Ztech Interface Solution Academic

Website

Ztech Interface Solution Academic Makarantar tana bayar da horo mai inganci a kan amfani da kwamfuta, programming, graphic desig

ZTECH Interface Solutions Academy makaranta ce ta zamani da aka kafa domin koyar da ilimin kwamfuta (computer) ga ɗalibai da masu sha’awa a fannoni daban-daban.

16/08/2026

Ba sai ka jira aikin gwamnati ba.
Ba sai ka jira wani ya zo ya taimake ka ba.

Wani lokaci, skill ɗaya ne kawai ya rage maka ka fara canza rayuwarka.

A yau duniya tana tafiya ne da DIGITAL SKILLS

Computer
Microsoft Word
Excel
Graphic Design
Data Protection
👉 Cybersecurity
👉 Artificial Intelligence (AI)
👉 Online Research & Digital Literacy

A ZTECH INTERFACE SOLUTIONS ACADEMIC, muna taimaka wa matasa su koyi skills masu amfani da za su iya amfani da su wajen karatu, aiki da kasuwanci.

Tambaya gare ka:

Idan aka baka damar koyon skill guda ɗaya kyauta yau, wanne zaka zaɓa? 👇

Rubuta amsarka a Comment 👇
Kuma SHARE wannan post ɗin—wataƙila mutum ɗaya da ka tura masa zai samu dalilin fara koyon skill da zai canza rayuwarsa.

ZTECH INTERFACE SOLUTIONS ACADEMIC
Learn • Practice • Improve • Succeed

Hukumar Alhazai Ta Ƙasa Ta Sanar Da Kuɗin Hajjin Shekarar 2027 Na Yanki-YankiHukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar d...
14/08/2026

Hukumar Alhazai Ta Ƙasa Ta Sanar Da Kuɗin Hajjin Shekarar 2027 Na Yanki-Yanki

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da kudin aikin Hajjin shekarar 2027 da Gwamnatin Tarayya ta amince da su.

An kayade wadannan kudade ne bayan tattaunawa da shugabannin Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi, da manyan ma'aikata masu bada shawara a Masarautar Saudiyya, da kuma duba yanayin canjin kudi da tsadar aiyuka.

Ga kudaden aikin Hajjin 2027 da aka amince da su dangane da yankunan tashi:Yankin Maiduguri / Yola: ₦7,560,822.00Yankin Arewa (Northern Zone): ₦7,672,822.00Yankin Kudu (Southern Zone): ₦7,882,822.00

Ga masu niyyar tafiya waɗanda s**a riga s**a biya ajiya ta ₦5,000,000.00 ana buƙatarsu da su cika sauran kuɗaɗen da s**a rage domin kammala rajista.

Sabbin masu rajista kuma su garzaya su biya kudadensu ta Hukumomin Alhazan Jihohinsu, ko kuma ta bankunan da ke cikin tsarin gajiyar ajiya na Hajj Savings Scheme (HSS).

Dangane da umarni mai tsauri daga Ma'aikatar Hajj da Umrah ta kasar Saudiyya, NAHCON ta sanya 26 ga watan Satumba, 2026 a matsayin ranar karshe ta tura bayanan tantance mutane (biometric data) na masu niyyar tafiya a dandalin intanet na Nusuk-Masar.

Haka kuma, dole ne jihohi su kammala tura dukkan kudaden aikin Hajjin 2027 kafin 2 ga watan Disamba, 2026. Ba za a kara lokaci ba bayan wadannan kwanaki, domin tsara bayani da rabon kujeru ya dogara ne kacokan kan tura kudi akan lokaci.

Hukumar na jaddada cewa rashin cika wadannan sharudda akan lokaci zai haifar da rashin samun kujerar aikin Hajji da aka ware wa mutum.

INTERNATIONAL YOUTH DAY(RANAR MATASA TA DUNIYA)A yau, Ranar Matasa ta Duniya, ya kamata mu tuna cewa matasa ba wai su ne...
12/08/2026

INTERNATIONAL YOUTH DAY
(RANAR MATASA TA DUNIYA)

A yau, Ranar Matasa ta Duniya, ya kamata mu tuna cewa matasa ba wai su ne shugabannin gobe kawai ba — su ne ginshiƙin yau. 💪🏽🌍

A Afirka, matasa suna da basira, ƙwazo da manyan mafarkai, amma rashin aikin yi, ƙarancin jari da rashin damar samun ingantaccen horo na hana da dama cimma burinsu.

Ya kamata gwamnati, ’yan kasuwa da al’umma su ƙara saka jari a matasa ta hanyar ilimi, sana’o’i, fasaha, tallafin jari da samar da guraben aiki.

Matashi da aka ba dama yau, zai iya zama ɗan kasuwa, ma’aikaci ko jagoran da zai taimaka wajen gina ƙasa gobe.

Ranar Matasa ta Duniya ta zama ranar tunatarwa cewa:

kada mu raina matasa, kada mu watsar da su, kuma kada mu kashe musu mafarki.

