Yakubun Bauchi Memorial Academy

Yakubun Bauchi Memorial Academy Hadda/islamiyya/Nursery & primary school

11/09/2026
31/07/2026

Assalamu alaikum warahmatullah
Munasanar da jamaa In sha Allah daafara karatu Ranan Asabar 15 July 2026 Har yanzu Muna bada admission ga masu buqata
08065780424
Yakubun Bauchi quarters behind Nitel Gombe road Bauchi

30/06/2026

📘 YAKUBUN BAUCHI MEMORIAL ACADEMY
Bayan NITEL T-Junction, Gombe Road, Bauchi
📞 08065780424
📢 SANARWA GA MAGIDANTA DA MATASA
Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh.
Makarantar Yakubun Bauchi Memorial Academy na farin cikin sanar da buɗe Sabon Aji na Karatun Al-Qur'ani ga magidanta da matasa.
🕌 Abubuwan da za a koya:
Tarteel da Haddan Al-Qur'ani
Koyon Huruf (Haɗa Baƙi)
Tauheed
Fiqhu
Hadisi
⏰ Lokacin Karatu:
Daga Magriba zuwa Isha'i
Kwanakin Karatu: Asabar zuwa Laraba
💡 An samar da hasken Solar a duk ajujuwa domin tabbatar da ingantaccen haske da yanayin karatu mai kyau.
💵 Kudin Shiga:
Form: ₦1,000
Registration: ₦5,000
Kudin Wata: ₦2,000
📅 Fara Karatu: Asabar, 04/07/2026, daidai da 18 ga Al-Muharram, 1448H, In shaa Allah.
📞 Domin ƙarin bayani ko yin rajista: Umar Ahmad Goni
08065780424
🌹 Ku hanzarta yin rajista. Wannan dama ce ta koyon Al-Qur'ani da ilimin addini cikin ingantaccen yanayi.kusani baa girma ko wajen Neman ilimin addini akwai matsala babba mutun ya mutu bai iya karanta Alqurani ba yadda muke qoqari akan yayammu mumafa baifadi akammu ba Neman ilimi wajibine akan dukkan musulmi da musulma.Allah Ya ba da sa'a.
Allah Ya sanya albarka a wannan shiri, Ya sa ya zama sanadin yawaitar masu koyon Al-Qur'ani da aiki da shi.

26/06/2026

📘 YAKUBUN BAUCHI MEMORIAL ACADEMY
(Bangaren Yan Hadda da Tarteel – Day & Boarding, Special Hadda)
📢 SANARWA TA MUSAMMAN
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh.
Makarantar Yakubun Bauchi Memorial Academy tana sanar da daukacin jama’a cewa ta fara karɓar sabbin ɗalibai a bangaren Yan Hadda da Tarteel (Day & Boarding – Special Hadda).
📅 Lokacin fara karatu:
Za a fara karatu daga 1 ga August, 2026, in sha Allah.
📝 Sayar da Fom da Interview:
Daga 1 ga Mayu, 2026 – 30 ga Yuni, 2026
💰 Kudin fom: ₦10,000
🗂 Lokacin Registration:
Daga 1 ga Yuli – 31 ga Yuli, 2026
➡️ Iyaye za su iya fara ajiya (deposit) na registration daga 1 ga Mayu, 2026, da zarar ɗalibi ya samu admission.
Muna roƙon Allah ya sanya albarka, ya ba mu nasara, ya kuma yi mana jagora.
📞 Lambar waya: 08065780424
✍️ Umar Ahmad Goni

Alhamdulillah aikin ajujuwan Haddan tareda wajen kwanan dalibai yakai linter Muna Neman gudumawa Domin cigaba da wannan ...
14/06/2026

Alhamdulillah aikin ajujuwan Haddan tareda wajen kwanan dalibai yakai linter Muna Neman gudumawa Domin cigaba da wannan aiki
Yakubun Bauchi memorial Academy Bayan Nitel
08065780424

07/06/2026

Nasiha Ga Dalibai, Iyaye Da Malamai Kan Dagewa Da Juriya Wajen Haddar Al-Qur'ani
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Alhamdulillah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), iyalansa da sahabbansa baki ɗaya.
Ya ku dalibai, ku sani cewa haddar Al-Qur'ani babban ibada ce kuma hanya ce ta samun ɗaukaka a duniya da lahira. Kada ku gaji ko ku karaya idan haddar ta yi wahala. Ku dage da maimaitawa, ku kasance masu haƙuri da juriya, domin Allah yana tare da masu haƙuri. Duk ayar da kuka haddace tana ƙara kusantar da ku ga Allah.
Ya ku iyaye, ku taimaka wa 'ya'yanku wajen haddar Al-Qur'ani ta hanyar ƙarfafa musu gwiwa, samar musu da lokacin karatu, da kuma yi musu addu'a. Kada ku matsa musu fiye da ƙarfi, sai dai ku kasance masu nuna ƙauna da kulawa. Ladan tarbiyyar yaro a kan Al-Qur'ani yana da girma ƙwarai.
Ya ku malamai, ku ci gaba da jajircewa wajen koyarwa da tarbiyya. Ku yi amfani da hikima, haƙuri da tausayi wajen mu'amala da ɗalibai. Ku tuna cewa koyar da Al-Qur'ani yana daga cikin ayyukan da s**a fi falala a Musulunci.
Mu sani cewa nasara a haddar Al-Qur'ani tana buƙatar:
Ikhlasi (kyakkyawar niyya).
Haƙuri da juriya.
Yawan maimaitawa.
Addu'a da neman taimakon Allah.
Kyakkyawar haɗin kai tsakanin iyaye, malamai da ɗalibai.
Allah Ya sanya mu cikin mutanen Al-Qur'ani, Ya sauƙaƙa mana haddarsa da aiki da abin da yake cikinsa.
Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Umar Ahmad Goni
Proprietor & Director
Yakubun Bauchi Memorial Academy
Hadda and Islamiyya Section

03/05/2026

Yan special Hadda Day da boarding sunkai suratu yusuf daga baqarah tafiya tafara nisa Kusa musu albarka.

01/05/2026

Assalamu alaikum warahmatullah fatan kuna lfy Muna neman gudumawan Gina ajujuwan Haddan Alqurani da hostel na dalibai Hadda dasuke kwana saka waqafi wa iyeyenka ko sadaqul jariya cikin irin wadannan ayyukan alkhairi
Munabuqatan gudumawan kayan aiki kudi ko daukan nauyin aikin gaba daya
Domin saka gudumawa ga account number na Makaranta
5979339019 fcmb yakubun Bauchi memorial Academy
Domin tuntuba 08065780424
Umar Ahmad Goni

Address

Yakubun Bauchi Quarters Gombe Road
Bauchi

Telephone

+19027078807

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yakubun Bauchi Memorial Academy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Yakubun Bauchi Memorial Academy:

Shortcuts

Share