Sabuwar Nigeria

Sabuwar Nigeria Domin samun sahihan labarai kan ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa a faɗin Najeriya

24/05/2026

📞🇳🇬 NAHCON Ta Kaddamar Da Cibiyar Karɓar Korafe-Korafe Ta Sa'o'i 24 A Makkah

Domin ƙara inganta walwala da jin daɗin alhazan Najeriya a Hajjin 2026, Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta buɗe sabuwar cibiyar karɓar kira ta zamani mai aiki ba dare ba rana a Makkah.

Sabon tsarin zai bai wa alhazai damar kai korafe-korafe ko neman taimako kan matsalolin da s**a shafi masauki, abinci, sufuri, lafiya da sauran harkokin jin daɗi yayin da suke ƙasa mai tsarki.

🎥 Kalli cikakken rahoton yadda wannan sabon tsari zai taimaka wajen inganta sadarwa da saurin magance matsalolin alhazai.

☎️ Lambobin Tuntuɓa: +966565460059 +966568608760

24/05/2026

Yadda Alhazai daga jihohi daban daban na Najeriya ke bayyana shaukin da s**a ji na ziyarar Annabi Muhammad SAWA a birnin Madina.

Yaren Hausa Da Yarbanci Na Cikin Harsuna 35 Da Za A Fassara Huɗubar Arfa Kai Tsaye A BanaDaga Aliyu SambaMahukuntan Ƙasa...
23/05/2026

Yaren Hausa Da Yarbanci Na Cikin Harsuna 35 Da Za A Fassara Huɗubar Arfa Kai Tsaye A Bana

Daga Aliyu Samba

Mahukuntan Ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa za a fassara huɗubar ranar Arfa ta Hajjin shekarar 2026 zuwa harsuna 35 na duniya, ciki har da Hausa da Yarbanci daga Najeriya, domin bai wa miliyoyin Musulmai damar sauraron saƙonnin huɗubar cikin yarukan da s**a fi fahimta.

Shirin, wanda Hukumar Kula da Harkokin Addini ta Masallacin Harami da Masallacin Annabi ﷺ ke jagoranta, zai kasance kai tsaye ta hanyoyin sadarwa na zamani da tashoshin yaɗa labarai masu alaƙa da aikin Hajji.

Hausa da Yarbanci na daga cikin jerin manyan harsunan da aka amince da su tare da Turanci, Faransanci, Indonesiya, Urdu, Turkanci, Farisanci, Sinanci, Rashanci, Hindi, Swahili da wasu da dama daga sassa daban-daban na duniya.

Mahukuntan Saudiyya sun ce manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa saƙonnin addini, nasiha da darussan da ke cikin huɗubar Arfa sun isa ga Musulmai a ko'ina cikin duniya ba tare da tangarɗar harshe ba.

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Addini ta Harami da Masallacin Annabi ﷺ, Abdulrahman Al-Sudais, ya bayyana cewa aikin fassarar huɗubar Arfa na daga cikin manyan shirye-shiryen da aka gina bisa gogewa da aka tara tsawon shekaru.

Ya ce shirin zai ba Musulman da ba sa jin Larabci damar amfana da saƙonnin ɗabi'a da jinƙai da huɗubar ke ɗauke da su, tare da isar da saƙon Musulunci na zaman lafiya ga duniya baki ɗaya.

Huɗubar Arfa, wadda ake gabatarwa a Dutsen Arafat a lokacin Hajji, na daga cikin mafi muhimmancin huɗubobi a Musulunci, kuma miliyoyin Musulmai a faɗin duniya na bibiyarta a kowace shekara.

A wani ɓangare kuma, mahukuntan Saudiyya sun sake tunatar da ƙasashen da ke halartar Hajji da su tabbatar da wayar da kan alhazansu kan bin ƙa'idojin aikin Hajji domin tabbatar da tsaro da nasarar gudanar da ibadar.

Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa tana ci gaba da daidaita ayyukanta da tsarin zamani, inda sashen fasahar sadarwa na hukumar ke aiki kan cikakken tsarin zamani domin inganta ayyukan Hajji daidai da hangen nesa na Saudiyya na shekarar 2030.

Masu lura da harkokin Hajji sun bayyana saka Hausa da Yarbanci cikin harsunan da za a fassara huɗubar Arfa a matsayin wani muhimmin mataki da ke nuna muhimmancin al'ummar Musulman Najeriya a duniya, tare da bai wa miliyoyin masu magana da waɗannan harsuna damar sauraron huɗubar kai tsaye cikin sauƙi da fahimta.

NAHCON Ta Magantu Kan Korafe-Korafen Masaukin Alhazan Najeriya A Mina Da ArafatHukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta magan...
23/05/2026

NAHCON Ta Magantu Kan Korafe-Korafen Masaukin Alhazan Najeriya A Mina Da Arafat

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta magantu kan wasu rahotanni da aka danganta da ɗaya daga cikin Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi game da matsayin shirye-shiryen masaukin alhazan Najeriya a Mina da Arafat gabanin babban aikin Hajjin shekarar 2026.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta fahimci cewa damuwa da korafe-korafe na iya tasowa yayin shirye-shiryen gudanar da aiki mai girma da sarkakiya kamar Hajji, amma ta jaddada cewa tattaunawa da ci gaba da tuntubar juna tsakanin masu ruwa da tsaki su ne mafi dacewa wajen warware matsaloli cikin lokaci.

NAHCON ta kuma bayyana cewa zaɓen kamfanonin da za su samar da ayyuka a wuraren Masha’ir, wato Mina, Arafat da Muzdalifah, ya kasance ne bisa shawarwari da zaɓin da jihohin da ke halartar Hajji s**a bayar yayin tattaunawa da hukumar.

A cewar sanarwar, hukumar ta mutunta matsayar da aka cimma tare da amincewa da ita domin tabbatar da walwalar alhazai da kuma gudanar da aiki cikin haɗin kai.

Hukumar ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki, ciki har da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da jami'ansu, da su ba da fifiko ga tattaunawa, haɗin gwiwa da neman mafita tare da masu samar da ayyuka maimakon garzayawa kafafen yaɗa labarai kan batutuwan da har yanzu ake kokarin warwarewa ta hanyoyin da aka tanada.

NAHCON ta kuma ƙarfafa gwiwar jihohi da su ci gaba da aiki tare da kamfanonin da ke samar da ayyuka a wuraren aikin Hajji domin gano gibin da ke akwai, inganta shirye-shirye idan buƙatar hakan ta taso, tare da tabbatar da cewa jin daɗi, tsaro da walwalar alhazan Najeriya sun kasance a gaba.

Hukumar ta sake bai wa maniyyata Hajji tabbacin cewa za ta ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da ayyuka a wuraren Masha’ir tare da haɗa kai da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da Hajjin bana cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da dubban alhazan Najeriya ke ci gaba da isa ƙasa mai tsarki domin fara manyan ibadun Hajjin shekarar 2026.

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Zaɓen Fidda Gwanin APC A Matsayin Kwarin Gwiwar Dorewar DimokuraɗiyyaShugaban Najeriya, Bola A...
23/05/2026

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Zaɓen Fidda Gwanin APC A Matsayin Kwarin Gwiwar Dorewar Dimokuraɗiyya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC da aka gudanar a faɗin ƙasar a matsayin wata alama ta ƙarfi da bunƙasar dimokuraɗiyyar cikin gida a jam’iyyar mai mulki.

Tinubu ya bayyana haka ne bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a mazabar Ikoyi-Obalende Ward L2 da ke jihar Legas ranar Asabar.

Shugaban ya ce tsarin ya bai wa mambobin jam’iyya a matakin ƙasa damar taka rawar gani wajen zaɓen shugabanninsu, yana mai cewa hakan na ƙara ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya.

