Jaharmu A Yau

Jaharmu A Yau ONLY POST YOU CAN TRUST

Zan sauke duk Ciyaman din da ya kasa tabbatar da nasarar APC a karamar hukumarsa a zaben 2027 - Gwamnan EbonyiGwamnan ji...
02/09/2026

Zan sauke duk Ciyaman din da ya kasa tabbatar da nasarar APC a karamar hukumarsa a zaben 2027 - Gwamnan Ebonyi

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya yi barazanar sauke duk wani shugaban karamar hukuma da ya kasa tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a karamar hukumarsa a zaben 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Abakaliki, babban birnin jihar, yayin bikin rantsar da sabbin shugabanni da mataimakansu na kananan hukumomi 13 na jihar.

Me za ku ce?

Wanda EFCC ke bincike na iya yi wa ɗan takara yaƙin neman zaɓe - WikeMinistan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce k...
02/09/2026

Wanda EFCC ke bincike na iya yi wa ɗan takara yaƙin neman zaɓe - Wike

Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce kasancewar mutum yana fuskantar binciken hukumar EFCC mai yaƙi da ci hanci da rashawa a Nijeriya, ba ya hana shi shiga harkokin siyasa ko yi wa ɗan takara yaƙin neman zaɓe.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Wike ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata ganawa da manema labarai da ya shirya, wadda aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na Channels.

Da yake martani kan sanya tsohuwar ministar jinƙai, Betta Edu, wadda aka sanya cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu a 2027.

Ministan ya ce idan mutum EFCC na bincikensa amma ba a kai shi kotu ko kuma ba a same shi da laifi ba, babu dalilin da zai hana shi shiga harkokin siyasa ko taimaka wa wani ɗan takara wajen neman kuri’u.

Sakataren rundunar sojin kasa ta Amurka ya mika takardar murabus ga TrumpSakataren rundunar sojin kasa ta Amurka, Dan Dr...
01/09/2026

Sakataren rundunar sojin kasa ta Amurka ya mika takardar murabus ga Trump

Sakataren rundunar sojin kasa ta Amurka, Dan Driscoll, ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaba Donald Trump, kamar yadda wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya tabbatar wa gidan talabijin na FOX News.

Har yanzu fadar White House ba ta amince da murabus din ba. Sai dai jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito cewa ana sa ran Driscoll zai bar ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Matakin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin takun saka tsakanin Driscoll da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth.

31/08/2026

“Tinubu Zai Riga Wasu Mutane Da Yawa Shiga Aljanna, Domin Waɗanda Suke Ce Masa Azzalumi Ba Su Da Hujja.”

— Sheikh Jalo Jalingo

30/08/2026

Muhammadu Rasulilla
S. A. W

Duk masoyinsa yayi comment da S. A. W

Sister zehrah Happy Maulud
30/08/2026

Sister zehrah Happy Maulud

Benzema zai bar Al Hilal bayan ya cimma yarjejeniya da ƙungiyar Saudi Pro League.Ana sa ran Karim Benzema zai bar Al Hil...
30/08/2026

Benzema zai bar Al Hilal bayan ya cimma yarjejeniya da ƙungiyar Saudi Pro League.

Ana sa ran Karim Benzema zai bar Al Hilal bayan ya cimma yarjejeniya da ƙungiyar Saudi Pro League zai soke kwantiraginsa bisa amincewar ɓangarorin biyu. Hakan zai kawo ƙarshen gajeren zamansa a ƙungiyar da ke Riyadh tun da wuri.

Masani kan harkokin saye da sayar da 'yan wasa, Fabrizio Romano, ya ruwaito a ranar Lahadi cewa “Karim Benzema ya yanke shawarar barin Al Hilal, kuma an amince da soke kwantiraginsa bisa yarjejeniyar ɓangarorin biyu a yau.

Benzema zai sanar da matsayinsa game da makomarsa nan ba da jimawa ba, zaɓin sa ya haɗa da yin ritaya ko kuma buga wasa a wata ƙungiya ta daban a Saudiyya. Amma ba zai koma Turai ba.

Dan wasan gaba na Faransa mai shekaru 38 ya koma Al Hilal a watan Fabrairun 2026 bayan ya bar abokan hamayyarsu na Saudiyya, Al Ittihad. Ya fara buga wasansa na farko da ƙungiyar a ranar 5 ga Fabrairu a karawar da s**a yi da Al-Okhdoud a gasar Saudi Pro League.

Adeleke ya tabbatar wa Shugaba Tinubu cewa zai tabbatar da an ba shi kuri’un jihar Osun.Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adel...
30/08/2026

Adeleke ya tabbatar wa Shugaba Tinubu cewa zai tabbatar da an ba shi kuri’un jihar Osun.

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu cewa zai tabbatar da an ba shi kuri’un jihar, yana mai jaddada cewa ba ya yin alkawuran banza, kuma dole ne a gudanar da siyasa bisa gaskiya da riƙon amana.

