Jibwis Tarmuwa

Jibwis Tarmuwa Official page of Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Tarmuwa Division.

Dedicated to the propagation of authentic Islamic teachings based on the Qur'an and Sunnah.

13/08/2026
13/08/2026
03/08/2026

I got over 50 reactions on my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

‎SAƘON TAYA MURNA‎‎Muna  miƙa saƙon taya murna ga Alhaji Ibrahim Baba Suleman Babban Daraktan Kwamitin Jibwis Social Med...
26/07/2026

‎SAƘON TAYA MURNA

‎Muna miƙa saƙon taya murna ga Alhaji Ibrahim Baba Suleman Babban Daraktan Kwamitin Jibwis Social Media ta Tarayannan Nigeria, bisa naɗa shi da aka yi a matsayin (National Media Officer) na Majalisar Agaji ta Tarayyar Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Engr. Mustapha Imam Sitti.

‎Wannan naɗin wata babbar shaida ce ta ƙwarewa, jajircewa, riƙon amana da kuma irin gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ayyukan Majalisar.

‎Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba shi ikon sauke wannan nauyi cikin hikima, adalci da nasara, Ya ƙara masa lafiya, basira da taimakonSa a dukkan ayyukansa.

‎Muna taya ka murna. Allah Ya sanya alheri, Ya sa wannan matsayi ya zama sanadin ƙarin cigaba da ɗaukakar Musulunci da al'ummar Musulmi. Amin.

HOTUNA:- ZIYARAR TA'AZIYYA A GARIN JAKUSKO LG YOBE STATE Jiya Alhamis Shugaban Jibwis Yobe Sheikh Imam Yusuf Adam Muhamm...
24/07/2026

HOTUNA:- ZIYARAR TA'AZIYYA A GARIN JAKUSKO LG YOBE STATE

Jiya Alhamis Shugaban Jibwis Yobe Sheikh Imam Yusuf Adam Muhammad Tare da Tawagarsa Sunkai Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Manyan Malaman Kungiyar Su Biyu A Jakusko LG wanda Allah ya Jarrabesu da Hatsarin mota ranan Laraba.

Kuma dukansu Allah yakarbi Abun sa Daya daga ciki Yana Garin Jakusko, Malam Ya’u musa, daya Kuma Yana Garin (Gasmu) Malam Abdulsalam.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki (SWA) Ya gafarta masu yasa Aljannatul Firdausi ta zamo makomarsu, Ya kuma bai wa iyalansu haƙuri, juriya, da ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi.

Jibwis Social Media Yobe State Directorate✍🏼

HAƊIN GUIWAR RABIƊA DA JIBWIS:Taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa mai taken: “BAMBANCE BAMBANCE TARE DA ZAMAN LAFIYA...
24/07/2026

HAƊIN GUIWAR RABIƊA DA JIBWIS:

Taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa mai taken: “BAMBANCE BAMBANCE TARE DA ZAMAN LAFIYAR JAMA’A” wanda Rabiɗah tare da JIBWIS s**a shirya yi a Abuja a ranakun 28-29/ 02/ 1448H, 11-12/8/2026M.

المؤتمر الدولي بعنوان: “التنوع والسلم المجتمعي” تنظمه رابطة العالم الإسلامي بالتعاون مع جماعة ازالة البدعة واقامة السنة في العاصمة أبوجا بتاريخ 28-29/ 2/ 1448 للهجرة الموافق ل 11-12/ 8/ 2026 للميلاد.

THE INTERNATIONAL CONFERENCE: “DIVERSITY AND SOCIAL PEACE” ORGANIZED BY MUSLIM WORLD LEAGUE IN COOPERATION WITH: JIBWIS

YOBE STATE JIBWIS SOCIAL MEDIA DAGA GARIN BAUCHI.Wasu daga cikin shugabannin kwamitin Jibwis Social media na Jahar Yobe ...
24/07/2026

YOBE STATE JIBWIS SOCIAL MEDIA DAGA GARIN BAUCHI.