"Wannan wata alama ce ta dimokuraɗiyyar cikin gida, kuma an gudanar da ita yadda aka tsara. Siyasar tushe ce wadda ke bai wa kowane mamba damar shiga cikin tsarin zaɓe," in ji shugaban.

Ya ƙara da cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana da tsari, lamarin da ya nuna cewa jam’iyyar APC na da ingantaccen tsarin gudanar da harkokinta na cikin gida.

Tinubu ya kuma yaba wa gwamnoni da shugabannin jam’iyyar a jihohi daban-daban kan yadda s**a gudanar da matakan shirye-shiryen zaɓen, tun daga zaɓukan gundumomi zuwa tantance wakilai da rajistar mambobi.

A cewarsa, yadda aka gudanar da waɗannan matakai ya nuna cewa ana iya bai wa dimokuraɗiyya maki masu yawa a ƙasar.

Shugaban ya jaddada cewa APC za ta ci gaba da rungumar tsarin dimokuraɗiyya mai gaskiya da bai wa mambobi damar zaɓar shugabanninsu cikin 'yanci, yana mai cewa hakan shi ne ginshiƙin ci gaban siyasa mai ɗorewa.

Ya kuma yaba wa jami’an zaɓe, shugabannin jam’iyya da hukumomin tsaro bisa rawar da s**a taka wajen tabbatar da zaman lafiya da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

Tinubu ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ci gaba da mara wa cibiyoyin dimokuraɗiyya baya tare da ƙarfafa haɗin kai na ƙasa.

Har ila yau, ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ci gaba da bin tafarkin dimokuraɗiyya, inganta shugabanci da aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’ummar Najeriya tare da tabbatar da zaman lafiyar siyasa a ƙasar.

Gwamnatin Tinubu Ta Tabbatar Da Kammala Jigilar Alhazan Najeriya Sama Da 40,000 Zuwa Saudiyya Cikin NasaraDaga Aliyu Sam...
23/05/2026

Gwamnatin Tinubu Ta Tabbatar Da Kammala Jigilar Alhazan Najeriya Sama Da 40,000 Zuwa Saudiyya Cikin Nasara

Daga Aliyu Samba

An samu wani babban gagarumin nasara a harkokin aikin Hajjin shekarar 2026 yayin da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta kammala jigilar alhazan Najeriya zuwa Ƙasar Saudiyya cikin nasara, inda aka yi jigilar alhazai sama da 40,000 cikin kwanaki 18 kacal.

Wannan nasara ta sake tabbatar da irin kulawa da muhimmancin da Gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ke bai wa harkokin addini da jin daɗin al’ummar Najeriya, musamman Musulmai masu gudanar da ibadar Hajji.

A cewar Hukumar NAHCON, an gudanar da jimillar jirage 98 daga ranar 3 ga watan Mayu zuwa ranar 21 ga watan Mayu, inda aka yi jigilar alhazai 40,250 da s**a samu bizar Hajji ta hannun hukumar. Wannan ya nuna irin ingantaccen shiri da tsare-tsaren da aka yi tun kafin fara aikin.

Shugaban Hukumar NAHCON, Ambassador Ismail Abba Yusuf, ya bayyana cewa nasarar da aka samu ba za ta rasa nasaba da cikakken goyon baya da jagorancin Shugaba Tinubu da kuma sa ido na kusa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, waɗanda s**a tabbatar da samar da yanayin da ya ba da damar gudanar da aikin cikin sauƙi duk da ƙalubalen da ake fuskanta a duniya.

Haka kuma, kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ya ƙunshi sanatoci da mambobin Majalisar Wakilai ya yaba da yadda aka gudanar da aikin Hajjin bana, inda ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a fannin daidaitawa, haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma ingancin ayyukan da aka samar wa alhazai idan aka kwatanta da shekarun baya.