Adeleke ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake karɓar Sakataren Ƙasa na Jam'iyyar APC, Ajibola Basiru, wanda ya kai masa ziyara ranar Lahadi.

Gwamnan, wanda ya kira Tinubu da “mahaifina masoyi,” ya ce goyon bayansa ga Shugaban Ƙasa na gaskiya ne, yana mai jaddada cewa da gaske yake nufi da alkawarinsa na tabbatar da cewa Shugaban zai samu kuri’un Jihar Osun ɗari bisa ɗari.

Kano ta zama kan gaba wajen kashe kuɗaɗe a fannin ilimi  a zangon farko na 2026Jihar Kano ce ta fi kowace jiha a Najeriy...
30/08/2026

Kano ta zama kan gaba wajen kashe kuɗaɗe a fannin ilimi a zangon farko na 2026

Jihar Kano ce ta fi kowace jiha a Najeriya kashe kuɗi kan harkar ilimi a zangon farko na shekarar 2026, inda ta kashe Naira Biliyan 59.11 .

Bayanan TheCable Index da aka samo daga kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) sun nuna cewa Lagos ce ta zo ta biyu da kashe Biliyan 39.93 , yayin da Delta ta kasance ta uku da Biliyan 33.34.

Oyo ta zo ta huɗu da Biliyan 28.24 , sai Benue da Biliyan 23.92 biliyan, yayin da Abia ta kashe N21.25 biliyan. Ekiti ta kashe N20.19 biliyan, Bayelsa N18.79 biliyan, Kaduna N18.05 biliyan, sannan Bauchi N17.71 biliyan.

Sauran jihohin da s**a kashe kuɗi masu yawa sun haɗa da Adamawa (N16.95bn), Ogun (N16.42bn), Kogi (N15.09bn), Katsina (N14.26bn) da Akwa Ibom (N14.21bn).

A ƙarshen jerin, Cross River ta kashe N3.87 biliyan, yayin da Imo ta kashe N3.52 biliyan.

Bayanan sun nuna cewa Jigawa ba ta samu wani adadin kashe kuɗi kan ilimi a zangon farko na 2026 ba, yayin da ba a saka adadin jihar Rivers cikin bayanan da aka fitar ba.

Ga jihohi 34 da aka samu bayanansu:

1. Kano – N59.11bn
2. Lagos – N39.93bn
3. Delta – N33.34bn
4. Oyo – N28.24bn
5. Benue – N23.92bn
6. Abia – N21.25bn
7. Ekiti – N20.19bn
8. Bayelsa – N18.79bn
9. Kaduna – N18.05bn
10. Bauchi – N17.71bn
11. Adamawa – N16.95bn
12. Ogun – N16.42bn
13. Kogi – N15.09bn
14. Katsina – N14.26bn
15. Akwa Ibom – N14.21bn
16. Nasarawa – N13.85bn
17. Gombe – N12.70bn
18. Osun – N12.42bn
19. Ebonyi – N12.36bn
20. Kwara – N12.09bn
21. Enugu – N9.12bn
22. Ondo – N8.66bn
23. Plateau – N8.46bn
24. Borno – N8.39bn
25. Yobe – N8.33bn
26. Edo – N7.84bn
27. Kebbi – N7.40bn
28. Taraba – N7.38bn
29. Niger – N7.15bn
30. Sokoto – N6.85bn
31. Zamfara – N5.74bn
32. Anambra – N4.79bn
33. Cross River – N3.87bn
34. Imo – N3.52bn

Da ɗumi-ɗumi: Abdulaziz Yari Ya karyata Atiku Yace Yana wa kansa da kansa karya da kuma yaudarar ƴan Najeriya kan batun ...
29/08/2026

Da ɗumi-ɗumi: Abdulaziz Yari Ya karyata Atiku Yace Yana wa kansa da kansa karya da kuma yaudarar ƴan Najeriya kan batun dawo da tallafin man fetur.

Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Bola Tinubu na 2027, Abdulaziz Yari, ya zargi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da yaudarar kansa da kuma ƴan Najeriya kan batun dawo da tallafin man fetur.

Yari ya ce maganar dawo da tallafin man fetur ba ta da tushe, yana mai cewa wanda ke yi wa ƴan Najeriya alkawarin dawo da shi yana wa kansa da kansa karya da kuma jama’a ne.

Ya kuma ce dawo da tallafin zai iya jefa gwamnati cikin kashe makudan kuɗaɗe, yayin da Atiku ke cewa zai dawo da tallafi na musamman (targeted subsidy) domin rage radadin tsadar sufuri da rayuwa ga al’umma.

Wannan kalamai na Yari sun ƙara zafafa muhawarar siyasa yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Address

001
Jigawa

Telephone

+2349027074793

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaharmu A Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaharmu A Yau:

Shortcuts

Share