Africa Trust

Africa Trust Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Africa Trust, Kano.
(1)

Africa Trust Media Hub Ltd deliver first-class news and programmes grounded in objectivity, fairness, and accuracy, promoting equal opportunitie within its team and fostering inclusive engagement with diverse audiences [email protected]

Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya na fuskantar babbar matsalar rashin abinci mai gina jiki, wadda...
17/09/2026

Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya na fuskantar babbar matsalar rashin abinci mai gina jiki, wadda ke buƙatar ƙarin saka hannun jari da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Jaridar Daily Trust ta rawaito Sanusi ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Legas, yayin taron kimiyya na shekara-shekara karo na 56 na ƙungiyar Nutrition Society of Nigeria (NSN).

Ya ce ba za a iya magance matsalar rashin abinci mai gina jiki ta ɓangaren lafiya kaɗai ba, domin noma, ilimi, ruwa da tsaftar muhalli, kasuwanci da shugabanci duk suna da tasiri a kai.

Sanusi ya ce wani sabon bincike ya nuna cewa kashi 41.1 cikin 100 na yaran Najeriya da shekarunsu ba su wuce biyar ba na fama da tangal-tangal wajen girma sakamakon rashin ingantaccen abinci, yayin da kashi 19.2 ke fama da matsananciyar matsalar.

Ya ce lamarin ya fi muni a Arewa maso Yamma, inda kashi 58.2 cikin 100 na yaran ke fama da tangal-tangal wajen girma.

Sarkin ya yi kira da a ƙara saka hannun jari wajen samar da abinci mai gina jiki a cikin gida, tare da ƙarfafa tallafin kuɗaɗen da ake ware wa harkar da kuma tabbatar da cewa sun isa ga waɗanda suke buƙata.

Ya kuma jaddada cewa ya kamata a mayar da hankali wajen haɗa harkar abinci mai gina jiki da noma, ilimi da sauran muhimman ɓangarorin tattalin arziki domin magance matsalar cikin dogon lokaci.

Ƙungiyar Ƙwadago ta kasa NLC ta buƙaci Gwamnatin tarayya ta gaggauta samar da tallafin rage radadin tsadar rayuwa da kum...
17/09/2026

Ƙungiyar Ƙwadago ta kasa NLC ta buƙaci Gwamnatin tarayya ta gaggauta samar da tallafin rage radadin tsadar rayuwa da kuma ƙarin albashi ga ma’aikata a faɗin ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito Shugaban ƙungiyar NLC, na kasa Joe Ajaero, ya ce ƙarin farashin man fetur zai ƙara tsananta halin matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke ciki.

Ajaero ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce tashin farashin man fetur kan janyo ƙarin kuɗin sufuri, wanda daga bisani ke shafar farashin abinci, haya, kuɗin makaranta da sauran muhimman kayayyaki da ayyuka.

Ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin rage wa ’yan ƙasa da ’yan kasuwa raɗaɗin ƙarin farashin man fetur.

NLC ta kuma yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da sayar da ɗanyen man Najeriya ga matatun mai na cikin gida da Naira.

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya ce ’yan Najeriya na da kaso kan rashin kyakkyawan shugabancin da suke y...
17/09/2026

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya ce ’yan Najeriya na da kaso kan rashin kyakkyawan shugabancin da suke yawan korafi a kai.

jaridar the cable ta ambato Ndume ya ce ’yan siyasa samfurin al’ummar da s**a fito ne, don haka bai kamata a dora dukkan laifin matsalolin shugabanci a kansu kaɗai ba.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, yayin gabatar da littafin Military Transformational Leadership in Action: The Buratai Era.

Sanatan ya ce ’yan ƙasa suna da muhimmiyar rawa wajen zaɓar shugabanninsu, ciki har da irin mutanen da suke goyon baya da kuma yadda suke shiga harkokin siyasa.

Ya kuma ce ya kamata ’yan Najeriya su taka rawa wajen kawo ƙarshen maguɗin zaɓe, yana mai cewa idan ’yan ƙasa s**a sanya shugabanni a kan kujeru, suna da alhakin irin shugabancin da za su samu.

Ndume ya yi wannan bayani ne yayin da yake mayar da martani ga kalaman Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda ya soki ’yan siyasa kan siyasantar da ƙabila da addini da kuma tasirin hakan ga tsaro da shugabanci.