Yayin wata ziyarar sa ido da s**a kai birnin Madina domin duba masaukan alhazai da tantance ayyukan da ake gudanarwa, shugaban tawagar, Sanata Ali Ndume, ya ce aikin Hajjin 2026 ya nuna kyakkyawan tsari, ingantaccen shugabanci da kuma ƙwarewar gudanarwa daga NAHCON da sauran hukumomin da ke da alhakin aikin.

Ya ƙara da cewa nasarar kammala jigilar alhazai kafin rufe sararin samaniyar Saudiyya wata shaida ce ta ingantaccen shiri da kuma kyakkyawar jagoranci wajen tabbatar da nasarar manyan ayyukan ƙasa.

Har ila yau, gwamnatin ta tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen gudanar da ayyukan Masha’ir a Mina, Arafat da Muzdalifah domin tabbatar da jin daɗi, tsaro da walwalar alhazan Najeriya yayin gudanar da manyan rukunnan Hajji.

Wannan ci gaba ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu ke ƙara mayar da hankali wajen inganta ayyukan sufuri, gudanarwa da hidimomin jama’a, lamarin da ke haifar da sakamako mai kyau a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma.

Bugu da ƙari, NAHCON ta sanar da cewa shirye-shiryen dawo da alhazai gida bayan kammala aikin Hajji sun riga sun fara, inda ake sa ran fara jigilar dawowa Najeriya daga ranar 3 ga watan Yuni.

Yayin da miliyoyin Musulmai daga sassa daban-daban na duniya ke gudanar da wannan babban rukuni na Musulunci, Najeriya ta sake nuna cewa tana da ƙwarewa da tsari wajen kula da alhazanta, abin da ke ƙara ɗaga martabar ƙasar a idon duniya.

Ana sa ran wannan nasara za ta zama tubalin da za a gina sabbin nasarori a kai, musamman yayin da NAHCON ta sanar da cewa shirye-shiryen Hajjin shekarar 2027 za su fara nan take bayan kammala aikin Hajjin bana.

Sanata Barau zai raba buhunan taki sama da 53,000 kyauta ga manoma a Kano ta ArewaMataimakin Shugaban Majalisar Dattawa,...
23/05/2026

Sanata Barau zai raba buhunan taki sama da 53,000 kyauta ga manoma a Kano ta Arewa

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kammala shirye-shiryen raba buhunan taki 53,040 kyauta ga manoma da sauran al’ummar mazabarsa a shiyyar Kano ta Arewa domin tallafa wa noman bana na shekarar 2026.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kai, Isma’il Mudashir, ya fitar, ya ce za a fara rabon takin ne daga ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026, a dukkan ƙananan hukumomi 13 da ke ƙarƙashin Kano ta Arewa.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan tallafi wani ɓangare ne na shirye-shiryen da Sanata Barau ke aiwatarwa duk shekara domin tallafa wa manoma, ƙara yawan amfanin gona da kuma taimakawa wajen tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.

A cewar sanarwar, buhunan takin da za a raba sun kai adadin manyan tireloli 88, kuma za su amfanar da manoma da sauran rukunan al’umma daban-daban.

Daga cikin waɗanda za su ci gajiyar shirin akwai manoma, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a matakai daban-daban, shugabannin ƙananan hukumomi da mataimakansu, kansiloli da sakatarorinsu.

Sauran sun haɗa da mambobin kwamitin APC, limamai, hakimai, masu unguwanni, shugabannin makarantu, jami’an tsaro da malamai, da sauran jama’a.

Sanata Barau ya ce yana ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da shirye-shiryen da ke inganta rayuwar al’ummar mazabarsa kai tsaye, yana mai cewa samun kayan noma kamar taki a kan lokaci na da matuƙar muhimmanci wajen ƙara yawan amfanin gona da tabbatar da wadatar abinci.

Ya kuma bayyana cewa tallafin na da nufin ƙarfafa ƙoƙarin gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.

Sanatan ya buƙaci waɗanda za su amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata domin cimma manufofin da aka tanada.

Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Raɗe-Raɗin Canza Sunan Najeriya Da Soke Shari’a A ArewaFadar Shugaban Kasa ta karyata wani ...
21/05/2026

Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Raɗe-Raɗin Canza Sunan Najeriya Da Soke Shari’a A Arewa

Fadar Shugaban Kasa ta karyata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin sauya sunan Najeriya zuwa “United States of Nigeria” tare da soke dokar Shari’a a Arewacin kasar.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar 21 ga watan Mayun 2026, gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin “labarin karya” da wasu ke yadawa domin haddasa rikici da tayar da hankalin jama’a gabanin babban zaben 2027.

Sanarwar ta ce babu wani kudiri da Shugaba Tinubu ke shirin aikewa Majalisar Dokoki ta Kasa mai suna “Project True Federation” kamar yadda ake yadawa.

Fadar shugaban kasar ta zargi masu yada rahoton da kokarin haifar da rabuwar kai da rikicin siyasa a kasar.

“’Yan Najeriya su yi watsi gaba daya da wannan labari saboda masu yada shi makiyan zaman lafiya ne kuma masu neman tayar da tarzoma,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa sauya kundin tsarin mulkin kasa ba abu ne da shugaban kasa ko majalisa za su yi kai tsaye ba, domin akwai matakai masu tsauri da s**a hada da samun amincewar kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin kasar da kuma majalisun dokokin jihohi 24.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu na mayar da hankali ne wajen aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin sa ta fara domin inganta rayuwar ’yan Najeriya.

Fadar shugaban kasar ta gargadi jama’a da su rika taka-tsantsan wajen karanta da yada rahotannin karya musamman yayin da harkokin yakin neman zabe ke kara karatowa.

21/05/2026

Alhazan Jihar Zamfara sun samu bita a Madina kan yadda za su gudanar da ibadun Hajji tun daga Mikat na Zul Hulayfa har zuwa Umara, Dawafi, Sa’ayi da sauran rukunan Hajji.

Sheikh Sa’idu Aliyu Gusau ya jagoranci gabatar da darasin tare da jaddada muhimmancin biyayya, hakuri da bin ka’idojin aikin Hajji domin samun Hajji karbabbe.

NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Najeriya Zuwa Saudiyya Cikin NasaraHukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da nasara...
21/05/2026

NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Najeriya Zuwa Saudiyya Cikin Nasara

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da nasarar kammala jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya domin aikin Hajjin 2026 cikin nasara tun kafin cikar wa'adin jigilar maniyyata zuwa Makkah.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar daga birnin Makkah, inda ta ce an kammala jigilar ne da misalin karfe 10:44 na safiyar ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce an kammala aikin ne kafin wa’adin da hukumomin Saudiyya s**a sanya na dakatar da jiragen shigo da alhazai kafin fara gudanar da ibadun Hajji.

NAHCON ta bayyana cewa aikin jigilar ya fara ne tun ranar 3 ga watan Mayu, inda jirgin Max Air daga Jihar Zamfara ya kasance jirgi na karshe da ya kai alhazai Saudiyya.

A cewar hukumar, an gudanar da jimillar jirage 98 cikin kwanaki 18, inda ake samun kusan jirage biyar a kullum.

Sanarwar ta kara da cewa an bai wa Najeriya guraben maniyyata 50,000 domin aikin Hajjin bana, ciki har da gurabe 9,750 da aka ware wa kamfanonin yawon Hajji masu lasisi, baya ga jami’an gudanarwa da sauran ma’aikata.

Hukumar ta ce zuwa lokacin kammala jigilar, kusan alhazai 39,000 ne aka yi nasarar kai wa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji, ba tare da kirga jami’ai da wakilan gwamnati ba.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa wasu daga cikin maniyyatan sun kasa tafiya sakamakon wasu dalilai da ba a iya kauce musu, ciki har da rasuwa da rashin lafiya bayan an fitar musu da biza.

NAHCON ta gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa yadda aka gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali da nasara tare da hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki.

