21/12/2025
“Shugabar Makaranta Ta Auri Mijin Ɗaya daga cikin Dalibanta”
Wannan wata ƙissa ce ta gaskiya da ta faru a wata ƙasa
Abin mamaki shi ne abin da shugabar makarantar ta yi wa malamai bayan dawowarta.
Bayan ta dawo daga hutun mako guda,
malaman makarantar s**a tarbe ta da farin ciki da fatan alheri, suna godiya ga Allah da ta dawo lafiya,
domin ta kasance misali na kyakkyawan hali da kyautatawa kowa ba tare da bambanci ba.
Malaman s**a ce:
“Alhamdulillah da kika dawo lafiya Malama.
Muna fatan komai lafiya, mun damu da tsawon lokacin da kika yi ba kya nan.”
Shugabar ta amsa:
“Alheri ne, babu sharrin da zai same ku, In sha Allah.
A gaskiya dai na yi aure!!!”
Malaman:
“Masha Allah! Waye wannan me sa’ar da kika aura? Allah ya sanya albarka, ya ba ki ’ya’ya, ya kuma albarkaci ku da arziki.”
Malaman mata:
“Me yasa baki sanar da mu ba, domin mu yi miki addu’a da taya murna?”
Shugabar:
“Gaskiya, na auri ɗaya daga cikin mazajenku!!!”
Dukkan malaman mata s**a yi tsit cikin mamaki da firgici.
Duk s**a fara tambaya cikin zuciyarsu:
“Mijin wace ta aura?”
Kowace malama ta sanya hannu a zuciyarta tana jin tsoro:
“Ko mijina ne?”
Shugabar ta ce:
“Ba sai kun sani ba!”
Malaman s**a ce:
“A’a! Ki gaya mana mijin wa kika aura, don kada mu fara zargin mazajenmu!”
Shugabar ta ce:
“Dole ne ku sani…”
Malaman s**a ce da murya ɗaya:
“Eh! Lallai dole ne ki gaya mana!”
Shugabar ta ce:
“To, amma da sharadi.”
Malaman s**a ce:
“Wane sharadi ne?”
Shugabar ta ce:
“Gobe kowacce daga cikinku ta kawo mijinta… sai ku sani!”
Daga shafin kamal bin mansur follow me
Shugabar ta ce:
“Gobe kowacce daga cikinku ta kawo riyal ₦500 , idan kin zo don sa hannu a takardar halartar zuwan safe, sai ki ajiye kuɗin a kan littafin halarta.
Wadda na ɗauki kuɗinta, to ba mijinta na aura ba.
Wadda kuma ban ɗauki kuɗinta ba, to ita ce wadda na auri mijinta.
Ai haramun ne in ɗauki mijinta da kuɗinta.” 😄
Malaman s**a ce:
“To shikenan, gobe zamu zo mu kawo ₦500, Allah ya kaimu lafiya.”
Washegari da sassafe, malamai s**a iso makaranta kowacce da kuɗinta.
Malama ta farko ta ajiye kuɗin, shugabar ta ɗauka.
Sai malamar ta saki ajiyar zuciya tana cewa, “Alhamdulillah ba mijina ba ne.”
Sai kowacce malama ta shiga ta sa hannu tare da ajiye kuɗinta, zuciyarta na bugawa har sai shugabar ta ɗauki kuɗin, tana sauke numfashi da kwarin gwiwa.
Sai da aka kai ga malama ta 11, ta ajiye kuɗin kuma ta sanya hannu, amma shugabar bata ɗauki kuɗin ba.
Malamar ta ce cikin rawar murya:
“Dan Allah ki ɗauka mana, zan ma iya saka dubu maimakon ɗari biyar.”
Shugabar ta ce:
“Yi hakuri.”
Malamar ta yi shiru tana jin wani zafin takaici.
Sai shugabar ta ɗago kai a hankali ta ce:
“Jooooooke!” (wato wasa kawai), sannan ta ɗauki kuɗin.
Malamar ta yi murna sosai domin ta san ba mijinta ba ne.
Shugabar ta ci gaba da dokin wasa da zukatan malamai, tana ɗaukar kuɗin kowacce har sai da ta tattara kimanin ₦11,500 na riyal.
Sai aka lura malama ɗaya bata zo ba, saboda rashin lafiya.
Ta kira ta ta waya ta ce:
“Yi hakuri ban samu zuwa ba, amma ku gaya min mijin wace ta aura?”
Malaman s**a ce:
“Wallahi har yanzu ba mu sani ba. Ta tattara mana kuɗi, kece kadai kikai saura!”
Washegari, malamar da bata zo ba ta kawo kuɗin nata, ta ajiye su akan littafin, shugabar ta ɗauka ta yi shiru.
Malaman s**a yi mamaki sosai.
S**a fara tunani:
“Wayyo! To mijin wace ne ta aura kuwa?”
Shugabar sai ta tara dukkan malamai ta kira su taron gaggawa.
Zukatan su na bugawa suna tsammanin yanzu za ta bayyana gaskiya.
Shugabar ta ce:.....
Shiga comment domin samun karshen labarin
Kamal bin Mansur