13/09/2023
DANDALIN HAUSA HAZAĆA YA CIKA SHEKARA 5 DA KAFUWA
A yau Laraba 13 ga watan Satumba 2023 shafin HAUSA HAZAĆA ke cika shekara biyar da kafuwa. Alhamdulillah, mun samu nasarori a cikin waÉannan shekarun musamman wajen isar da saĆonnin faÉakarwa da ankararwa ga al'umma, ta hanyar tsarawa da fitar da maganganun hikima na magabata, malamai, da wasu haziĆan mutane da ke cikin al'umma.
An ĆirĆiri HAUSA HAZAĆA ne a ranar 13 ga watan Satumba na shekarar 2018. Mun fara da rubuce-rubuce a shafin sada zumunta na Facebook daga bisani kuma muka buÉe zaure a manhajar WhatsApp.
TAĆAITACCEN TARIHIN HAUSA HAZAĆA
Sunan HAUSA HAZAĆA ya samo asali ne daga lokacin da muka tattauna a kan cewa wanne irin suna ya dace a kira dandalin da shi? Aliyu Musa Yunusa shi ne wanda ya ĆirĆiri sunan dandalin HAUSA TALENT, wato HAUSA HAZAĆA, Sadiq Rabi'u Ahmad kuma shi ne ya ĆirĆiri shafin a zaurukan sada zumunta.
Tambarin da aka fara amfani da shi an rubuta HAUSA HAZAĆA ne kawai, mun sauya waÉansu tambarin guda biyu zuwa uku, daga Ćarshe muka fitar da guda Éaya shi ne wanda yake Éauke da littafi da kuma tambarin Arewa. Duk inda aka yi arba da littafi magana ce ta karatu shi kuma tambarin Arewa na nufin al'ummar Hausawa. A taĆaice dai tambarin HAUSA HAZAĆA, yana nuni ne a kan MU TASHI MU NEMI ILIMI, ilimi ginshiĆin rayuwar dan Adam!
MANUFAR ĆIRĆIRAR HAUSA HAZAĆA
A shekarun baya mutane sun fi mayar da hankali ne wajen Éora hotunansu idan wani abin murna ya same su, ko kuma idan ranar Jumma'a ce da ke da babban matsayi a gun Musulmi, mutane suna yaÉa saĆonnin Barka Da Jumma'a, da ke cewa Jumma'a Mubarak da sauran ire-iren waÉannan saĆonnin.
Mun yi wani nazari a kan canza salon yadda muke amfani da dandalin sada zumunta musamman a Arewacin Najeriya, ta hanyar ĆirĆiro wani abu da zai taimaka wajen inganta rayuwar al'umma, domin mutanen mu suna da basira da Ćwazo wurin karatu, amma a zaurukan sada zumunta, ko wani abu na ilimantarwa basu ciki mayar da hankali a kansa sosai ba, sai Éora hotuna.
SUNAYEN JAGORORIN HAUSA HAZAĆA
-Sadik Rabi'u Ahmad
-Aliyu Musa Yunusa
-Umar Yahaya Muhammad
NASARORI:
HAUSA HAZAĆA mun samu nasarori masu yawa, a cikin shekaru biyar da muka yi muna muna yaÉa rubuce-rubucen magabata, da malamai. KaÉan daga cikinsu su ne:
⢠A Shekara biyu da s**a gabata dandalin HAUSA HAZAĆA mun yi nasarar buÉe Gidauniya wadda muka yi wa laĆabi da HAUSA HAZAĆA FOUNDATION, mun samu tallafawa marayu da marasa Ćarfi da kayan abinci domin rage musu raÉaÉi, duba da halin da muke ciki na tsadar rayuwa. Amma duk da halin matsi da ake ciki, mutane sun bada gudunmawa sosai. Alhamdulillah!
⢠A wannan azumin da ya gabata Gidauniyar Hausa Hazaka, mun yi rabon tallafin kayan abinci kimanin mutane hamsin (50), wanda jama'a da dama s**a bada tallafi, duba da matsin rayuwa da tattalin arziĆi da muke ciki.
⢠Mutane da yawa sun farka daga dogon barcin da suke yi, kuma kasancewar dama suna da hazaĆa da basirar rubutu, ta dalilin ayyukan da muke yi an samu canji sosai a yadda tunanin matasa yake nunawa a zaurukan sada zumunta da ayyukan su, tun da kuwa zuwa yanzu idan mutum ya lura zai ga matasa na fito da basirar da Allah ya yi musu ta hanyar rubuce-rubuce da irin hazaĆar su, sannan kuma suna samun Ćwarin gwiwa.
⢠Kawo yanzu HAUSA HAZAĆA mun yi ĆoĆarin tantance rubutun faÉakarwa, da tunatarwa, wanda s**a kai guda 1,905 wanda muka ÉabbaĆa su a shafukan yanar gizo, inda s**a hada da manhajoji irin su Whatsapp, Facebook, Instagram, da kuma Telegram.
⢠Yanzu haka muna da dandali har guda goma sha shida a Manhajar WhatsApp wanda muke gabatar da ayyuka a cikin su, a Facebook kuma muna da shafuka (Pages) gudu biyu da babban dandali wato Group.
⢠HAUSA HAZAĆA mun samu nasarar isar da saĆonni masu cike da faÉakarwa da tunatarwa har da wa'azantarwa, wanda al'umma ke yabawa da yadda HAUSA HAZAĆA ke zaĆulo nasihohin magabata da nasihohi masu ratsa zukata.
Wata Maganar idan mun rubuta sai kaji kamar da kai ake, duba da yadda saĆon yake Éauke da darasi akan rayuwar duniya.
⢠HAUSA HAZAĆA mun samu nasarar janyo hankulan jama'a kan dogaro da kai, tsayawa kan gaskiya, da riĆon amana da uwa uba kula da addini.
⢠A duk watan Ramadan, Hausa Hazaka, muna ĆoĆarin fitar da nasiha a kowacce rana, tun daga farkon Ramadan har ya fita.
⢠Kamar yadda muka saba, in sha Allahu a wannan karon ma za mu gabatar da rabon Satifiket, tare da karramawa wasu daga cikin jajirtattun mutane, waÉanda suke bai wa al'umma gudunmawa, da waÉanda suke bai wa wannan dandalin namu na HAUSA HAZAĆA gudummawa babu dare babu rana.
Muna fatan za ku ci gaba da ya yi mana addu'o'in da ku ke mana a koda yaushe. Babu shakka hakan yana Ćara mana Ćwarin gwiwar cigaba da ayyukan da alkhairi, in sha Allah.
Mun gode
* *