’yan Najeriya na da kaso kan rashin kyakkyawan shugabancin da suke yawan korafi a kai.
17/09/2026

’yan Najeriya na da kaso kan rashin kyakkyawan shugabancin da suke yawan korafi a kai.

Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kano ta sanar da maye gurbin dan takararta na gwamna, Muhammad Bello Dalha, inda ta sanya Alh...
17/09/2026

Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kano ta sanar da maye gurbin dan takararta na gwamna, Muhammad Bello Dalha, inda ta sanya Alhaji Muhammad Sani Abacha, dan tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Janar Sani Abacha, a matsayin sabon dan takararta na zaben mai zuwa.

Canjin ya biyo bayan janye wa daga takara da tsohon wanda aka zaba ya yi, kamar yadda Africa Trust ta rawaito daga jaridar Daily Trust.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Dr. Bello Gambo Bichi, ya bayyana hakan ne a wani taro na musamman da aka gudanar a babban birnin jihar Kano, inda aka gudanar da zaben fidda gwani na musamman domin tabbatar da sabon dan takarar.

Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan tattaunawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar s**a yi a Kano da kuma babban birnin tarayya Abuja, inda aka amince da a gudanar da sabon zabe bisa ga kundin tsarin mulkin jam'iyyar da dokokin zabe.

Baya ga haka, jam'iyyar ta kuma amince da ba da matsayin takarar mataimakin gwamna ga tsohon shugaban faction na jam'iyyar, Alhaji Yusuf Ado Kibiya, a wani mataki na dinke baraka da samar da hadin kai tsakanin mambobin jam'iyyar.

Shugabannin jam'iyyar sun yi kira ga dukkan magoya baya da su hada kai wuri guda domin tabbatar da cewa jam'iyyar ta samu nasara a dukkan matakai a zabe mai zuwa.

Idan har kana tunanin campaign din Tunibu must go wasa ne to kafara shirin rugumar taransifoma ~ Abdullah Amdaz, Jarumin...
17/09/2026

Idan har kana tunanin campaign din Tunibu must go wasa ne to kafara shirin rugumar taransifoma ~ Abdullah Amdaz, Jarumin fina-finan Hausa

Kuskure mafi muni da za mu sake yi a ƙasar nan shi ne ƙara zaɓar Tinubu a karo na biyu, wallahi ~  Alh Mustapha Haladu M...
16/09/2026

Kuskure mafi muni da za mu sake yi a ƙasar nan shi ne ƙara zaɓar Tinubu a karo na biyu, wallahi ~ Alh Mustapha Haladu Mai citta Dan jamiyyar APC

16/09/2026

Ƙungiyar ’yan tebura da ke Kasuwar Kantin Kwari, ƙarƙashin jagorancin Abba Maisabuwa, ta bayyana godiyarta ga Kwamishinan Ƙasa da Safiyo na Jihar Kano, bisa ƙoƙarinsa na ganin Gwamnatin Kano ta biya ’yan tebura hakkokinsu.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke kofar kudu a Kano ta aikewa Malam Lawan Triumph sammaci domin ya bayyana a gabanta...
16/09/2026

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke kofar kudu a Kano ta aikewa Malam Lawan Triumph sammaci domin ya bayyana a gabanta, bayan wasu ƙungiyoyin addinin Musulunci sun shigar da ƙara a kansa.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Ibrahim Sarki Yola, ta bayar da sammacin ne bisa zargin cewa Malam Lawan Triumph ya yi wasu kalamai da ka iya tunzura al’umma.

Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagorancin Muhammad Al-Bakary Mikail, ne s**a shigar da ƙarar, inda s**a zargi Malam Lawan da yin kalaman da ka iya haifar da tashin hankali ko rikici a tsakanin al’umma.

Ana sa ran Malam Lawan Triumph zai bayyana a gaban kotun domin amsa tuhumar da aka shigar a kansa.

16/09/2026

Kwamishinan Yaɗa Labarai ya ƙalubalanci ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, da su fito su gwada tseren gudu domin tantance cikakken namiji

Address

Kano

Telephone

+2348177352017

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Africa Trust posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Africa Trust:

Shortcuts

Share