da ƙwai da hanyoyin kyankyasa (Natural & Incubator Hatching).

Zaɓen kaji iyaye masu kyau (Breeding Stock Selection).

Hanyoyin rage mace-macen kaji da talotalo.

Tsarin kula da kaji daga ƙanana zuwa manya.

Dabarun samun riba daga kiwon kajin gida da talotalo.

Yadda ake kasuwanci da tallata kaji da ƙwai.

Tambayoyi da amsoshi kan matsalolin mahalarta.

TSARIN KOYARWA

📝 Darussa a rubuce.

🎤 Voice Notes.

📲 Horon zai gudana ne a Telegram Group.

❓ Za a ba mahalarta damar yin tambayoyi kai tsaye tare da samun amsa.

✅️.Zan Bada Training Akan Kiwon Kajin Gida Da Talotalo Yadda Zaa Magance Matsalolin Su Na Kwana 3.Masu Buqatar Shiga Kud...
10/07/2026

✅️.Zan Bada Training Akan Kiwon Kajin Gida Da Talotalo Yadda Zaa Magance Matsalolin Su Na Kwana 3.

Masu Buqatar Shiga Kudin Shiga #1000

Biya Kudin Kawai Zakayi Ka Tura Mana Shedar Biya A WhatsApp

Acc Name Sifiyanu Idris Shanga
Acc No 0705252071
Gt Bank

WhatsApp 09133372408.

Akwai Wasu Training Da Muka Fara Muka Dakatar To Kuyi Hakuri Akwai Dalili Amma An Kusa Cigaba Daga Inda Aka Tsaya In Sha Allah.

✅️Abubuwan Da Suke Hana Kaji Yin Kwai Ko Talotalo.✔️. Zafi Yana Haifar Da Dakatar Da Yin Kwai Ga Kaji Ko Kuma Karancin Y...
10/07/2026

✅️Abubuwan Da Suke Hana Kaji Yin Kwai Ko Talotalo.

✔️. Zafi Yana Haifar Da Dakatar Da Yin Kwai Ga Kaji Ko Kuma Karancin Yin Kwain,

✔️.Yawan Takurawa Kaji Yana Haifar Da Rashin Kwanciyar Hankali Wanda Hakan Yake Haifar Da Rashin Yin Kwain,

✔️.Cunkoso Yana Haifar Da Damuwa Ga Kaji Wanda Yake Hana Su Tsayawa Suyi Kwai,

✔️.Rashin Ingantaccen Abinci Yana Haifar Da Rashin Yin Kwai Ga Kaji.

✔️.Rashin Isasshen Sinadarin Calcium Yana Haifar Da Karancin Yin Kwai,Shan Kwai,Rashin Kwarin Jiki,

✔️.Rashin Muhalli Mai wadataccen Iska Yana Haifar Da Matsalar Numfashi,mura,tari,atishawa,sanyi da zai iya dakatar da kaji daga yin kwai,

✔️.Cutar kare dangi wato (Newcastle Disease) tana haifar da alamomi da yawa ajikin kaji da yake hana su yin kwai,

✔️.Rashin Ingantaccen Ruwan Sha Mai Tsafta Ga Kaji Yana Haifar Da Cututtuka Da Zasu Iya Hana Kajin Yin Kwai.

✔️.Kwari wato(Lice) da suke jikin kaji s**an Tsotse jinin su ne a hankali wanda hakan yana hana kaji sukunin da zasu iya tsayawa suyi kwai.

✔️.Rashin Tsaftar Muhalli Yana Kawo Cututtukan Dake Hana Kaji Yin Kwai,

Duk Lokacin Da Ka Sayo Tsuntsaye Ka Fara Tsayawa Ka Duba Wadannan Abubuwan Da Idon Basira Domin Tabbatar Da Baka Yi Asarar Kudin Ka Ba.

Allah Yasa Mu Dace Acikin Kasuwancinmu.

Masu Buqatar Ilimin Kiwon Kaji Munada Littafan Da Muka Rubuta Da Hausa Muna Sayarwa #3500 Kacal,Kuma A Wayarka Nan Take Zaa Tura Maka Idan Ka Saya

Mai Buqata Ga WhatsApp Lamba (09133372408).

Address

Unguwa Uku Yan Awaki Kafin Masallacin Daurawa Na Sallar Jumaat
Birnin-Kebbi

Telephone

+2349133372408

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mainas Livestock Production And Marketing Ltd posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mainas Livestock Production And Marketing Ltd:

Shortcuts

Share