14/05/2026
ƘAUYAWA'S DAY KO ISKANCI.😈
•Wannan ɗabi'ar da 'yan mata s**a ɗaukarwa kansu ta wani taron rashin mutunci ea da sukeyi Alokacin bukuwan aure dasunan wai ƙauyawa's day wallahi ba alheri bane a society.
•Mu waiwayi baya muga lokacinda wannan iskancin yafara fitowa zamuga abubuwanda akeyi wancan lokacin sunsha banban da waɗanda akeyi yanzu,to nan gaba bamusan ya abin zai kasanceba.
•Yarinyace kasanta koda yaushe tana cikin hijabinta ta rufawa kanta asiri ta ɓoye tsiraicinta,amma da ance yau ranar ƙauyawa's day ɗin ƙwarta haka zaka ganta ta sanya wata 'yar ƙaramar riga wadda zata bayyana duk wani lungu da saƙo na tsiraicinta, ta bayyana tudun nononta.Kuma fa har waɗanda baka taɓa tunanin zasu iya yin irin wannan shigar zaka gansu.
•Cikin wannan isknacin kowa yabada tashi gudummuwa, Nafarkon zargi sune iyaye da suke barin 'ya'yansu suna fita da irin wannan shigar, nabiyu sai hukuma wadda itace takeda haƙƙen tsabtace society,na uku su kansu samarinda keyin auren sunada nasu laifin, eh sunada laifi kam,sai kace kai wallahi baza'ayima ƙauyawa's day ba,idan kuma akayi zaka fasa auren.
•Su mata ba'a taɓa miƙa musu ragama a barsu da ita dole a kula dasu sosai,saboda ɗan ƙaramin abu sai ya canja musu tunani.
Allah ya tsare mana imaninmu da mutuncinmu Ameen.🙏🙏🙏