Wasu daga cikin shugabannin kwamitin Jibwis Social media na Jahar Yobe da wakilan Kwamitin na kasa, yayin taron karawa juna sani daya gudana a dakin taron na tunawa da Sheikh Ja'afar Mahmud Adam dake Babban Masallacin Juma’a dake Gwallaga Bauchi State, cikin satin daya gabata.
Allah ya Karba mana yasa a mizanin kyawawan Aiyukanmu Aminnn.

✍️✍️✍️
JSM TARMUWA

ALHAMDULILLAH.A yau, Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale ya gabatar da wata muhimmiyar lacca ga jami'an 'Yan Sanda da...
24/07/2026

ALHAMDULILLAH.

A yau, Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale ya gabatar da wata muhimmiyar lacca ga jami'an 'Yan Sanda da Hukumar Hisbah a Mumbayya House (Abdulkadir Danjaji Room), Aminu Kano Centre for Democratic Studies, Gwammaja, Kano.

Taken laccar shi ne:

"Building Sakinah in the Home: Strengthening Islamic Marriage, Family Life and the Prevention of Oppression."

A cikin laccar, Sheikh ya yi bayani kan:

• Ka'idojin Musulunci game da aure da rayuwar iyali.
• Haƙƙoƙi da nauyin da ke kan ma'aurata wajen gina gida mai cike da natsuwa (Sakinah).
• Hanyoyin hana zalunci, tashin hankali a cikin gida da sauran munanan ɗabi'u ta hanyar koyarwar Musulunci.

Wannan lacca na daga cikin shirin horo da Partners West Africa Nigeria (PWAN), ƙarƙashin Rule of Law and Empowerment Initiative, s**a shirya tare da cikakken tallafin Ford Foundation. An shirya taron ne domin ƙarfafa ilimin limamai da shugabannin al'umma kan gina zaman lafiya a cikin iyali, kare martabar mata da yara, da hana cin zarafi da tashin hankali a gidaje ta hanyar koyarwar addinin Musulunci.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka wa Malam da alheri, Ya ƙara masa ilimi, hikima da ƙarfin ci gaba da yi wa addinin Musulunci da al'umma hidima.

Allah Ya sanya abin da aka tattauna ya amfani mahalarta da al'umma baki ɗaya.

✍️ Sadik Abu Abdalla
08 Safar, 1448
23 July, 2026

DALILIN KULLA KYAKKYAWAR ALAQA TSAKANIN SHEYKH ABBAS JEGA DA ALARAMMA ABUBAKAR ADAM KATSINA. Bayan kafa Izala yanzu shek...
24/07/2026

DALILIN KULLA KYAKKYAWAR ALAQA TSAKANIN SHEYKH ABBAS JEGA DA ALARAMMA ABUBAKAR ADAM KATSINA.

Bayan kafa Izala yanzu shekara 48 zuwa 49, Shekara biyu da kafa Kungiyar Izala anyi wani wa'azin kasa agarin Gashua lokacin babu jahar Yobe.

Alarammomi s**a hadu masu yawan gaske, akayi wa'azin kasa aka ƙare, akwai wani Malami Malam Hudu Chikaji Zaria, a lokacin wa'azin, yayi wa'azi akan abinda ya shafi barin yiwa mutane rubutun Sha da Alarammomi keyi, da abinda ya shafi harakar tsubbu.

Bayan Idar da wa'azin, sai Alarammomi s**ayi zama da Shugabannin Kungiyar Izala a lokacin, s**a nemi da sahale musu subar wannan tafiyar ta Izala, saboda basu da wata sana'ar cin abinci sai rubutun sha da harakar tsubbu.

Kungiyar Izala ta amince musu, a lokacin Alarammomi biyu kawai s**a yarda zasu cigaba da kasancewa da Kungiyar Izala, sune Alaramma Alaramma Abubukar Adam Katsina da Alaramma Yahuz Bauchi , daga lokacin sune kawai akaci gaba da gudanar da wa'azin ƙasa kowane sako da lungu na Nigeria da sauran ƙasashe tare da su.

To awurin wannan taron Sheykh Abbas Jega ya fara haɗuwa da Alaramma Abububakr Adam Katsina, har Sheykh Abbas Jega yaji yana son su cigaba da kasancewa har zuwa yau.

Abdulqawiyyi Abbas
07 Safar 1448M

Address

Babbangida
Damaturu

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Tarmuwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share