Shugaban Hukumar, Ambasada Ismail Yusuf, ya yaba da jajircewa da hadin kan mambobin hukumar, ma’aikata, hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, kamfanonin yawon Hajji, kamfanonin jiragen sama, jami’an tsaro da sauran kwamitocin gudanarwa.

Hukumar ta kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa harkokin Hajji, tare da gode wa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, kan sa ido da kulawar da yake bayarwa domin tabbatar da jin dadin alhazai duk da kalubalen da ake fuskanta a duniya.

NAHCON ta tunatar da alhazai cewa lokacin Hajji lokaci ne mai muhimmanci da ke bukatar hakuri, da’a, sadaukarwa da kuma yawaita addu’o’i.

Hukumar ta bukace su da su kiyaye dokoki da ka’idojin aikin Hajji a kasar Saudiyya tare da gujewa duk wani abu da ka iya jawo musu hukunci ko matsala.

Har ila yau, hukumar ta tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen gudanar da ayyukan Masha’ir, tare da cewa za a ci gaba da sanya ido domin tabbatar da walwala da jin dadin alhazai.

NAHCON ta kara da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen dawo da alhazai gida, wanda ake sa ran zai fara daga ranar 3 ga watan Yuni.

Hukumar ta ce za ta sanar da jadawalin dawowar alhazai a lokacin da ya dace, tare da bayyana cewa shirye-shiryen Hajjin 2027 za su fara nan take bayan kammala aikin Hajjin bana domin kara inganta ayyuka da nasarorin da aka samu.

A karshe, hukumar ta roki Allah Ya karbi ibadun Hajjin maniyyata tare da dawo da su gida lafiya.

Najeriya da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin ArzikiGwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na yin aiki ...
21/05/2026

Najeriya da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na yin aiki kafada da kafada da ƙasar Poland wajen inganta harkokin tsaron cikin gida da bunƙasa tattalin arziki.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi Mataimakin Firaministan Poland, Krzysztof Gawkowski, a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Tunji-Ojo ya ce Najeriya na da burin anfani da ƙwarewar Poland wajen kula da iyakoki da kuma dabarun tsaron cikin gida da s**a tabbatar da nasara a ƙasar.

Ya ce gwamnatin Najeriya na sa ran yin haɗin gwiwa da Poland musamman a fannoni kamar horas da jami’ai, amfani da fasaha, tsaron yanar gizo da sauran muhimman fannoni.

“Mun yi imani cewa haɗin kai da koyo daga juna ne hanya mafi dacewa wajen rage rauninmu tare da ƙarfafa bangarorin da muke da ƙwarewa,” in ji shi.

Ministan ya tabbatar wa baƙin cewa ziyarar ba za ta zama ta al’ada kawai ba, domin za ta zama tubalin da za a gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin ƙasashen biyu.

Ya kuma bayyana cewa ana shirye-shiryen kai ziyara ƙasar Poland domin ƙara zurfafa tattaunawa da gwamnatin ƙasar da kuma ɓangaren kasuwanci masu alaƙa da ma’aikatar harkokin cikin gida.

Tunji-Ojo ya ƙara da cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na nuna cewa gwamnati na fahimtar hanyoyin gina tattalin arziki mai ƙarfi.

A nasa jawabin, Mataimakin Firaministan Poland, wanda kuma shi ne Ministan Harkokin Dijital na ƙasar, Krzysztof Gawkowski, ya ce Najeriya ƙasa ce mai tarin albarkatun tattalin arziki, yawan jama’a da kuma damar ci gaban fasaha.

Ya bayyana Najeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa wajen gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin ƙasashen biyu.

Gawkowski ya ce Poland a shirye take ta taimaka wa Najeriya ta hanyar ƙwarewarta a fannoni kamar kirkire-kirkire, fasahar zamani, gina ababen more rayuwa da kuma sabbin dabarun fasaha.

Haka kuma ya bayyana fatan ganin Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya ya kai ziyara Poland domin ƙara ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu.

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sabuwar Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sabuwar Nigeria:

Share

Category