08/02/2025
GWAMNA DAUDA LAWAL YA JAJANTA AKAN ƊALIBAI 17 DA S**A RASA RAYUKANSU SAKAMAKON GOBARA A ZAMFARA
Gwamma Dauda Lawal ya isar da saƙon ta'aziyyar sa ga iyalai da ƴan uwan ɗalibai 17 waɗanda s**a rasa rayukansu sakamakon gobara a wata makarantar Almajiri a Zamfara.
Aƙalla dalibai 17 sun rasa rayuwarsu ta dalilin wutar gabara a makarantar Almajiri dake ƙaramar hukumar mulkin Ƙaura-Namoda.
Kakakin gwamnan, Sulaimim Bala Idris, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Laraba ya bayyana gobarar a matsayin babban abun tashin hankali
"Na kaɗu matuƙa da gobarar da ta afku ranar Talata a Makaranatar Mallam Ghali, wata Makarantar Almajiri dake ƙaramar hukumar mulkin Ƙaura-Namoda.
"A madadin gwamnatin jihar Zamfara, muna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalai, makarantar, da kuma al'umma baki ɗaya akan wannan rashi da akayi.
"A wannan lokacin marar daɗi, ina roƙon Allah Maɗaukakin sarki da yaba ƴan uwa haƙuri da dauriyar jure wannan rashi. Ina fata da addu’ar samun sauƙi ga waɗanda s**a jikkata.
"A matsayin mu na gwamnati, za mu bincika abubuwan da s**a haifar da wannan wuta kuma zamu bi hanyoyin magance afkuwar hakan a gaba.
"Za mu samar da duk tallafi da taimakon da s**a dace ga iyalan waɗanda abin ya shafa."
Sulaiman Bala Idris
Mai magana da yawun gwamnan Zamfara
05, Fabrairu, 2025