29/04/2026
CHAKWAKIYA A JAMIYAR APC JAMA'ARE ITAS GADAU
Hajiya Bilkisu Haruna
“Ban ɗauki wannan mataki cikin gaggawa ba. Na zauna da wakilaina daga kowane lungu da saƙo na Jama’are domin jin ra’ayinsu da koken al’umma.
Wannan ba lamari na kaina ba ne—ina siyasa ne saboda al’umma. Idan ina son ci gaba da mutunci da amincewar da aka ba ni a matsayin Chairlady, dole ne in saurari muradunsu kuma in tsaya a inda za a ba su daraja.
Saboda haka, ina kira ga daukacin al’umma da su bude ido, su yi zaɓi cikin basira, su kuma goyi bayan waɗanda suke da tabbataccen tarihin aiki da gaskiya irin su SULEIMAN SAAD SULGAD . Su ne kaɗai za su iya kawo cigaba mai dorewa da walwalar Mata”