Mu ba su dama su nuna abin da za su iya.

🇳🇬❤️
Happy International Youth Day! 🎉
Matasa su ne ƙarfin al’umma, idan aka ba su dama za su iya canza duniya. 🌍🔥

12/08/2026

🕊️ MU CETO AREWA, MU ZAUNA LAFIYA 🕊️

Arewa tamkar gida ce da muka gada daga kakanninmu. A cikin wannan gida akwai Musulmai da Kiristoci, Manoma da Makiyaya, Hausawa da Fulani da sauran kabilu. Bambancinmu bai kamata ya zama dalilin kiyayya ba.

Mu daina kallon juna da ido na kabila ko addini. Mu cire hassada, kiyayya da gulma daga cikin zukatanmu. Idan muka ci gaba da rarrabuwar kai, wanda zai fi cin gajiyar hakan ba mu ba ne.

Manoma da Makiyaya: mu fahimci cewa kowa yana da muhimmiyar gudummawa ga rayuwar Arewa. Rikici ba zai magance komai ba. Tattaunawa, hakuri da adalci su ne hanyar samun mafita.

🔥 Lokaci ya yi da za mu hada kanmu!
Ba don kabila ba.
Ba don addini ba.
Ba don siyasa ba.
Sai don ceton Arewa da makomar 'ya'yanmu.

Mu zama masu kare juna, ba masu cutar da juna ba. Mu koyawa matasanmu cewa zaman lafiya shi ne arziki, hadin kai shi ne karfi, kuma ilimi shi ne makamin ci gaba.

Arewa ba za ta ci gaba da rarrabuwa ba.
Arewa za ta tashi ne idan 'ya'yanta sun fahimci cewa juna muke bukata. ❤️🤝

🤲 Allah Ya kawo zaman lafiya a Arewa, Ya hada zukatanmu, Ya cire hassada da kiyayya daga cikinmu, Ya kuma kare kasarmu Najeriya. Amin.

🕊️
🤝
❤️

🎉📢 SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! 📢🎉🎓 WAEC RELEASED RESULT 2026! 🎓An SAKI SAKAMAKON WAEC 2026! ✅🔥Ga duk ɗaliban da s**a r...
11/08/2026

🎉📢 SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! 📢🎉

🎓 WAEC RELEASED RESULT 2026! 🎓

An SAKI SAKAMAKON WAEC 2026! ✅🔥

Ga duk ɗaliban da s**a rubuta WAEC 2026, yanzu lokaci ya yi da za ku duba sakamakonku. 🎊

🖥️ CAFE ɗinmu yana nan a shirye domin taimaka muku wajen:

✅ Duba WAEC Result 2026
✅ Result Checking
✅ Generating WAEC e-PIN
✅ Taimako wajen shigar da bayanan Result Checker
✅ Printing na Result Slip

📌 KADA KA ZAUNA KANA JIRA!
Zo yanzu da WAEC Examination Number ɗinka, mu taimaka maka ka duba sakamakonka cikin sauƙi da sauri. 🚀

🏆 MUNANAN DA AIKI CIKIN SAURI, SAUKI DA AMINCI!

📍 Ku zo CAFE ɗinmu yanzu domin duba sakamakonku.

🔥 WAEC 2026 RESULT IS OUT!
🔥 COME AND CHECK YOUR RESULT NOW!

📞 Contact Us: [09029880868]
📍 Address: [NO. 4 LAYIN MAHAUTA ZANGON AYA]

29/06/2026
🎉🌙 BARKA DA SALLAH 🌙🎉ZTECH INTERFACE SOLUTIONS ACADEMIC na taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar wannan babbar rana ta E...
27/05/2026

🎉🌙 BARKA DA SALLAH 🌙🎉

ZTECH INTERFACE SOLUTIONS ACADEMIC na taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar wannan babbar rana ta Eid al-Adha.

Muna addu’ar Allah (SWT) ya karɓi ibadunmu, ya karɓi layyoyinmu, ya sanya wannan Sallah ta kasance mai cike da albarka, zaman lafiya, farin ciki da nasarori a rayuwarmu baki ɗaya.

Ga ɗalibanmu da al’ummar ZTECH baki ɗaya, muna godiya da kasancewarku tare da mu. Mu ci gaba da neman ilimi, ƙwarewa da cigaban rayuwa.

✨ Ilimi + Ƙwarewa = Nasara ✨

📧 Email: [email protected]

Sanarwa daga CEO Academic:
Abdullahi Yusuf

🐏 Barka da Sallah — Allah ya maimaita mana cikin alkhairi. 🕌

03/05/2026

ZTECH INTERFACE SOLUTION ACADEMIC TA SHIRYA TSAF DOMIN KARANTAR DA YARA ILIMIN COMPUTER DA SAURAN NA ZAMANI

Address

NO. 1 BAKIN KASUWA ZANGON AYA, LAYIN MAHAUTA KADUNA
Zangon Aya
800101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ztech Interface Solution Academic posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share